← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 67

Sashe 67

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Mai yasa kamin ƙarya? AJ ya ce "Kiyi haƙuri ba sai mun tuna baya ba. Ta ce "Faɗa min yanda komai ya faru? AJ ya sauke ajiyar zuciya domin baya son tuno komai na baya musamman abunda ya faru tsakanin sa da Hajiya Babba. Nan ya fara bata labarin komai har barindin Nigeria da da wowarsu da zuwansa gidansu. Zara na jin haka ta ce "Gaskiya ban taɓa jin labarin mutum mai son kuɗi irin naka ba AJ, kaso ka jefa kanka a cin masifa da bala'i. Haka dai itama ta sanar da shi irin halinda ya jefata bayan tafiyarsa. Harda ƙullesu da a kayi da dukan da tasha. Bayan ta gama ne taga yana kuka sai itama ta fara kukan tana share masa hawaye. Ya ce "Tabbas zara ke ɗin alkairice a rayuwata, na tabbatar da cewar kina sona son da ba'a yin irinsa a wannan zamanin namu, babu abunda zance miki sai godiya da addu'ar Allah ya bamu haƙurin zama da juna. Ta amsa da amin tana ƙara shigewa jikinsa tana jin cewar son aJ a jinin jikinta ya ke.

Haka rayuwar wannan mutane ke tafiya cikin so da kwannar junayensu, haka ɓangaren Salis da Nana da Ibrahim a garin Abuja, itama Hajiya Babba da Muhammd da ƴarsu guda ɗaya Hajara suke zaune cikin farinci.

*Bayan wasu lokuta.*

Muhammad ya sanar dasu Ibrahim wasiyyar mahaifinsu. Suka ce kawai a gida masa masallaci da kuɗin, kowa yayi na'am da maganar da Ibrahim ɗin yayi. Haka suka sayi fili a ka gina Malallacin cikin ƙanƙanin lokaci. Hajara kam ta zama mai gidaje da yawa, yau tana gidan Salis gobe gidan AJ ko gidan Ibrahim watarana ma har kano gidan su Abdalha, ko kuma gidan Laɗifa wacce dole tasa ta auri Umar wanda shima yanzu yana aiki ƙarƙashin Salis. Yanzu haka suna zaune lafiya da ita bayan bidirin da a kayi a baya. Yanzu haka tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki a jikinta, kuma yanzu tana son Hajara sosai, domin watarana da kanta take cewa a bata ita tayi kwana biyu,.

Nana ce ta ke sanar da Salis cewa "Nifa har tsoran wannan shigen wayon na Hajara na keyi,gata da ɗan banzar tanbaya. Ai kuwa tana rufe baki sai gata da wani hoto tana ce wa "Mami wannan hotunan da naga anrubuta *ADDININMU* a jiki to wannan mutum ɗayan waye? Ta faɗa tana nuna hoton da ta gane kowa amma banda Daniyel. (Ahmad) Nana ta ce "Ooo Ni wai ke mai yasa ba kya jin magana ne, komai kiga gani sai kin tambaya to"..."Kafin Nana ta ƙara sa Hajara ta bargidan cikin kuka tana cewa "Ita gidan Uncle ɗinta zata tafi kuma bazata ƙara dawo nan gidan ba tunda faɗa a ke mata. Nana da Salis sai kiranta sukeyi amma tayi banza dasu har ta bar gidan. Salis ya ce "Kinga manta da ita da kanta zata dawo ta ce shima Uncle ɗin nata ya mata faɗa, suka kwashe da dariya Salis na ruƙo hannunta yana sakar mata kiss har ya kai ga zarcewa, itama ta shiga mayar masa da martani cikin so da kwanar nunansu. Suna cikin haka sukajiyo Muryar Abubakar ya tashi a barci yana kuka, dole yasa Salis sakinta yana mai da nunfashi ita kuma ta nufi sama gurin ɗan nasu.

AJ ya ce "Innah ta sarkin tambaya to wannan ɗin fafinkine. Ya faɗa yana kallon Zara da take kallon Hajara cikin wani sabon mamakin. Zara ta ce "Wai dama wannan hotunan suna nan har yanzu? AJ ya ce "Wannan ai hutunan tarishi ne kinga ai dole mu kula dasu. "Uncle Ya sunan fafin nawa? Cewar Hajara tana kallon hoton har yanzu. AJ ya ce "Innah ta tambayar taki tana yawa. Ai kuwa ta buɗe baki zatayi kuka Zara ta ce "Sorry Innar mu ga Bybe ya tashi je ki ɗauko min shi. Tana jin haka ta miƙe da gudu ta nufin ɗakin da yaron yake. Aj ya kamo ta ya ce You ar the best in my life. Itama ta ce kaine komai nawa mijina. Ya haɗa bakinsa a guri guda yana kallon hoton da Hajara ta zo dashi mai ɗauke da hotunan su dukkan su anrubuta *ADDININMU* aJikinsa da manyan harufa. A fili suka haɗa baki da cewar "Alhamdulillh da kasancewarmu a cikin addininn Musulunci.

*Nima S REZA na ce Alhamdulillh,Alhamdulillh. Tammad bihamdillah.*

*Ha ƙiƙa littafin ADDININMU ya faɗakar sosai da sosai, babu abunda zance sai godiya ga Allah. I love all my fan's irin sosai ɗinnan, Allah ya ƙara haɗa kan al'ummar musulman duniya baki ɗaya, Allah ka san munafukai a cikin Addinin Musulunci Allah kai mana maganinsu, Allah ka shiryemu , Allah ka tabbatar damu a cikin Addinin Musulunci. Ya Allah suskuran da nayi a cikin wannan littafin Allah ka yafemin, abunda na faɗa daidai kuma Allah ka tabbatar da ladansa a garemu baki ɗaya . Mu kasance da ku wani lokaci masoyana ina sonku sosai da sosai, idan zan dawo zan dawo muku da labari mai zafi irin wanda kukeso da yardar Allah!*

*Kar a manta da min addu'a a kan gasar da nece na shiga, kuma in sha Allah idan result ya fito ko ban samu nasaraba zan sanar muku, amma dai muna fatan nasarar🤗* .

*Watpad*
Salis m Reza.

*Feecbook*
Salis m Reza

*Arewabooks*
Salis m Reza

*Gimal*
[email protected]

*Whasoop numbar*
08100785178

*Instagram*
*Salis m Reza.

*A ko'ina inada gurin da zan zanta da kowa idan da buƙatar hakan🥰🥰*

*S REZA ikonn Allah*
Chapter 67 · 0% Book details