← Book details Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 67

Sashe 46

Addininmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take Innah ta kwashe komai abunda a ka musu ita da Nana, tun daga marin da a ka fara mata a cikin gida izuwa gidan ƴan sanda da a ka kaisu, ga cin mutuncin da ƴan sandan suka musu, da taimakon da Salis ya musu shida abokin AJ ɗin, har sallamosu da a kayi, sannan ta ɗora da zamansu a asbiti da kuɗin da Dr ya kashe a kansu da irin kulawar da ya basu, aikuwa dai inna labarin ne ya ƙara dawo mata da komai sabo ta ci gaba da kuka ta ce "Tabbas Allah yayi i'nada sauran numfashi a duniya badan haka ba saide ka dawo kaga bana duniya, bansan lokacin da Nana ta kaini asbiti ba ban sani ba!

"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! AJ ya dinga furtawa yana mai sakin kuka da jin tausayin inar ya ƙara rushewa da kuka ya na ce wa "Walhi duk nine sila, ba haka nasoba dan Allah Innah ki hukuntani na cutar daku a kan son abun duniya, waiyo ni Abdul na kusa kashe ahalina da kaina. Ganin irin sambatun da yake ne yasa Innah fara bashi haƙuri a kan cewar haka Allah ya tsara zai faru ya bar kuka. Da kyar ya tsaya yana kallon Nana wacce duk sai yaji wani irin rauni a zuciyarsa jin irin halin da ta shiga, ya kafeta da ido yana jin kamar ya ɗauketa ya sakata a cikin sa ko zata huta da wannan kukan da yake sakata, rungumeta yayi yana shafa kanta da bayanta yana saka mata albarka ita kuma tayi luf a jikinsa tana jan hanci. Innah ta yi shiru tana tunanin me AJ zai ai kata ya sa shi irin wannan halin. Sai da suka nutsu kafin AJ ya fara magana kamar haka...

"Kuskure na farko da nafara yi a yanzu shine wannan mutumin da ya sa a ka kaiku gidan ƴan sanda to yarinyarsa ita ɗin budurwata ce. Gaban Nana ya bada wani darammm tana jin shikenan ta tabbata. "Amma ni ina sontane badan komaiba sai dan dukiyar iyayenta duk da kuwa suɗin ba musulmai bane. Ita kuma ta na sona tsakani da Allah, sai nayi amfani da son da takemin nake turata ta sato min kuɗi a gidan su. AJ ya sanar dasu komai dake tsakanin sa da Sarah, duk yawan kuɗin da ta bashi saida ya faɗa musu har zuwa lokacin da a ka kamata. Ya sanar musu irin ƙiyayyar da mahaifinta ke yiwa Musulmai, saida ya gama komai Innah ta ce ...

"To saboda baka son ya kamaka ne yasa ka gudu shi kuma ya zo ya tafi damu ko kuma kana cikin garinnan kaiwai dai ka ɓoyene? AJ yayi shiru yana tsoron sanar dasu asalin abunda ya jawo wannan tashin hankalin. Shin to aure zaice yayi ko kuma me? Shin da wani ido zai kalli inna ya ce yayi aure, auranma mahaifiyar Salis, kai no bazan iya ba, kawai na je na saketa sai ta auri tsohon mijinta ni kuma ta bani kuɗina amma dai ba zan tona wannan sirrin ba.

"Abduljabaru kayi shiru kuma muna sauraron ka. Firgigitin ya dawo da ga tunaninsa yana kallon Nana da ta ƙura masa ido da a lamar dai a kwai magana a bakinta. AJ ya ce "kaman yanda na sanar da ke cewar aiki aka ɗaukemu izuwa ƙasar Niger kuma duk mun dawo lafiya. Ya faɗi maganar wacce daga ji kasan ƙarya yayi. Ya ci gaba da cewar bayan na dawo na samu labarin abunda a ka muku shinefa na je gidansa, to a can ya sa a ka rufeni muda wasu mutane. Haka dai AJ ya sanar dasu abin da ya faru a gidan Daniyel a kan ƙonesu da zaiyi, har zuwa asibitin da a ka kaisu da kuma shigowarsa yanzu. Amma bai sanar musu da cewar shida baban su Salis bane kawai dai ya haɗa ne domin wanke kansa, ya haɗa da dukan da yasha a hannun sojoji.

Nann ma dai wani kukan suka sha jin wai ƙonesu a kaso yi, suma sun tausaya masa sosai,, kafin Innah ta ce "To Allah dai ya kiyaye gaba, yanzu sai ka keyaye, babu ruwanka da yarinyarsa, ka fita a harkarta, AJ ya ce "In sha Allah Innah.

Innha ta ce "To aikin me kukaje yi a Niger É—in? Cikin ruÉ—ewa ya ce "Amma am dama fa wani uban gidanmune ya ce muje tonun zinare wai ana samu sosai, shinefa ya fara bamu kuÉ—i wai kowa ya sallami iyalansa kafin mu dawo. "To yanzu kun samo zinaren ne? "Eh mun samo amma babu yawa saboda bamu daÉ—e ba. "To Allah yayi albarka, yanzu sai ka tsaya ka nutsu kasan me kakeyi. Nana da AJ sukayi dariya jin wai kasan mekakeyi.

*HAJIYA BABBA POV*

Numbar AJ ta shiga kira amma ana sanar mata cewar a kashe ta ke, ta ma rasa wani irin tunani zatayi yanzu, kawai ta samashe ya saketa ta bashi kuɗin sa kowa ya kama hanyar gabansa, to ya zatayi da Muhammad. A fili ta ce "Kai co na! Rashin haƙuri baiyiba kwata-ƙwata ma sati nawa da yin auran! Shekara nawa nayi ba tare da namij ba, amma na kasa jure wannan lokacin, a'she dai Salis da Laɗifa taimakona suke sonyi amma na ƙi yarda, na shiga uku ina zan sa kaina.

Ɓangaren su Muhammad kuwa Salis ne ke bashi labarin irin cigaban da suka samu a harkar kasuwancinsu da irin nasarorin da suka ƙara samu. Shima Muhammad ya jin-jinawa matar tasa. Haka sai suka dinga hira sosai a kan rayuwa, Titi da su Samuel ma duk sun saki jikin su Umar da Usman duk an kaisu ɓangaren da zasu zauna kafin su huta zuwa wani lokaci a shiga Katungu. Titi ma a gidan ta kwana ita da Usha. Nann fa Laɗifa da SAMUEL suka fara zama a tare. Ita dai a zahirin gaskiya tana sonsa shi kuma a da yana sha'awar ta ne kawai, yanzu kuwa sai yaji duk babu koɗaya kodan ita ɗin jininsace. Hakanne yasa a zaman da sukayi bai wani sake da itaba sai Usha ne ma yake ɗan janta da hira, shi kuwa gaba ɗaya hankalinsa yana ga surarr jikin Hadiza. Sarah da laɗifa a ɗaki ɗaya suka kwana hakanne ya ba Laɗifa damar gano komai dake tsakanin ta da AJ domin kuwa ta bigi cikinta. A wannan lokacin Laɗifa ta sake yarda da cewar AJ kawai yana bin ƴaƴan masu kuɗine ya na manne musu kuma daga yau idan ta ƙara ganinsa a gidansu walhi sai ta wulaƙan tashi.

Washe gari bayan sun gama breakfast wanda Hajiya Babba ta kasa cin komai kasan cewar ta tashi da ciwon kai, ga kuma abincin da bata son ganinsa kamar zatayi a'mmai. Bayan sun gama ne Hajiya Babba ta kalli Salis ta ce "Zaka rakani gidan su AJ domin zan kai masa gudun mawa kaga abun da ya sameshi shi bai kamata a barshi haka ba ko? Cikin sauri Salis ya ce "Ok Tom Hajiya amma Abba ya ce zan rakashi gidan abokinsa ki bari idan mun dawo sai na kaiki? Da sauri Sarah ta ce "Na san gidan zan rakata? "Muhammad ya ce "Hajiya bazaki bari ki sake hutawa ba? Ko dai zamu koma asbiti ne? Naga yanayin jikin naki ,ko a kira Dr yazo? Ta ce "No karka damu yanzu zan dawo kuma ba wani ciwo da nakeji. Hajiya Babba da ta ke jin cewar bazata iya cikekken minty biyar batare da sun haɗu da AJ ba ta yi saurin ce wa da Sarha "To ba damuwa idan har zaki gane gidan ai sai mu tafi. Laɗifa kuwa da take takaicin wannan abun ganin Sarah tayi hakane domin taga AJ, shi kuma Salis yayi hakane domar har ya dawo ya je yaga wannan shegiyar ƙanwar AJ ɗin da ya ce yana so. Ai kuwa a zuciyarta ta ce "Yau dai zan sai naga wannan yarinyar kuma naga shi AJ ɗin a ina ya ke, daga nann kuma na ci masa mutunci.

Da sauri ta ce "Hajiya nama zan rakaku? Hajiya Babba da bata son a sirinta ya tonu ta ce "No Auta ki zauna a gida yanzu zan dawo? Laɗifa ta ce "Haba mana zan iya takawa fa ƙafar bata ciwo yanzu na warke fa? Muhammad ya ce "A'a auta keda Samuel ku zauna a gida har mu dawo domin kuna buƙatar hutu, ga Anty Titi tana tare da ku kinji? Jin haka yasa ta ce "To amma ku dawo da wuri Pls?. Salis da Muhammad da Umar da Usman suka tafi gurin abokin Muhammad wanda shiɗin malamine domin nemo hukuncin auransa da matarsa shin auran yana nann ne tinda bata ƙara wani auran ba, ko dai sai an gyara auran duba da an daɗe ba'a tare. Bai sanar dasu abunda zaijeyi ba shi kaɗai ya barwa kansa hakan.

Hajiya Babba da Sarha ne a bakin gidan su AJ da safe. Hajiya ta ce da Sarah "Shiga ki ce ana sallama da AJ? Sarah ta kalleta ta ce "Ok i'm Coming. Ƙarasawa gurin mai shayin unguwar ta yi ta ce da yaron da yazo siyan shayi yazo ta aike shi. Gaba ɗaya ƴan gurin suka zuba mata ido domin kuwa turanci tayi. Yaron da bai san me take cewa ba ya ce "Mai shayi ana maka magana wai zata siya shayi? "Gaba ɗaya suka kwashe da dariya mai shayi ya ce "Hajiya na nawa kikeso? Sara ta ƙara Mai-maita abun da ta ce sai akayi sa'a wani ya gano abunda ta ke nufi shikuma ya sanarwa da yaron. Ai kuwa take yaron ya tafi kiran AJ ɗin. Suna tafiya kuwa sabuwar hira ta ɓarke a kan taiburin mai shayi. Wasu na yaba irin kyun da yarinyar ke dashi, wasu kuma suna zaginta saboda arniya ce, wasu kuma na gulmar me tazo yi gidan su AJ domin dai basu ganeta ba, kuma basu manta irin tashin hankalin da ya samu gidan su AJ ɗinba a kan idonsu.

Tasaye suke a jikin motar su, Hajiya Babba na jin kamar ta shiga gidan tsabar ruÉ—ewa.
Chapter 46 · 0% Book details