Sashe 57
Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Salis ne zaune a polo shida Samuel yana ɗan masa bayani game da Addini kafin ya karɓi kalmar sha'hada. "Da farko dai zaka ajiye shan kiya da neman mata, sannan girmama iyaye koda ba musulmai bane...Zaka daina zuwa coci, salloli guda biyar a kowacce rana.... A kwai A'zumi da a keyi a cikin watan Ramadan wanda yanzu haka ya kusa kamawa...sannan ya zama dole ka daina"...."Bai ƙara saba sukaji sallama daga bakin palon gidan. "Yes Samuel ya ce sai suka zubawa ƙofar shigowar ido. Kawu da AJ ne sai kuma Nana da ta ce lallai sai tazo.
Mi ƙewa sukayi tsaye suna kallon juna tsakanin AJ da Salis harda Samuel. Kawune ya fara maga "Ko Mahaifinka yana ciki? Salis ya kai kallonsa izuwa ga Kawu ya ce "Eh yana ciki" Nana da take bayan AJ har yanzu bai gantaba sai zuciyarsa da ta ke ta harbawa a lamar dai da mosoyi...?
Kawu da Muhammad Hajiya Babba Salis AJ laɗifa Samuel Sarah ne duk acikin palon a zaune kowa ya nutsu yana jiran abun cewa. SAMUEL dai sai yanzu ya ƙara gane waye AJ ɗin. Laɗifa kam idonta kar a kan AJ da Nana, tana jin tamkar ta tashi ta harbe su kowa ma ya huta.
Muhammad ya fara magana bayan sun gama sauraron abunda kawun ya ce kamar haka..."To muna mai sake miƙa godiya ga Allah da ya sa komai yazo cikin ruwan san yi da fahimtar juna...sannan muna ƙara miƙa ta'aziyar marigayi ya Innah, Allah yasa ta huta, mukuma idan tamu tazo yasa mucika da imani. Duk palon suka amsa da amin. To sai kuma abu na gaba... Kowa ya ɗaga kai yana kallon Muhammad. Ya ce "Aisha tana ɗauke da cikin sa a jikinta har tsawon sati huɗu yanzu haka.
Zumbur AJ ya miƙe yana kallon Hajiya Babba wacce ta kifa kanta a kan cinyoyinta. Da sauri itama Nana ta wrufe bakinta tana ƙoƙarin fashewa da kuka. Salis kam wata iriyar kunyace ta rufeshi. Laɗifa kam tsaki taja ta miƙe ta nuna AJ dake tsaye ta ce "Wallahi saina ga bayanka kuma saika tozarta kamar yanda ka tozartamu, ba dai kai mayen kuɗi ba, to wallahi Allah saiya saka mana , mugu maci amana wawa mara tinani dabba jahili ɗan a kuy"..."Kyeeeee!!! Laɗifa ya isa ya isa! Cewar Salis yana miƙewa tsaye. Da sauri Laɗifa ta bar gurin tana kuka. AJ ya ce "Ta faɗi gaskiya cewar banida tunani bani da hankali jajili maci amana tabbas duk wannan suffofinane, naci amanar Salis, bai cancanci haka daga gareniba. Yana faɗa yana kuka. Sannan ya ɗauko takardar gidan da a ka bashi ya ajiye a gaban Salis , ya ɗauko jakar kuɗin ya haɗa da makullin motar ya ajiye ya ce....
"Ga kayanku nan, basu da amfani a gareni, dama saboda Innah ta nayi gashi ta tafi batare da tamoresu ba. Tabbas Allah yasan irin halin da zata shiga idan har taji labarin na yi aure harda ciki ba tare da ta saniba, Allha ne kaɗai yasan halin da zata shiga. Tabbas Innah kin huta da ta kaicina. Sai kuma ya dawo gurin Nana itama ya fara cewa "Ki yafemin ƙanwata na lalata komai na zubar da mutuncin kanmu a kan kuɗi. Haka dai AJ ya dinga sambatu har saida ya ba kowa tausayi. Kawu ya rasa mai zaice tsabar ruɗewa.
Muhammad ya ce "Karka ɗorawa kanka laifi kai ɗaya, ni dai a ganina ai wannan ma abun farincikine , sannan wannan kuɗaɗan sun zama naka harda gidan da motar, wannan hakkin kane har a gurin uban Giji. Nan fa a kayi a kayi da AJ ya ce sam bazai ɗaukaba, Salis ya bashi baki ya ce shifa wallhi saide ya ƙare a talauci, haka ya tashi ya bar gidan cikin kuka, yana cewa "Na karɓi cikina kuma zanyi komai da uba yakeyiwa yaronsa ban yarda a tayani da komaiba, zan nemi nawa na kaina insha Allah! Yana faɗa ya fita batare da yajira komai ba. Nana ta tashi zata bishi Kawu ya tareta.
Salis ne ya kaisu gida yana rarrashin Nana. Koda sukaje gidan AJ bayanan ga gidan nasu ba kwamai domin sun kwashe komai sun kai sabon gidan. Salis bai shiga gidan ba dan haka baisan da cewar ba komai a gidan ba. A mota suka tsaya bayan kawu ya fita ya kalleta ya ce "Nana ina sonki karkiyi tunanin wannan abun zaisa na gujeki, ina tare dake har ƙarshin numfashina, sannan ga wannan ki ajiye a gurinki ko zaki buƙaci wani abun? Ya faɗa yana miƙa mata kuɗin da ya ciro. Yana jin kukan da takeyi kaman ya rungumota jikinsa ya rarrasheta, amma ba dana. Ba ta ce komaiba ta buɗe motar ta bar shi yana binta da kallon mamaki har ta shiga gida. Haka ya zauna a cikin motar yana tunanin abunyi.
*Comments É—inku shine abun da*
*S REZA*
[10/21 22:06] Aliyu Makko: *S REZA...âœï¸*
*ADM*
*First Class writer's asso...*
*PAGE4ï¸âƒ£3ï¸âƒ£*
........Haka Salis ya bar ƙofar gidan cike da damu wa a ransa, baya son ya taƙura Mata, zai bata dan lokaci kafin komai yayi daidai. Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta ko wani ɓangarori. AJ ya koma aikin sa na tuƙa motar bredi wanda suɗinma da ƙyar suka ɗauke shi a kan suna da ma'aikata, yaci sa'ar dai ya taɓa aiki a gidan ne kuma lokacin da yayi aikin basu taɓa gamashi da wani laifi ba. Dubu goma za'a dinga biyansa duk wata ɗaya, haka ya nuna farin cikinsa sannan ya kama aikinsa ba wasa. Ita kuwa Nana kaman yanda Aj ya ce ta kama kanta ta riƙe maraicinta ta nutsu ta mai da hankalinta a kan karatun ta, hakan tayi domin bin maganar Yayan nata. Wayar hannunta ya karɓa ya sayar, da kuɗin wayar ya sayo musu duk wani kayan buƙata domin yace bazai kwaso nasu na da ba. Rayuwa ta yi musu tsanani sosai, hakan kuma baisa ya nunawa ko wa cewar yana cikin damuwaba, harta kawunsu baisan da haka ba, wani lokaci abunda zasucima wahala yake musu, ɗan sauƙin abunma a kullum yana zuwa da bredi kida, daga ƙarshe ma Nana daina zuwa school ta yi, sai islamiyya, shiɗinma dai ana binsu bashin kuɗin wata. Duk da haka ya ce duk lokacin da Hajiya Babba zataje asbiti to baya buƙatar suyi amfani da komai nasu. Da farko Muhammad bai yardaba amma ya ga AJ ɗin kamar hakan yakeso, hakanne yasa komai idan za'a yi sai an sanar masa, albashin sa na farko ma a kan yaron ya tafi, hakan ma dan an rage masa kuɗin ne. Izuwa yanzu rashi da damuwa sun fara nunawa a jikinsu, duk da irin halin da suke ciki bai hana Kadija gabatar da kanta a gurinsa ba, amma ya mata kace kace ya ce idan a kan haka take zuwa gidansu to karta ƙara zuwa. Yanzu yana yawan zuwa gidan kawunsa kuma duk lokacin da zaije sai ya ruƙo musu bredi ya kai musu. Har Wannan lokacin bai manta da Sarah a ransa ba amma yasan babu komai yanzu a tsakanin su, yanzu itama ta daina kiransa , sai kawai yaji baiji daɗiba. Lokacin da abubuwa suka rincaɓe masa sai kawai ya siyar da wayarsa ya sayo ƙarama, kuɗin wayar kuma ya fara siyan kayan jinjiri, sannan ya biya wa Nana kuɗin school taci gaba. (Wannan kenan)
*ABDALHA POV*
Kamar da wasa abubuwa sun chakuÉ—e masa, Duk gurin wanda yake ganin zai tayashi domin shawo kan mahaifinsa a kan lamarin auransa amma abun yaci tira. A kan wannan abun yasa iyayen nasa sun samu matsala, yanzu haka mahaifinsa ya cire hannunsa a kansa gaba É—aya, yanzu haka ya dawo gidansu da zama kasan cewar bashi da lafiya, ciwon zuciya ya sa shi a gaba, Daddy yayi tunanin Abdullah yana yin hakane domin ya amince da auransa , baisan cewar É—ansa ya faÉ—a cikin kokin love ba. Wayarsa ya ciro yana daga kwancen ya nemo numbar Isa, kira É—aya ya É—aga yana sallama.
"Yauwa Isa ya kukayi da shi? Yayi tambayar cikin Muryar da kanaji kasan yana cikin wani hali.
"Isa yaja doguwar ajiyar zuciya ya ce "Wallhi kunyarsa nake ji, bansan da wani ido zan kalleshiba, bansa ma mai zance masa ba.
"Kwana nawa ya rage? Cewar Abdalha yana lumshe idonsa?
"Kwana takwas? Ya bashi amsa yana jin babu daÉ—i ga tausayin halinda Abdalha ke ciki.
Azuciyarsa ya furta "Takwas! Sai ya kashe wayar yana jin cewar dama haka a ke ji idan kana son mutu! Gani yake babu wanda ya taɓa jin irin abunda yakeji a kan Zainab, sam bai yarda da cewar wani ne zai aureta ba, yana mata son da zai iya ja da kowa domin mallakatarta, gani yake shi nashi salon son daban yake, duk lokacin da ya tuno da cewar auranta saura kwanaki kaɗan sai ciwonsa ya tashi. Numbar ta ya kira yana jin cewar zai samu mafita daga gareta.
*ZAINAB POV*
Mutuƙar wannan auran da zatayi zaisa mahaifinta farinciki kamar yanda ya ce, to tabbas zata auri Aliyu badan tana sonsaba, zatabi zaɓin mahaifinta kodan ganin yayi alfahari da ita kamar yanda ya ce, ta yarda da cewar tana son Abdalha kamar yanda yake sonta amma wani ƙaramin abu ya shiga tsakani yayi baƙe-baƙe babu damar kaucewa. Hirar su da shi ta jiya ta tuno lokacin da ya ke ce mata "Kar zuciyarki ta raya miki cewar zaki auri wani baniba, domin haka bazai taɓa faruwa ba, kisa a ranki nine mijinki, bansan soba sai a kanki, haka zaluka bansan komai game da shiba na sa ƙafa ta a ciki, bansan komai ba ban saniba! Ya ƙara sa yana kallon wayar kamar ita zai gani. Kawar da idanunta ta yi itama daga kallon wayar tana jin cewar sonda take masa yafi wannan abun da ya lissafo kawai dai shi ya fito da nasa filine.