← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 128

Sashe 90

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari kamar kullum danayi sallar asuba ban koma bacciba, karatun Alkur'ani mai girma nayi, seda gari ya fara haske sannan na tashi na fara gyara gidan. Har yau bana girki a part ɗina, sedai mu haɗu muyi a part ɗin ammi, na safe Kuma kafinma nagama aikina ammi ta aiko ankawo mana..... suhailat tunda Aunty ta tasheta tayi sallah da ƙyar take ta tambayar "ina yaya, ko ba'agidan yake kwana bane.?" Aunty da aliya banza suka mata suka cigaba da sabgarsu ko tanka mata basuyiba. Kafin su fito, ammi ta shigo dakin da kanta sun gaisa, bayan sungama gaisawa ta dubi suhailat dake ta kallonta tace. "Wannan ƴar gidan Alhaji mainasara ce?" Aunty tace, "A'a mahaifinta kanine a gurinsa Ni kuma yayanane, amma Allah ya masa rasuwa tun tana yarinya shida mahaifiyarta, se rukunta ya koma hannunsa." cikin tausayawa ammi tace, "Allah sarki, Allah yajikansu ya gafarta musu" suka amsa baki ɗaya da "Ammeen" ammi ta ƙara cewa, "yaranshi nawa ne? har yau be kawo mana suba" murmushi Aunty tayi tace, "su huɗu ne, kuma duk mazane. Abunda yasa basu zoba saboda harkar kasuwancinsa duk sune akai, babban kuma kinsan suna saudiyya mabiyanshi kuma tare suke jinyarsa da yayah, suma su haidar ɗin kullum mukayi waya zancensu yaushe yayansu ze dawo Kano sunyi missing ɗinsa." Ammi na murmushi itama tace, "su a tsammaninsu Muhammad ze koma Kano da zamane?" Aunty tace, "ehhh mana ko kinfiso ya zauna anan?" Ammi tace, "ehhh gaskiya inda so samune nafiso ya zauna anan, amma shima naga yafison ya koma Kanon" Aunty tace, "to ai kinga can ya taso, a can komai nasa yake, kuma harkar kasuwancinsama duk yana can, zeyi wuya mutum yayi rayuwar Kano yazonan yaji daɗin rayuwa, kinsan nan da can da banbanci." Ammi tace "hakane kam to idan Allah yakaimu bayan babbar Sallah sesu koma Kanon da gabaɗaya" suhailat dake sauraren hirar tasu ta dubi Aunty tayi farat tace, "Aunty nima Dan Allah kibarni anan, idan yayan ze koma semu koma tare" wani kallo Aunty ta wurga mata sannan tace, "A'a, gobe zamu tafi tare" suhailat ta marairaice tace, "Please Aunty I want....." Aunty ta katseta cikin faɗa, "nace fa bazaki zaunaba gobe zamu tafi" ammi ta tari Aunty da faɗin, "haba Hajiya sauda kibarta mana ta ɗan kwana 2 tunda tanaso" Aunty tace, "Tana zuwa makaranta shiyasa" ammi na duban suhailat tace, "To kinji ɗiyata ashe da makarantarki, kiyi hakuri ki bitan ku tafi, idan kukayi hutu sekizo mana" suhailat batace komaiba, amma bataso hakaba, taso Aunty ta barta ta zauna anan ɗin kusa da yayanta, duk da batasan alaƙarsu da mutanen gidanba, amma ita wannan ba damuwarta bace, Ita dai tunda zata dinga ganin yayanta kullum zata zauna. Tun jiya da yamma ta kashe wayarta saboda kar mommy ta addabeta da kira, dan tunda taga Mustapha a gidannan tasa aranta ta samu gidan zama. (Suhailat badai hankaliba 🤣) hirar duniya ammi da Aunty suka shigayi. Aliya kuwa dama tana kitchen aunty ta turata suna aiki ita da umaimah da Aunty zuhura....

Se kusan ƙarfe goma nagama aikina, duk da ba wani aiki bane a gidan amma kullum haka nake, sena wanke komai nayi goge_goge, har kayan dana cire duk se na wankesu shiyasa bana kammala aikina da wuri. ina toilet ina wanka Aliya ta shigo part ɗin, fitowa kawai nayi daga wanka naganta zaune a bakin gado tana danna waya. Da mamaki nace mata, "ke yaushe kika shigo ko motsinki Banji ba" Aliya ta ajiye wayar hannunta tace, "yanzu na shigo na kawo muku kayan break, se yanzuma kika tashi kenan?" Ina karasawa gaban mudubi nace, "sekace wata ke, zanta bacci har safiya haka" cike da shaƙiyanci Aliya tace "nasani ko yanzu kin koya, tunda yanzu kina lole mana jikin yaya" ban kulataba nacigaba da shafa maina. Bayan mun shirya muka fito falo na haɗa tea nasha da soyayyiyar wainar kwai da dankali, ina ci ina yamutsa fuska ina babu daɗi tunda aliya tacemun ita tayi. Itama da bakinta baya shiru ba kyaleni tayiba, mayarmun take. Cin abincin nake amma hankalina yana kan kofar dakin yaya, so nake na ƙarasa cin abincin naje na dubo jikinnasa. ina gama karyawa na nufi dakinnashi, Aliya kuma na kitchen tana wanke kwanukan danayi amfani dasu. Amma abun mamaki Koda na buɗe Kofar dakinnasa senaga wayam bayananan, amma dakinnasa fess dashi se tashin kamshinsa yake dana room freshener. A part din ammi na tarar dashi suna hira da Aunty, cikin shirinsa da alamama fita zeyi. Naji daɗin yanda nagansa da alamun yaji sauƙi kenan. ban wani jima da zuwaba ya fita. Suhailat yauma taso ta shishshige masa amma be bata fuskar hakanba, daga gaisuwarta daya amsa be ƙara kallon koda inda takeba. Ita batason bayason ganintaba, saboda indai ya kalleta seya tuno da mommy, shikuma bayason ya dinga tuna mommy so yake yayi deleting ɗinta gabadaya daga cikin rayuwarsa ko tunata bayason ya dingayi. Yauma haka na wuni a part din ammi, munashan hira cikin nishadi, sosai zuwansu Aunty yaymun dadi. Aunty ta kirani daki ta tambayeni, ko akwai wata matsala a zamanmu da yaya, nace mata babu matsalar komai. nasiha ta ƙaramun akan zamantakewar aure, ta kuma bani wasu turaruka masu kamshi tace kullum kafin na kwanta na dinga tsugunno dashi, wani kuma na turara jikine dana shafawa harda na turare kaya duk ta bani. Cike da kunya na karba na mata Godiya. Yauma se dare na koma part dinmu, tun safe dana ganshi a part din ammi ban ƙara sakashi a idonaba dana dawo kuma banganshi a falo ba kamar yadda na zataba, haka na wuce ɗakina zuciyata babu daɗi, kewarsa duk ta cika mun zuciya kamar naje naganshi haka nakeji, amma bazan iyaba, tunda innaje bansan mezan ce masa yakawoniba.... Abangaren mustapha ma, zuciyarsa cike ta wuni da tunanin maryam har mamakin kansa yake akan yanda tunaninta ya yawaita acikin zuciyarsa. duk abunda zeyi tunaninta na makale a cikin zuciyarsa. yau kam yaji sauƙin jikinsa sosai, dan tunda ya tashi ciwon kan da ciwon marar yasarara masa, yayi zaton yauma zatazo ta ƙara dubasa amma yaji tsit, ya gama budget dinshi akanta yau idan tazo, amma ta bata masa shiri. zuciyarsa babu daɗi shima ya kwanta cike da takaici. (🙄 kai kaje mana, wannan miskilancin naka ya ishemu fa🤕🥺).....

Washegari su Aunty suka tafi tun safe, kamar na bisu haka naji. su ammi ma sunso su Aunty su ƙara kwanaki amma Aunty tace tafiya zasuyi saboda makarantar Aliya, wani satin zasu koma kuma zataje dangin babanta kafin su koma. Suhailat ma kamar tayi kuka, se botsare_botsare take tana bata rai, Aunty dai ko kulata batayiba tafiyace dai dole seta yita. Direban ammi ne ze kaisu gida, dan direban su Aunty tun a ranar daya kawosu ya juya ya koma. Wunin yau gabaɗaya cikin rashin walwala nayishi saboda tafiyar su Aunty. Danma munyi waya dasu saleemat ne da gwaggo, shiya ragemun kewar su antin.....

Har bayan sallar magriba ina part din ammi, bayan na idar da Sallah naji babu abunda nakeson ci se wainar fulawa. kitchen din ammi na shiga na hado kayan hadi na fara kwabawa, Aunty zuhura tazo diban abinci ta tarar ina kwabawa, tsokanata ta shigayi wai yau kuma babynnasu waina zeci, dariya nayi kawai bance mata komaiba. Na fara soyawa ammi ta shigo kitchen din tana faɗin, "Maryam dakanki kikeyi, kinsan ita waina idan mutum ne ya soya da kansa baya iyaci, dakin fadamun dana soya Miki da kaina ai, kokuma nasa umaimah ta soya Miki" cikin ladabi nace mata, "Ammi ai zan iyaci, agidama idan inaso ni nake soyawa da kaina" murmushi ammi tayi tace, "To ai yanzu da da ba ɗaya bane Maryam, sekiga yanzu kin soya kuma kinkasa ci." nace, "ammi fa zan iya da gaske" ammi tace, "toh shikenan ɗiyata sekin gama." Se bayan isha'i nagama soya wainar. Yawuna har tsinkewa yake tun kafin nagama, dibar tawa nayi acikin flaks sauran kuma na barwa su ammi. Part dinmu na wuce, akan dinning na aje flaks din sannan na nufi ɗakina, toilet na faɗa cikin sauri nayi wanka tare da dauro alwala. Shap_shap na shirya cikin wata doguwar rigar mara nauyi Black colour, wadda na turarata da turaren da Aunty ta bani, tun bayan sallar azhar nayi kabbasunta amma haryanzu kamshin yananan ajikin rigar. wanda ta bani na shafawa a jiki na shafe jikina dashi lungo da sako, turaren yanada daɗin kamshi sosai shiyasa naita mulkashi ajikina. Hijabi na zira na tada sallah, bayan na idar na fito falo batare dana cire hijabin jikinaba, flate na dakko a kitchen da robar yaji na dawo kan dinning na zuba wainata na faraci, ina tunanin har yanzu yaya bedawo ba...
Chapter 90 · 0% Book details