← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 128

Sashe 108

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bayan na gama cin abincin na zauna a falo muka cigaba da hira da Aunty zuhura, wayar ammi na hannuna na ajiye ta a gefe ban kira yayanba shima kuma be kira ba, Ni duk a tunanina yau ze dawo, shiyasa rashin kirannasa be dameniba. Se bayan sallar magriba fareedah ta tafi, bayan ta gama ƙara dora Umaimah akan gurbatacciyar hanya da munanan shawawarinta, ita kuma dayake bata da wayo ta yarda da shawarwarinnata, fareedah dazata tafi haka taita kallon Maryam harseda Maryam ɗin ta tsargu. har bayan sallar isha'i wayar ammi na hannuna ina dakon kiransa, Ni kaɗai ce zaune a falon yanzu, Aunty zuhura ta koma part dinta ammi kuma na ɗakin ta umaimah ma haka, tunanin yaya kawai nake da kewarsa ta cikamun zuciya, ammi ce ta shigo falon, zama tayi a kujerar dake fuskantata tace "kin kirashi kuwa?" Buɗe idona nayi a hankali nace "nakirashi ammi, amma wayar taƙi shiga" ammi tace "sharrin network ne, nasan ze kira anjima, may be shi idan yakira ta shigo" mikewa nayi na miƙa mata wayar nace "ammi gashi zan koma part dinmu na fara jin bacci" ammi tace "yau ba'anan zaki kwanaba, ko kinbar jin tsoron yanzu?" Nayi murmushi kawai, ammi tace "kiyi kwanciyarki anan, gobe idan yadawo seki koma" _"gobe kuma_?" na maimaita haka a raina, komawa nayi kan kujera na zauna saboda wani irin zafi danaji ya ziyarci raina, daure abinda naji araina nayi a hankali nace "Toh ammi Allah yakaimu" ammi tace "ameen" kwanciya nayi akan kujera zuciyata na mun suya, Ni inanan kewarsa ta hanani sukuni, inata shirye-shiryen tarbarsa, shi kuma yanacan yana sha'aninsa hankali kwance, yacemun yau ze dawo ashe se gobe, nasan tunda ammi ta faɗa haka ne, kuma gashi har dare ma yayi bedawo ɗinba, ta tabbata se goben, tashi nayi na koma ɗakin ammi na rage kayan jikina na kwanta ko wanka banyiba saboda yanda nake jin zuciyata babu daɗi, na daɗe da kwanciya inata juyi bansan sanda bacci ya kwasheniba, yau ma seda maryam tayi bacci mustapha ya samu kansa ya kira ammi, yau kam beyi nauyin bakinba, ya tambayi ammi Maryam, ammi ta shaida masa tayi bacci. Washegari tunda asuba da mukayi sallah muka fara aikin snacks na tarbar yaya bisa umarnin ammi, danni duk shirin danake na dawowarsa na manta da batun yi masa abun tarba, bayan mungama aikin, na koma part dinmu, yauma banyi sanyaba na ƙara gyara part dinnamu fiye da jiya, bayan nayi sallar la'asar naci abinci na kwanta bacci saboda gajiyar dake addabar jikina.....

Mustapha yau tun safe ya gama shirinsa na komawa Jos, amma Daddy ya hanashi tafiya, su haidar ma se roƙonsa suke ya ƙara kwanaki kar ya tafi yau, shidai murmushi kawai yake musu, shikanshi bayason ya tafiyar ya barsu, amma dole ya tafi a yau, dan wata irin kewar Maryam ce take addabarsa wanda idan begantaba a yau akwai matsala, kwana biyun da yayi be gantaba beji muryartaba jinsu yake kamar wata biyu sukayi rabonsu da juna, wajen 12 na rana,faruq ya kaishi super market ya lodowa Maryam kayan zaki, su sweets da choculates da popcorn, su kuma su ammi turaruka yasai musu kala_kala, se can yamma Daddy ya barshi ya tafi da ƙyar, su haidar kamar zasuyi kuka, shima cike da kewarsu ya barosu, a Jet din daddy za'a maidashi, dama driver'n ammi already ya koma Jos tun jiya da safe... Maryam bata jima tana baccinba ta tashi, ƙara gyara gadon tayi sannan ta shige wanka, cikin wani haddadden less black colour an masa zanen fulawa me kyau da orange colour ta shirya, ɗinkin riga da skirt, ɗinkin ya zauna dass a jikinta yayi matuƙar yi mata kyau, hips ɗinta ya fito sosai ajikin skirt, daurinta ta kafa irin na zamani wanda ya ƙara kawata kyawun kwalliyar tata, ɗan kunne da sarka da zobuna da abun hannu haɗi da agogo masu kyau tasaka, ta bulbule jikinta da turaruka masu sanyin kamshi da daɗi, sosai yau tayi kyau fiye da jiya kamar ka saceta, har aka kira sallar magriba tana gaban madubi tana shiryawa, duk da fushi take da yayannata amma so take ta burgeshi sosai, seda aka shiga sallah ta bar gaban madubin ta shimfida darduma ta zira hijabi ta tada sallah dama da alwalarta tayi tun da ta shiga wanka. Mustapha se daf da magriba suka ƙaraso gida, hakan yasa be shiga gidanba ya bawa megadi ajiyar kayan tsarabarsa ya nufi masallaci...........✍️

*BARKANMU da sallah, da fatan anyi sallah lafiya,ALLAH ya maimaita mana, ameen.*

_*JUMA'AT MUBARAK🕌🕋*_

*By*
*Zeey kumurya*
*ABIN DA KA SHUKA....!*

*BY*
*ZEEY KUMURYA*

*7️⃣4️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*
Chapter 108 · 0% Book details