Sashe 101
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
..........Kamar ta watsa masa garwashin wuta a jiki haka yaji saboda tsabar takaici, da ƙarfin gaske kamar ze ballata ya rabata da jikinsa wani wawan mari ya wanketa da shi, seda jinta ya ɗauke na wucen gadi saboda ƙarfin marin. kamar wata kara ya cillar da ita ta fadi ta baya yayi gaba abinsa yana jin wani irin zafi a cikin ransa. _"wanne irin sakaci yayi da har yarinyar ta rainashi haka_" ya faɗi haka a ranshi danshi a ganinshi wannan ba ƙaramin raini bane. kwafa yayi kawai ya danne ɓacin ransa ya shiga part din ammi. Umaimah da kyar ta yunkura ta iya tashi hannunta dafe da kuncinta cikin tsananin baƙin ciki da kunar zuci, part din mama ta nufa tana hawaye dan fitarma da zatayi gabadaya taji ta fitar mata a rai, kuma bazata iya komawa part din ammi ba dan batasan da idon zata kalleshiba. mama na ɗakinta Umaimah ta shiga falo ta zauna akan kujera tana rusa kuka, haushin fareedah gabadaya ya cika mata zuciya, tunda gashi ta aiwatar da abunda tace ɗin tayi kuma ba'aci nasaraba, yanzu batasan wanne mataki ze ɗauka akantaba akan abunda ta masa....Mustapha sama_sama suka gaisa da ammi, duk da yadda yaso boye ɓacin ransa amma seda ammi ta gane. harta tambayeshi da faɗin "NOOR kana lafiya kuwa?" daga mata kai kawai yayi alamar eh. Ammi bata kuma ce masa komaiba se ido data tsareshi dashi, dan tasan ba haka bane faɗa kawai yayi. seda aka kira sallar magriba ya mata sallama ya nufi masallaci. Bayan anyi sallah mama tataso umaimah a gaba suka zo part ɗin ammi, ammi na kitchen tana ƙarasa girki ita da zuhura taji mama na kwada mata kira. Fitowa tayi tana faɗin "lafiya mama?" Mama ta dubi umaimah dataci kukanta ta koshi tace, "yarki ce na fito na sameta tanata kuka kamar wadda aka ce mata kin mutu, kuma na mata tambayar duniyarnan meyafaru taƙi bani amsa, shine nace bari inzo ko ke kinsan meyafaru" ammi ta dubi umaimah da kyau tace, "Auta meyafaru?" Umaimah ta girgiza mata kai alamar a'a. Ammi tace, "baki da bakine ina tambayarki kina gyada mun kai kamar kadangaruwa" umaimah cikin muryar data ci kuka ta koshi tace,"ba komai" ammi tace, "kukan daɗi kike kenan?" umaimah data fara tsorata da yanda ammi take mata magana tace, "A'a" ammi ta tabe baki tai komawarta kitchen. umaimah ta shige ɗakinta cikin mamakin yanda ammi ta mata, tasan halin ammi zata yi ta tattalinka tana rarrashinta akan abu, amma idan ka isheta seta kyaleka tayi banza dakai. mama tabi ammi kitchen tana faɗin, "dama wai ba daga nan take bane?" Ammi tace, "nifa lafiya kalau muka rabu da ita, zataje gidan zulfa (kanwar mamanta) data kirata tace taje, toni banmasan bata tafiba ashe part ɗinki tayi tana kukan banza." Mama tace, "to me akai mata?" Ammi tace, "wlh mama bansaniba, kwana biyunnan na lura akwai abunda ke damunta bata da aiki sedai ta zauna taita kunci ita kaɗai, na tambayeta, na tambayeta meyake damunta amma yarinyarnan kullum setacemun ba komai shiyasa na watsar da ita kawai" zuhura dake jinsu tayi murmushi kawai dan tasan meke damun umaiman. Mama tace, "ikon Allah, to ko dai rashin auren dabatayi bane ya fara damunta yanzu?" Ammi tace, "Rashin aure kuma?" mama tace, "eh mana, kila yanzu abun ya fara damunta" ammi ta tabe baki tace, "tasan ze dametan take korar duk wanda yazo da sunan aurannata" mama tace, "ai kinsan yarinta, yanzu kuma ta fara hankali shine abun ze dameta." Ammi tace, "to ai ba damuwa ya kamata ta zauna tayi tayiba, setayi addu'a Allah yakawo mata mijin nagari tayi auran" mama tace, "hakane, Allah ya kyauta" A bakin part ɗin ammi muka haɗu da mama zan fito ita kuma zata fita, gaisawa mukayi cikin fara'a na wuce ciki. har bayan sallah isha'i ina part ɗin ammi, tare muka ƙarasa girki da muka gama muka zauna nida aunty zuhura muna hira. umaimah ce ta fito daga ɗakinta bata kalli kowa a cikinmu ba ta wuce ɗakin ammi. Ammi na toilet tana wankewa umaimah ta shiga, har toilet din umaimah ta bita, tsayawa tayi a bakin kofa tace, "Amminah sannu da aiki" fuska babu walwala ammi tace, "yawwa" umaimah ta ƙarasa cikin toilet din tana faɗin "ammi kawo na tayaki" ammi tace, "barshi" a taƙaice. umaimah jiki a sanyaye ta koma ɗaki ta zauna a ƙasa ta dafe kuncinta da har yanzu take jinsa wani dimmm saboda marin datasha. 5 minutes later ammi ta fito, bata ko kalli inda umaimah takeba ta nemi guri ta zauna a bakin gado ta mike kafarta cikin gajiya. umaimah tatashi ta hau kan gadon, kwantar da kanta tayi a jikin ammi cikin shagwaba tace, "Amminah dan Allah kiyi hakuri kidena fushi dani, wlh bana iya jurar fishinki ko kaɗan" ammi ta harareta tace, "me kikamun dazanyi fushi dake" umaimah tace, "kiyi hakuri dai amminah Please" ammi ta sauke numfashi tace, "to naji, meke damunkine kwana biyunnan? kinsan dai bazan juri ganin ki a haka ba cikin damuwa" umaimah ta kama kame_kame ta rasa me zata cewa ammi. Ammi ta mata wani kallo tace, "Aure kike so ko umaimah?" gaban umaimah ne ya yanke ya faɗi ganin ammi ta ramkota, tabbas a yanzu babu abinda takeso sama da taga tayi aure. ƙasa tayi da kanta batace komaiba kwalla na cika mata ido. Ammi ta ɗan sassauta murya tace, "ki faɗamun mana daughter idan baniba waza ki faɗawa" umaimah ta ƙara rungume ammi tace, "Eh" tana sakin kuka ammi ta dubeta cike da tausayawa tace, "to ai ba kuka yakamata kiyiba, ko kuma kiyita kunci ba addu'a zakiyi Allah ya kawo miki mujin kiyi auren..." faɗa ammi tashiga yiwa umaimah sosai akan korar samari data dingayi a baya, ta faɗa mata. "Itafa rayuwa komai yazo maka a matsayin kaddararka karba kakeyi hannu bibbiyu, idan kace dole bazakayi aure ba, seka samu irin mijin da zuciyarka takeso zaka mutu bakayi aureba ballema ita umaimah data tsawwala akan yanda takeso mijin dazata aura ya kasance zeyi wuya ta samu, yanzu gashi ta doshi kusan shekara 30 a gida babu auren babu manemi, tunda manemanma yanzu babu, dama ita mace ai lokaci gareta, idan ta kai wani munzalin samarin ma ɗauke ƙafa suke" nasiha dai sosai ammi ta mata, umaimah harda kuka, ammi ta rarrasheta tace ta dage da addu'a kawai. umaimah kamar ta faɗawa ammi son mustapha ne ke damunta, amma dai ta daure bata faɗa matanba.