Sashe 54
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
............Nakasance ni macece me hassada gami da kyashi akan duk wanda naga wani yafini samun wani abu na rayuwa tun ina yar karamata,tun ina budurwa na baci da bin bokaye da malaman tsibbu". duban daddy mommy tayi tacigaba da magana. "Sulaiman yakamata ace kayi tunani akan yanda na dage kai nakeso da aure alhalin nakasance mace me shegen son kudi kai kuma baka da kudi a lokacin kuma Wanda kawuna yakeso yabani yafika kudi,amma na nadage kai nakeso. To kasani auranka danayima ina da dalilin yinsa kuma ban aureka da niyyar zama dakai na dindinba,na aurekane amatsayin garkuwa wanda dazaran nagama cimma burina zan tilasta maka ka sakeni" dasauri daddy yadago da niyyar yiwa mommy magana amma tadaga masa hannu alamar yadakata sannan taci gaba da magana. "Na aurekane bisa umarnin wani boka danaje gurinsa akan wata bukatata yakuma tabbatarmun da bukatata bazata biyaba harse na auri miji irinka kamar yadda ya siffantamun, kuma gashi nayi nasara na aureka nacika burin dayasa na aureka tun aurenmu bajimawa, amma bazan fada muku ko wanne buri bane saboda ba huruminku bane. lokacin da burinnawa yagama cika ina kokarin cewa kasakeni wannan arzikin yazomana shiyasa nafasa rabuwa dakai. Idan baka mantaba afarkon aurenmu nayi barin ciki toba barewa yayiba nina zubar dashi da kaina domin banason haihuwa dakai, daganan kuma nafarashan magungunan hana daukar ciki, daga baya kuma Allah yanunamun ikonsa duk da inashan maganin amma sega cikin sadiq, a lokacin naso zubar dashi kawai kuma sena hakura. Tun lokacin daka kawo mustapha haka kawai naji tsanar yaron ta cikamun zuciya sannan kuma zuciyata ta kasa aminta da labarin daka bani akan yanda kasamesa. hakan yasa tun yana dan jariri nayita gasa masa azaba iri_iri wanda kai sulaiman baka saniba kana gurin aiki, Allah ne kawai yayi mustapha yanada rabon shan ruwa a duniya datuni yadade da mutuwa domin na dade ina yunkurin kasheshi. bayyanar dukiyar mustapha shine abu nafarko mafi rinjaye acikin duk wani abu nafarinciki daya sameni arayuwata,bansan yazan misalta muku farin cikin danayiba a wannan lokacin, domin dama nican burina sonake inzama matar hamshakin me kudi wanda duniya tasanshi sekuma gashi Allah yakawowa sulaiman kudin a lokacin da banyi zatoba. Sedai kuma wata matsala daya da sulaiman yacemun dazarar mustapha ya girma ze damka masa dukiyarsa gaba daya a hannunsa. Alokacin daya fadamun natada hankalina naita fadace_fadace domin dai sulaiman yacemun yajanye ra'ayinsa amma yaki. Nanfa nafara tunanin hanyar dazanbi dan ganin nahana wannan kudiri nashi cika. haka muka cigaba da rayuwa ina nunawa mustapha kauna fiye da kowa a duniyarnan kuma koda wasa bantaba fadawa wani bani nahaifi mustapha ba domin ina da muradin nakasheshi dazarar yakai wasu shekaru kuma banason agane nina kasheshidin. sulaiman yasakarmun bakin aljihu inayin yanda naso da kudi hakan yasa nabazama gurin bokaye Neman maganin dazan hallaka mustapha cikin sauki nakuma mallake sulaiman akan se abunda nace yayi shizeyi. wata kawata hannatu ita tahadani da wani boka wanda shiyakemun aiki har yanzu wato *boka tsidau* ta kuma tabbatarmun da aikinshi tamkar yanka wuka yake duk abunda nakeso yamun zemun amma fa yana bada aiki masu wahala gami da cazar kudi. nace mata nidai indai bukatata zata biya koma menene zanyi kuma ko nawane zan kashe ba matsala bane. can wani kursungumin kauye a garin katsina hindatu ta kaini inda anan bokan yake da zama, muna zuwa tunkafin nafada masa bukatata yasanarmun hakan yasa nakara gasgasta zancen hindatu na aikinsa nada kyau, domin alamar karfi tanaga me kiba. abu nafarko dayasanarnun zanyi shine nafara kawar da duk wani wanda yasan mustapha badanmu bane, ma'ana nakasheshi. Godiya namasa nadawo gida.Tun daga ranar nafara bin duk hanyar dazanbi danganin na kashe isma'il domin a iya sanina shikadaine yasan wannan maganar, dama kuma inajin haushin yanda sulaiman yake sakasa a komai na harkar kasuwancinsa kuma damacan bama wani shiri dashi duk da yakasance mijin kanwata. Isma'il gabadaya a kowanne sati yana abuja yana kula da kamfanin dake can na sulaiman, se weekend yake dawowa nan kano, ko tausayin suhailat banjiba a lokacin nasa aka cire burkin motar sulaiman wata ranar Monday da safe ranar ze koma abuja, Ashe ni bansaniba jamila ta tatakura masa a daren da ana gobe zasuyi tafiyar akan tanaso tabishi abujan itama shine suka shirya suka tafi tare. dama suhailat a gurina ta kwana aranar. Tafiyar sassafe zasuyi shiyasa jamila batazo mana sallamaba, kuma tasan idan tazo bazan barta su tafi tareba saboda banason tayi nisa dani, shiyasa idan tace zata bishi nake hanawa. seda suka fice daga gidan sannan tamun text a wayata nibanmaga text dinba seda aka kira sulaiman akace sunyi hatsari duk sun rasu, hankalina bakaramin tashi yayiba danaji harda yar'uwata tuggun dana hada yakama nayi kuka kuma nayi takaici amma duk da haka bansadudaba bayan rasuwar tasu komai yalafa nakoma gurin boka, yacemun aikina akan mustapha baze tafi yadda akesoba harse na hada da namiji saurayi wanda betaba aureba kuma yakasance jinin sulaimanne,amma a lokacin yabani maganin dazanyi amfani dashi domin na mallake sulaiman din, kuma maganin yamun aiki yanda nakeso. Nikuma a lokacin na fito da kissa da kisisina tare da biyayya akan sulaiman tamkar wata ta Allah, duk dan na kawar da tunaninsa akan zargina da wani abu agaba. Haka nacigaba da rainon suhailat cikin tsananin so da kaunarta domin ita nake gani ta debemun kewar yar'uwata rabin jikina. Naso mustapha ya lalace yanda sulaiman zeji ya tsaneshi shiyasa na turashi karatu kasar waje amma abun Allah seshi be lalaceba yayana nacikina su suka lalace. Nayi nasarar mantar da sulaiman komai akan mustapha saboda yanda kullum cikin zancen dukiya batasa bace ta mustapha ce. Ni kuma da raina da lafiyata bazan bari wannan dinbin dukiyar ta tserewa yayanaba inaji ina gani. Lokacin da yarana sadiq da faruq suka tasa suka zama samari senajewa da boka tsidau da maganar ga samarin ansamu,yayan sulaiman nema nacikinsa kuma bani da matsala dasu zasumun komai danakeso,tunda yayanane. boka yacemun akwai maganin daze bani inawa mustapha amfani dashi ze mutu cikin sauki, amma wannan azurfar dake tsintsiyar hannunsa wadda da ita mahaifiyarsa tabawa sulaiman acikin jakarnan tana bashi kariya ga sihiri kuma mustapha mutum ne meriko da addini gami da addu'a dan haka sedai muyi wani aikin daban. Aikin da boka ya bani shine yanason daya daga cikin yayana yayiwa yanmata guda goma shabiyar fyade sannan kuma daga baya aljanunsa zasu shanye jinin jikinsu su mutu,bayan ya shanye wanda yazuba na budurcinsu. daga zarar nayi haka to burina guda biyu ze cika aduniya na mutuwar mustapha da mutuwar sulaiman aranar da akayiwa yarinya ta goma shabiyar din fyaden koda bata mutuba. Gaskiya wannan aikin da boka yabani ya girgizani bakadanba domin bansan ina zansamu yanmataba wadanda zanyi aiki dasuba a lokacin. Alokacin inada wata me aiki dake kula da part dina wadda bazatafi shekara 40 ba, se sulaiman ya nuna yana sonta ze aureta. aiko nan nayita bala'i na kuma koreta, sulaiman yata bani hakuri domin Alokacin aikin boka nacinsa se'abunda nace yayi shiyakeyi. Da wannan abun na fake aka dinga kawomun yara yanmata aikatau sadiq na musu Fyade sena maidasu gurin iyayensu su karasa mutuwa acan. Da farko faruq nafarawa maganar bukatata domin naga duk cikin yayana yafi kowa zuciya gami da kwazontaka amma faruq yaki bani hadin kai se wasu wa'azizzika daya shiga yimun danaga yana kokarin tonamun adiri sena bada sunansa gurin boka ya rufe masa baki tundaga lokacin faruq ya koma tamkar kurma seya wuni yakwana beyi maganaba. kuma kome akayi baze iya magana akaiba sedai yabi mutum da ido kawai. Lokacin dana tunkari sadiq da maganar nayi mamaki daya amincemun da gaggawa domin banyi zaton haka daga gareshiba kasancewarsa mutumin kirki azahiri, daga lokacinma senadena zuwa gurin boka da kaina sedai natura sadiq yajemun. yanmata uku aka farayiwa fyaden wanda duk wata tsohuwace take kawomun su daga kauyensu daga baya mutanen garin suka ganeta se sukasa aka kamata har gidan yari aka akaita nikuma namata gargadi da cewa matukar tabari sunana yafito acikin abun senasa ankarar da duka danginta hakan yasa ta tsorata taki fadin sunana bansan kuma yasuka karkeba ita da mahukunta. talatu itace farkon me aikina kuma ita kadaice tasan sirrina saboda abun yafaru akan jikarta da wasu yan garin su guda biyu data kawomun. sena koma bin kauyuka daban_daban inda ba'asanniba inasa ana dakkomun yara aikatau ahaka har'akayiwa yara 14 fyaden saura daya kenan. Boka yatabbatarmun dacewa aranar da akayiwa ta cikon 15 din mustapha da sulaiman bazasu kwana arayeba. Maryam itace yarinyar danasa wata kawata lami ta nemomin tun ranar da aka kawo maryam gidannan a kallon farko dana mata naji gabana yayanke yafadi, wanda kuma bansan daliliba. hakan yasa nake yawan kallonta dan ganinakeyi kamar zangano wani abu atattare da ita. Maryam itace ta zamo silar lalacewar kowanne shirina." Numfashi mommy taja ta kalli mustapha fuskarta cike da tsantsar mugunta tace, "bayan duk wannan abubuwan namaka asirin da bazaka taba iya wata mu'amalar aure da wata diya maceba, hakan yasa ko tunanin aure bakayi. Boka tsidaune yacemun matukar nabari kayi aure kowanne shirina ze lalace. Lokacin da suhailat tazomun dabatun kai takeso hankalina bakaramin tashi yayiba, saboda nasan sulaiman yanajin zancen zece ayi auranku, amma ganin yanda suhailat din duk tabi tadamu sena maka zancen kuma nace kasota,amma seta gama karatu zakuyi aure,duk dan hankalinta ya kwanta amma banada niyyar kuyi aureba. Nabi hanyoyi dadama domin ganin na muzantaka gami da bataka a idon jama'a amma banyi nasaraba, har yan kamfaninku nahada baki dasu duk dan abata maka suna. idan zaka tuna wata rana da P.A tazo office dinka tayi tari amatsayin asmarta tatashi hartazo zata fadi ka tallafota jikinka, alokacin manager ya daddaukeku photo a wayarsa da niyyar ya watsashi aduniya amatsayin kuna lalata amma ita P.A din ta gogeshi saboda tace tana sonka bazata iya ahada baki da ita a cutar dakaiba. Na kyaletane kawai saboda nasamu hanyar dazan kasheka cikin sauki wato wannan cutar dakayi ta watanni. wani maganin boka yabani yace inmaka turare dashi cikin dare, zanga abun mamaki. Cikin Daren ranar da sadiq yakawomun maganin nazo namaka turaren a lokacin ma idanunka biyu nace maganin tsarin jiki zanmaka. Shine da safe katashi da wannan ciwon, dalilin dayasa kenan nakafe baza'a maka maganin hausaba, amma saboda takurawar saudart seda takira malaminnan, maganin malaminnan yana aiki sosai hakan yasa namisanya