← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 67

Sashe 66

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*S REZA ✍️*

*ADDININMU*

*S REZA ✍️*

*Watpad*
Salis m Reza.

*Feecbook*
Salis m Reza

*Arewabooks*
Salis m Reza

*Gimal*
[email protected]

*Whasoop numbar*
08100785178

*Instagram*
*Salis m Reza.

*A ko'ina inada gurin zanta wa da kowa idan da buƙatar hakan🥰🥰*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

*PAGE5️⃣0️⃣END* babu editing sai hakuru

........*RANAR LAHADI.* Kamar yanda suka faɗa cewar ranar Lahadi ko bai warkeba to zai ƙarɓi hukunci irin nasu na Sojoji daidai da abunda ya aikata. Saidai kuma wani abun da ya baiwa kowa mamaki shine... a washe garin ranar lahaɗi sai kowa yazo ya ga Daniyel lafiya lau babu wannan ciwukan na jikinsa, kansa ya dawo daidai haka hannayensa da ƙafafunsa. Shi kansa mamaki yakeyi domin shima haka ya tashi yaga kansa. Ya buɗe baki zaiyi magaba nannma yaji muryarsa ta fita kamar da lafiya lau, ai kuwa ya fara ihun kiran sunan matar tasa Elixa!. Cikin tsananin farincin Eliza ta kira Muhammd da sauran yaran ta sanar musu cewar Daniyel ya warke. Kowa ka gani bakinsa a washe domin kuwa abun ya basu mamaki. Ana cikin hakane saiga Umar da Usman sunzo gidan tare da matayensu domin Muhammad ya sanar dasu su cewar ranar Lahadi suzo gidan. A nanne Umar da Usman suke sanar dasu cewar wai ai jiya wanda yayi tsfin ya war-ware komai kuma ya kirasu ya sanar masu. Da mamaki Muhammd ya tambaye su waye? Suka kalli juna cikin rashin son faɗan sunan wanda yayi ɗin. Kafin suyi magana Daniyel ya ce "Basai kun faɗa ba ni nasan waye. Muhammad da Sadiya (Titi) da Elixa sukace waye? Daniyel ya ce "Sarkin garin ne, domin kuwa ya sanar dani cewar zanga abinda zai sameni domin kuwa na cimasa mutunci saisai. Muhammad da sauran suka cika da mamaki domin kuwa harda Sarkin a ke neman wanda sukayi a sarin a she shine da kansa yayi. Umar da Usman suka sanar musu da cewar wai sarkin ya ce saboda kaine ma yasa ya karya asirin badan ba da saidai ta ƙare a haka. Jin haka yasa Muhamd sauke a jiyar zuciya yana tausayin yayan nasa.

Suna cikin haka ne saƙon Sojojin yazo musu cewar an bashi a'wa huɗu ya gama komai domin idan sukazo tofa komai nasa ya ƙare babu wani ɓata lokaci da zasu jira. Acikin wannan a'wa huɗun sun cinye a'wa guda da koke-koke. Muhammad ya naimi ɗan uwan nasa da ya karɓi kalmar shahada kafin lokaci yayi. Daniyel ya ce "Solomon yanzu babu wani abu da ragemin aduniya kaga koda na koma addininku ai babu wani amfani kawai yanzu ka yafemin duk abunda na maka kaida Titi harda matarka". Muhammad ya ce "Na yafe maka duniya da lahira n
Muma Allah ya yafemana kuma kaima ka yafemin, sannan shi Allah mai karɓar addu'o'in bayinsane a koda yaushe, saboda haka dan Allah zan baka kalmar shahada kafurtata kuma kasa a ranka cewar kayi hakanne har cikin ranka. "Nayi Laifuka da dama wanda ko a Addinimu ni ba mutumin kirki bane, saboda hk bazan koma addininkuba, addininda na tarbatar shine addinin Allah, kuma shine addinin gaskiya, kuma addinin mutanan kirki ba irinaba. Anan Daniyel ya fara faɗo irin abubunda ya aikata a rayuwarsa game da Musulmai. A nanne ya ke sanar musu cewar musulmai ne suka kashe mahaifinsu a gabansa hakanne yasa ya ɗau alwashin babu shi ba duk wani mudulmi, daga baya ya gano a she musulmain irin marasa addininnane masu fashi da makami, amma dukda na gano gaskiya naji zuciyata taƙi yarda da musulmai, hakan yasa nake amfani da muƙamina na babban Soja ina kashesu ta yanda babu wanda zai zargeni, to yanzu a hakan ne Allah zai yafemin? Ya ƙara sa yana kuka yana kallon kowa dake ɗakin yana jin abunda yake cewa.

"Eh Allah shene kaɗai wanda yakeso idan kayi laifi ka koma gareshi ka tubu, to hakan nasa Ubangiji yaji cewar lallai wannan bawan nasa ya yarda da cewar shine kaiɗai mai yafiya kuma mai jin ƙai. Allah zai yafe masa ya kuma karɓeshi hannu bibbiyu kuma Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yayi alfahari da shi. Muhammad ya shiga masa bayani yanda zai gane cewar babu irin laifin da bawa zaiwa Ubangiji ya kasa yafe masa saidai laifi tsakanin bawa da bawa ko kuma shirka. Itama shirkar malamai sunyi bayani a kan cewar Allah na yafewa mutuƙar mutum ya tuba ya dawo gareshi. Jin haka yasa Daniyel cewa "Na yarda zan koma na yarda na yarda. Kowa dake ɗakin ya ɗau hamdala suna murmushi. Saida Daniyel yaje Muhammd ya koya masa yanda a ke alaula da wanka irin na Musulunci kafin a ka bashi sabuwar jallabiya fara da hularta aka fara bashi kalmar shahada. Itama Momy Elixa ta ce zata koma. Haka cikin aminci Allah da yardar sa da kuma amincewarsa Daniyel da Eliza suka dawo addininsa addininmu Addinin gaskiya.

Anan cikin palon Daniyel ya ce "Nima sunan Muhammadu na keso a bani. Ai kuwa Muhammad ya ce "to daga yau ka koma Ahamad, ko da bayan ranka haka zamu dinga kiranka. Haka kuwa a kayi kowa ya kirasa da sunnansa na Ahamad, kuma ya amsa. Ibrahim ya fita ya samo mai hoto ya É—aukeso dukkansu, sannan ya dinga É—aukarsu É—aya bayan É—aya. A nanne Ahamad ya sanar da Muhammd cewar a kwai ku É—aÉ—e masu yawa a account É—insa , sannan ya sanar da shi cewar Zara da Ibrahim suma kowannansu ya buÉ—e masu nasu account É—in kuma yana sa kuÉ—i a ciki, sannan ya bashi wasu ta kardu na filayensa da kuma shaidar tabbatar komai É—in nasane. Muhammad ya ce "Dama Kanada wannan amma kuma ka tsaya neman gurin zuwa kaida matarka? "Idan na nuna cewar nawane to sai sojoji sun kwace domin kuwa haka dokar take. Muhammad yayi kuka sosai yana jin inama da abun da za'ayi a fasa harbe É—an uwan nasa.

A wannan lokacin ne kuma motar Amoka ta sojoji tazo unguwar tare da motocin manyan Sojojin ƙasar ta Nigeria. Haka dai su tattara shi suka tafi dashi, sannan suka naimi mutum ɗaya wanda zaibisu. Muhammad ya bisu har filin gurin da za'a harbesu ɗin. Mutane huɗe ne a gurin an rufe kansu da baƙin ƙyelle sannan an ɗaure hannayensu ta bata. Gurin filine mai girman gaske wanda ba'a iya hango ƙarshensa, saida a ka yi wasu yan zantuka a ka haɗa connecting kafin a ka sakesu suka fara gudu, sannan a ka baiwa sojojin damar harbi. Ahmad yana kudu yana maimaita kalmar shahada da Muhammad ya sanar dashi har lokacin da yaji shigar bulet a jikinsa.

Kuka sosai Muhammd keyi lokacin da yaga ɗan uwansa a kwance ba numfashi, nan take ya fara roƙa masa Allah. Haka ya ɗauko gawarsa izuwa gida a ka sallaceshi. Lokacin da Shek Kabir kabuga da Malam Adamu sukaji labarin abun sunyi masa addu'ar samun tsira daga mahaliccin mu, sannan suka jinjinawa Muhammd ɗin da irin ƙoƙarin da yayi. Haka su kaɗai suka yi zama makoki har na kwana uku. Ranar juma'a kuma a ka kai kowacce amarya ɗakinta. Ibrahim da Sadiya Abuja suka huce, Salis da Nana su kuma sabon gidansu da ya ke kusa da tsohon gidan da su Hajiya Babba suka taɓa zama. Zara da AJ kuwa sabon gidansa a ka kaita ita ka ɗai a gidan.

Shiru tayi tana kallon zara-zaran yatsun kafafunta tana tariyo komai cikin ranta, tun daga ranar da suka fara haɗuwa da AJ har Kawo yau da take cikin gidan sa. Godiya tayi ga Allah da ta tunoinaemahaifinta da mahaifiyar ta sun karɓu addinin musulunci.tana cikin wannan tunanin ya fito daga wanka ɗaure da tahul. Bai kalketaba har ya gama saka kayansa kafin ya ce "Nasan na miki laifi amma bai kai a ce har zuwa yanzu kina fushi dani ba, na baki haƙuru amma har yanzu magana ma kin kasa min haba my Zara? Yanzuma bata ko tanka masa ba ta shiga toilet itama tayi wanka da alaula ta fito ta sameshi ya haɗa kai da ƙafa yana kallonta. Ganinn hk yasa itama ta zauna tana jiran jin abunda zaice. Tashi yayi ya ce zo mu gabatar da Sallah ta miƙa gudiya ga Allah da ya mallaka min ke. Babu musu tabi bayan sa har palon gidan idan ya shin fuɗa musu darduma ya jasu raka'a biyu. Bayan sun idar ne ya shiga mata tambayoyi game da addini. Cikin mamaki yaji tana bashi amma. Sosai yayi mamakita, sannan ya kamo kanta ya fara mata addu'o'in ta na amsawa a zuciyarta da Amin. Suna idarwa ya kawo musu kayan ciye-ciye amma ta miƙe ta izuwa ɗaki ta hau gado ta barshi a gurin yana kiranta amma ko kallonsa batayiba. Haka shima yaji bazai iya cin komaiba , sai ya bita a baya har ɗakin yana sanar da ita abinci fa zasuci. Haka suka share kwana uku babu abunda yake haɗasu sai gaisuwa da gyaran ɗakinsa , amma bayan wannan bata ƙara shiga sabgarsa. A kwana na huɗune da asuba bayan ya dawo daga Sallha ya nufi ɗakinta yana addu'a a ransa. Ya na shiga ya sameta zaune ta idar da Sallah tana addu'a. Zama yayi a bakin gadon yana jiranta. Tana idarwa bata ko kalleshiba ta ta tashi zata koma kan gado.da sauri ya jawota jikinsa ya na cewa "i'm so sorry my zara dan Allah ki tsaya muyi mugana wallhi na gaji, na miki laifi amma na tuba Please? Kwantawa tayi a jikinsa jin ta kasa kwace jikinta tana dukan bayansa tana jin cewar itama ta gaji da wannan fushin nata domin itama tana cutuwa.
Chapter 66 · 0% Book details