← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 128

Sashe 2

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jan jiki nayi nadawo tsakar gida,hawayene masu zafi kawai suke fita daga idona.bansan menayiwa gwaggo ladiba,ta tsaneni,kullum cikin azabtar dani takeyi.abincin daban karasa Ciba kenan,na tattara kayan na fara wanke_wanke.inayi ina sharar hawaye. Seda nagama na maida komai muhallinsa. Girkin abincin rana na Dora,shinkafa da miya gwaggo tace na dafa.dorawa nayi.bandaki na wanke kafin shinkafar ta tafasa na tace. Seda naga girkin sannan na faki idon gwaggo,na Dora ruwan wanka,saboda banda kauri babu abunda nakeyi.daki na kaimata abincin duka.wanka nayi,na wanke hakorana Tass da gawayi,domin duk kudinnan da gwaggo take samu,amma bani da MacLean da burush.alwalar sallar azhar na dauro.saboda har anfara kiran sallar.bayan nagama shiryawa nayi sallah.waken suya na auno,na jika zankai markaden awarar yamma......

***************
Karfe daya suhailat ta fito daga lecture,kuma daga ita tatashi kenan.amma tayiwa mommy karya tace mata se 6:00 pm zata tashi.kamar yadda ta saba kullum seta kara lokaci.wayarta ta dakko kirar iPhone 12,takira wani saurayinta akan tafito yazo ya dauketa.

Wata farar motace ta tsaya a gabanta,wani matashi ya fito yana fadada fara'arsa, babbar yarinya dama jiranki nake tayi,kinji dadin danaji kuwa dana ganki.murmushi ta masa tare da fadin,"nima naji dadin ganinka saboda inada bukatar adan yamutsani.dariya ya saki."kinkuwa samu tawan,gaban motar yabude mata ta shiga.domin suhailat macece me izza,daji da kai.zagayawa yayi yashige shima bayan ya rufe mata kofar.wani matsakaicin gida ya kaita,ba kowa agidan,hakan yasa da kanshi ya fito ya bude get din gidan.sannan suka shiga.karamin gida amma yayi matuakar kyau da tsaruwa.suna shiga bedroom din gidan ta fara cire kayan jikinta,.janta yayi suka fada kan gado............✍️

*BY*
*zeey kumurya*
https://chat.whatsapp.com/LvF2kmkAjrZ2UUUZ2ZzvaN

*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

*Bismillahirrahmanirrahim*

02

Bayan ya danyi mintuna,da jikawa na tace ruwan na kara daurayewa,nanufi gidan markaden.ina zuwa bansamu layiba,tsayawa nayi aka markadamun sannan na dawo gida.har lokacin gwaggo tana daki,yau gantalallun kawayennata basu zoba.seda na fara tace awarar sannan na kara hura wuta na daura.salimata ce ta shigo gidannamu da sallamarta.fadada fara'ata nayi ina mata sannu da zuwa.kujerar tsugunno ta dakko,ta zauna.nima wata na dakko na zauna a kusa da ita. "Saleemat harkin dawo Daga school, din." na dawo maryam ya gida ya aiki. "Lafiya kalau,saleemat.ya umma. "Umma tananan kalau,dama zuwa nayi nadan tayaki aiki kafin lokacin islamiyya yayi. Dasauri nace" haba saleemat,aina kusa gama aikin,awarafa kawai zan dafa,se dakan yaji.dakinyi zamanki agida kin taya umma aiki.hararata tayi,tace."umma ta gama aikinta,ki dakko yajin nadaka miki lokaci yana tafiya.sanin danayi kona roki saleemat babari zatayiba,yasana mike na nufi kitchen. Barkono na dakko da su maggi da gishiri.gabanta na kawo na ajiye mata.da kanta tatashi da dakko turmi,ta fara dakan.

Nima cabejin awara na dakko na dawo kusa da ita na zauna na fara yankawa.dubana saleemat tayi tace."yau gwaggo batananne. "tananan, na bata amsa atakaice. "Najita shiru ne,kuma banga kawayenta da suka saba zuwa sun zoba. "nima nayi mamaki saleemat da basu zoba,kila anjima ki gansu. Saleemat tace. "Gwarama da basu zoba,saboda zuwannasu ba alkhairi bane,duk du suke kara zuga gwaggo take miki abunda taga dama. "hmmm kawai nace. "Umma tace kwana 2 baki lekotaba. "dan Allah saleemat kibata hakuri insha Allah anjima idanna gama aikina da wuri,kafin nafara awarar magriba,zan lekota. "Allah yasa domin ke kullum haka kike baki da lokacin kanki,gaskiya gwaggo ladi muguwa ce,tana azatar dake sekace kedin ba jinintabace.tana zalintarki da yawa,ta hanaki samun ishashshen ilimi sannan kuma ta zaunar dake agida se bautar dake takeyi. Aiko abaiwa ta siyeki se haka,wannan......da sauri na rufe mata bakinta,ina waro idona waje, kofar dakin gwaggo na kalla,cike da tsananin tsoro. "Kiyi a hankali mana saleemat karta jiyoki. Ture hannuna tayi Daga bakinta,tana hararata,tace." Dalla can,dama ke shegen tsoronkine yake jamiki komai,da tun farko kinnuna mata baza ki juraba,ai bazata dinga tula miki wannan uban aikinba kamar jakaba. Wukar hannuna na'ajiye ina duban saleemat,nace."haba saleemat,mahaifiyatafa ta rasu mahaifina kuma kamar yadda gwaggo ta fada,guduwa yayi yabar mahaifiyata tunda cikina,kuma ba'asan kowa nasaba.gwaggo itace ta rikeni bayan rasuwar inna,nake zaune a gidanta,ta ciyar dani da abincinta kome namata banfadiba,tunda ta rikeni bata barni ina garari a titiba,shiyasa duk aikin danake mata banajin komai,domin ta cancanki haka. "Hmmm,maryam kenan,dududu shekarar gwaggo nawa tana rikeki,kumama dan tana rikonki seta miki wannan izayar. Numfashi naja,nace" saleemat ki godewa Allah daya barki da iyayenki,rashin iyaye bakaramin masifa da bala'i bane,burina arayuwa inyi ilimi me zurfi,amma hakan besamuba,nasan da mahaifiyata tananan da rai dako me zatayi setayi wajen ganin nasamu ilimi.na karshe zancen idona yana ciccikowa da hawaye.dafa kafadata saleemat tayi tace."Kiyi hakuri Maryam,kowa dakika gani a duniyarnan datasa kaddarar,ke taki jarrabawar kenan,kuma kidena yarda da maganar gwaggo datake cewa,babanki ya gudu, be zama lallai gaskiya bane,kila kawai tana fadane danta bataki.kiyi hakuri wata rana se labari,kedai kawai kici gaba da'addu'a,zakiga komai yazo miki cikin sauki.hawayen daya zubomun na share nace shikenan saleemat nagode,insha Allah zan cigaba da addu'a. "Yawwa kawata share hawayen inbaki wani labari me dadi. Murmushin karfin hali nayi ina goge hawayena." Inajinki to bani labarin. Labarinta da saurayinta tashiga bani.saleemat tana sona sosai,tana kokarin ganin nayi farin ciki akodayaushe,shiyasa na bata wani babban matsayi araina.tana bani labarin har muka gama abunda mukeyi.se wajen karfe uku da rabi tatafi saboda lokacin islamiyya ya yayi.kamar karta tafi haka naji,amma babu yanda zanyi.sallar la'asar nayi.bayan na idar gwaggo ta kirani ta bani abincin rana,ina gamaci na hau yanka awarar Dana dafa..........

Sai da 5:00pm ta wuce kamal ya sauke suhailat a department dinsu.sallama sukayi ya tafi.kiran mommy tayi taturo mata da driver domin ita tafi karfin waya da driver. mintuna goma shabiyar,se gashi ya karaso school din.tana hangosa ta nufo inda yake,fuskarta a hade,se wani ciccin magani take,tana yatsina fuska sekace wata basarakiya.saboda jijji da kanta da uban girman kanta ko kawar arziki bata da ita.gani takeyi tafi karfin kula kowacce yarinya a school din. Dasauri driver ya fito daga motar yana bude mata bayan motar.wani kallon banza tabishi dashi. "Seyanzu kaga damar zuwa seda gama shanyani,tun yaushe nake jiranka,ta fadi hakan tana jifansa da wani mugun kallo. " yanzu duk saurin danayi,da gudun dana dinga kwararawa yarinyarnan bata ganiba,ya fadi hakan aransa.amma a fili seyace"kiyi hakuri hajiya insha Allah hakan bazata kara faruwaba,kinsan hanyar da akwai gosl....."Dalla malam ni shiga kajani,banason wani bayaninka na banza da wofi.ta katsesa cikin tsawa. Dasauri ya shiga gaban motar bayan ta shiga itama,suka dauki hanya.

Ba kowa a falon kasa,sama ta haura nanma ba kowa,dakinta ta nufa.kamar yadda ta fita ta barshi kaca_kaca haka ta dawo tatarar dashi,wani dogon tsaki taja,jakar hannunta kawai ta ajiye ta nufi dakin mommy.

Mommy! Mommy! Ta shiga kwala mata kira. "Na'am daughter nah,harkin dawo.yamutsa fuska tayi tana zama a gefen mommy. "nadawo mommy amma nayi matukar gajiya." Ai dole my daughter throughout fa yau kina school ai dole ki gaji. "Niba wannanbama mommy, wai har yanzu ba'a samo me aikiba,dakinafa yanda nafita na barshi haka nadawo na samesa.kaca_kaca bakiji yanda raina ya baciba.dafa kafadarta mommy tayi,am sorry daughter ananan ana binkitawa,amma bari zansa su talatu ki gyara miki dakin yanzu.bata fuska tayi nifa tsofaffinan bawani iya gyara sukayiba. " kidaiyi hakuri daughter kiyi maleji,kafin asamo yarinya. "Shikenan mommy bari naje na dubo yaya,yau gabadaya nayi missing dinsa. Tafadi hakan tana mikewa tare da ficewa daga dakin.murmushi kawai mommy tayi.

Yana zaune a falonsa,akan 3 star wayarsa yake lallatsawa,suhailat ta shigo dakin,fuskarta dauke da murmushi kamar ba itace,wannan Mara fara'arba,me kallon kowa a wulakance,kodagowa beyiba balle ya kalli inda take.zama tayi agefensa,tare da kwantawa ajikinsa tana shakar daddadan kamshinsa. "Babynah I missed you,ta rada masa hakan a kunnensa.ahankali ya dago da kansa,yana jifanta da wani rikirkitaccen kallo,batare da yace mata komaiba.hannunta ta fara jawo dashi ajikinsa,tana shashshafa bayansa, harshenta tafito dashi tana lasar wuyansa zuwa habarsa. Ahankali ta hade bakinsu guri daya tafa sucking tattausan lips dinsa.lumshe idonsa yayi badan yanajin komaiba,shi
kansa yana mamakin yanda duk wani Abu da suhailat take masa bayajin komai na feeling ajikinsa,ko wani canjin yanayi.

Ba ita kadaibama,harta da turawan dayayi rayuwa acikinsu matan koda sunyi hugging dinsa bayajin komai. Shikansa yana tambayar kansa anya kuwa yanada lafiya.jiyayi suhailat tana Neman wuce gona da iri,hakan yasashi dawowa daga duniyar daya tafi. Tureta yayi daga jikinsa,baya tayi tana fitar da numfashi dai_dai idonta harya canza kala tsabar jaraba,lips dinta na kasa ta taune,kara matsawa jikinsa tayi,a shagwabe tace"pls my baby,kabarni na kara sucking lips dinka,inajin dadi sosai,gakuma soft skin dinka bana gajiya da......wani mugun kallo daya wurga mata yasata saurin hadiye maganarta,kofa ya nuna mata da hannunsa cikin kakkausar murya yace"get out!! Sum_sum ta mike ta fice jikinta asanyaye,saboda tasan halinsa baya son musu,duk da tsananin sonda yake mata hakan bayahanashi cin ubanta,idan ta masa ba daidaiba.dafe kansa yayi tare da runtse idonsa.bayan ta fice daga dakin, aransa yake cewa,jarabar suhailat tayi yawa,dan bayason ta damune shiyasa yake kyaleta take masa abunda taso,amma ya lura kullum.iskancinnata kara yawa yakeyi,amma zeyi maganinta.kiran sallar magriba da'aka kirane yasashi mikewa,dakinsa ya koma yayi alwala a toilet dinsa,ya nufi masallacin dake manne ajikin gidansu.

Kafin magriba na kafa kaskon a warata saboda har anfara zuwa nema.ina tsaka da suyar awarar bayan sallar magriba, abun mamaki,gwaggo ta fito daga daki da saurinta. Maryam zo kije gidan lantana yanzunannan zaki karbomin wani sako,kiyi sauri sakonna saurine,kuma kinga da sauran awara karki zauna. "Toh gwaggo insha Allahu bazan zaunaba,dakina nanufa da niyyar in shiga na dakko hijabi,saboda na jikina yana dan kauri kaurin hayaki,amma gwaggo ta dakamun wata irin tsawa," gidan uwarwa zaki kuma bayan na fada miki sauri nakeyi. Da sauri nayi hanyar fita,jikina na rawa.lantana tana gandun sarki ne,da dan nisa tsakaninmu hakan yasa nake tafiya da dan sauri sauri.....

Text yayiwa mommy zeje gurin abokinsa,lukman saboda damunsa dayakeyi akan bayason zuwa wajensa sedaishi yayita zuwa.mommy tana ganin text dinsa tayi murmushi, domin dama sometimes yasaba mata hakan,idan zefada mata Abu befiya kirantaba,sedai ya mata text.reply ta masa akan Allah ya kiyaye hanya.shikadai yaja motarsa,yatafi batare da koda drivernsaba.......
Chapter 2 · 0% Book details