Sashe 7
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nanfa inna tace bata isa ta auri,Wanda ba'ason asalinsaba,ita kuma mahaifiyata ta dage dole seshi takeso.inna kuma ta kafe tace sedai ta zaba,ko shi ita.amma mahaifiyata taki hakura dashi,har ciwo ne ya kwantar da ita.ganin tana kokarin mutuwa mahaifinta yace yabata shi.ita kuma inna tace be isaba.sedai idan mahaifiyata ta mutu.shikuma mahaifinta yace shiya haifi maryam,dan haka Wanda takeso ze bata baze mata auran doleba,kokuma yanaji yana gani ita kadai din dayake da ita yarasata.dama ita kadaice 'yarsu.inna tanaji tana gani aka daura auran mahaifiyata da mahaifina.inna tacemun,kwata kwata batason auran tayi iya yinta kar ayi auran,amma Allah yayi dole se'anyi.haka inna ta hakura,amma tace babu ita babu mahaifiyata. Bayan bikin befi da wata dayaba,Allah yayiwa kakana rasuwa.halin dasu inna suka shiga baze misaltuba.a lokacin mahaifiyata tayi Dana sanin bijirewa inna,tazo tana kukanta ta nemi yafiyarta domin ta gane duniyar ba gidan zama bace.itama inna a lokacin jikinta yayi sanyi,hakan yasa ta sassauta mata,amma bata sakko dukaba.a lokacinma tanata fama da laulayin dan karamin ciki.
Haka sukaciga da rayuwa,tsawon shekara uku.inna tacemun mahaifiyata bata taba zuwa ta kawo mata karar mahaifinaba,akan ya mata wani Abu ba daidai ba koya muzguna mata.kana ganin yanda suke rayuwama,kasan cikin kwanciyar hankali da jin dadi sukeyinta.duk da mahaifiyata Daga ta samu ciki baya wuce wata uku ya bare.amma kokadan mahaifina be nuna damuwarsaba,ko kuma ya canzawa mahaifiyata.ita cema take damuwa akan haka, shikuma yana kwantar mata da hankali.
Tayi barin ciki,yakai biyar Allah yayi dai zanzo duniya. Mahaifiyata tasha wuya akan cikina tamkar zata mutu haka take shan wahala.hakan yasa inna ta dakkota ta dawo da ita gidanta.duk shima suna tunanin ze bare kamar sauran.amma abun mamaki ana wuce wata uku,hudu se ciwo ya dauke,ta komar sumul da ita.ta koma gidanta suka cigaba da rainon cikina ita da mahaifina.soyayya sosai mahaifina yake nunawa cikin,tun lokacin yaketa siyan kayan haihuwa. Saboda murnar wannan cikin ya tsaya tunda haryakai wata shida.mahaifina dama akusuwar kantin kwari yake a shagon wani uban gidansa.inna tace mun,yana samu sosai.yanada rufin asirinsa.wata rana yaje kasuwa mahaifiyata taga har dare bedawoba.shida yake dawowa kafin magriba.hankalinta ya tashi,ta kira duk Wanda take tunanin suna tare an tabbatar mata daya taho gida lafiya kalau.shiru_shiru tana jiransa,amma har wajen goman dare shiru,bedawoba.zarar hijabinta tayi ta nufi gidan inna tana kuka ta sanar mata.itama inna ta girgiza sosai,amma ta daure ta kwantar wada mahaifiyata hankali.shiru_shiru har cikin dare bedawoba.abun kamar wasa har washegari.duk inda ake tunanin za'a sameshi anje bayanan.hanakalin mahaifiyatafa ya tashi bataci batasha se aikin kuka.tun ana saran ganinsa har kwanaki suka shude babu shi,babu labarinsa.nan maganganu suka dinga yawo akan ya gudu yabar mahaifiyata,dama abunda yasa yake zaune da ita danbata haihu bane,yanzu kuma tunda yaga zata haihu shine ya gudu ya barta.bayason wahalar 'yaya.tundaga ranar mahaifiyata ta koma,bata da aiki se kuka,tun inna tana rarrshinta harta zuba mata ido.haka tacigaba da rainon cikina cikin bakin ciki.ranar wata juma'a da yamma ta haifeni.a gida ta haihu.bayan an gama gyarata aka miko mata ni.inna tacemun kamarmu daya,hakan yasa ta kuramun ido tana kallonna.idanuwanta cike da hawaye.lafiya kalau ta haihu,amma bayan befi awa biyuba, wani ciwon cikina me tsanani ya kamata.ana kokarin kaita asibiti,tace kada su wahalar da Kansu ita mutuwa zatayi,amma tabar wasiyya,idan Allah yarayani a bani wata takarda data rubuta tana cikin kayanta.kuma asamun sunanta wato maryama,saboda shine sunan da mahaifina yace mata zesaka idan ya haifi diya mace.su inna basu kulataba da ita da maganganunta,suka dauketa zasu kaita asibiti domin sunyi tunanin zafin ciwone yasata fadar haka.amma kafin sukaiga asibitin Allah ya mata rasuwa.
Inna tayi kuka,tamkar ranta ze fita.mutuwar tilon yartata bakaramin dukan ta tayiba.ta gane rabonane yasa mahaifiyata ta dage seta auri mahaifina. Hakan yasa tayafe mata duniya da lahira.ita kanta shedace akan mahaifiya mutumin kirkine,kawai dai matsalarsa rashin sanin asalinsa.inna ta rungume ni,tacigaba da rainona cikin so da tsantsar kauna,tana jina tamkar maryam dinta data rasa.inna bata boyemun sunaba maryam take kirana dashi.
Nataso cikin gata da kulawa a wajen innata.innata bata rageni da komaiba.abincin siyarwa,dasu sobo da kunun aya, shine sana'ar da inna takeyi take rufa mana asiri.duk da girma yafara kamata.komai nakeso innata tanamun,tasani a private school. Tare da islamiyya.Burina arayuwata,inyi karatu me zurfi Insamu aikinyi,in hutar da inna Daga wannan wahalar datakeyi,kullum tana bakin wuta.inna bata da 'yan uwa a garinnan,yan uwanta duk suna can kauye a garinsu.iyayenta kuma Allah ya musu rasuwa. 'Yar uwarta guda dayace,da suke uwa daya,uba daya wato gwaggo.
Amma nidai tunda naso so daya nataba ganin gwaggo a gidan innata.innata batamun irin rikonnan da'ake cewa rikon kakaba,ta shagwabaniba kota sangartani.ta bani tarbiyya ingantacciya.tun ina karama take nunamun rayuwa,takemun nasiha,akan narike mutuncina.nakasance me hakuri a duk halin Dana shiga.bansan kowaba,se innata.itace uwata itace ubana,itace dangina.itace gatana.shakuwa me karfi,tare da tsantsar kaunace a tsakanina da innata.dominni a lokacinma saboda yarintata,bansan ba itace ta haifeniba.innata macece,ta mutane saboda kirkinta da mutunta dan'adam.
Dogon Numfashi,naja ina duban baaba talatu,nace "zan takaita miki labarinane,saboda yanayin lokaci.domin idannace zan fayyace miki komai,semu kwana anan bangama mikiba. "Tom shikenan maryam,kici gaba domin inason jin karshen labarinnannaki.
"Wata rana,nadawo Daga school, da misalin karfe biyu na rana.a lokacin shekarata goma shabiyu. Ina J.S.S 1. Da sallamata na shigo gidan da murnarta ina kwalawa inna kira,kamar kodayaushe,idanna dawo.turus na tsaya ganin banga innata a kitchen ba,agurin saida abincin ta.babu alamun ma tayi girkin yau.dasauri na nufi dakin da muke kwana ina kwala mata kira.Kudundune na hangota akan gado ta lulluba da abun rufarmu.jakar makarantata na cillar na nufi kan gadon.ina cigaba da kiranta.yaye bargon data lullaba nayi,jikinta se rawar Dari yake.wuyanta na taba naji zafi zau. "Innata baki da lafiya meyasameki meke damunki.na tambayeta kwalla na taruwa a idona.Bakinta ta fara motsawa alamun tanason tace wani Abu,amma maganar taki fita.jikinta serawa yake hakoranta na hadewa kamar me jijjiga.bantaba ganinta cikin ciwo irin hakaba.kuka na farayi ina girgizata.tare da tambayarta abunda yake damunta,amma inna ta kasa magana.abunda yafi tsoratani yanda naga idanuwanta sun juye.gashi gida ba kowa dagani se ita.
Wani tunanine yazomun cikin zuciyata.dasauri na tashi nanufi gidan su umman saleemat,dake jikin gidanmu. Umma! Umma! Nashiga kwala mata kira. "Na'am maryam wannan kiran hakafa,lafiya? "Umma innace bata da lafiya,tana kwance jikinta se rawa yakeyi. "subhanallah, shiyasa yau banji hayaniyar masu siyayyar abinciba,muje inga jikinnata.bari in dakko hijabina........✍️
```sannu bata hana zuwa,sedai adade ba'ajeba.kada kudamu da sannu zamuzo inda kukeso.```🥰😘
*By*
*zeey kumurya*
*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*
*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚
~*Free novel*~
*Bismillahirrahmanirrahim*
0️⃣7️⃣
..............Muna shiga dakin nida umma,mukatarar inna har lokacin jikinta se rawa yakeyi.dasauri umma ta karasa kanta dagota tayi taji jikinnata yayi zafi sosai,"maryam debomun ruwa abaho,kitaho da towel. "To umma" har lokacin kuka kawai nakeyi.da sauri na debo ruwan nakawo mata.harta fara cirewa inna rigarta,kara umartata tayi naje nakirawo wani isa me chemist dake bakin layinmu.
Cikin yan mintuna muka iso gidan nida Dr isah,a lokacin har umma ta gama gasawa inna jikinta.dubata yayi ya mata allura tare da sanya mata Karin ruwa.se alokacin nasaki wata ajiyar zuciya.saboda ganin jikin innata ya dena rawa,numfashinta yana fita dai_dai alamun ta samu bacci.magunguna ya rubuta ya bani yace kafin tatashi naje na siyo,kuma atabbatar tasha koda ruwan tea ne idan ta tashi.ranar ninayi duka aikin gida.saboda inna babu abun data iyayi.abinci kuma ummace ta kawo mana.washegari, jikin inna tatashi dashi da sauki.amma bata warke duka ba. Inna tayi_tayi inje school,amma nace mata nibazanjeba.seta kara samun sauki.haka ta hakura ta kyaleni.bayan nagama share_share da wanke_wanke.muna zaune adaki da inna,ta dubeni tace.
"Maryam,ina horanki daki kasance me juriya,akan duk halin dakika tsinci kanki aciki.komai runtsi komai wahala kada ki zubar da mutuncinki,domin mutuncinki shine kadararki.koda na mutu,kada ki koma kauye wajen 'yan uwana,kici gaba da zama anan saboda kisamu ingantaccen ilimi,saboda iliminkine kadai ze taimakeki a rayuwarki.nasiha sosai inna tamun me ratsa zuciya me kama da wasiyya.rungumeta nayi ina kuka nace."inna kidena fadar haka bazaki mutuba,insha Allah harse kinga yayana,kinci gajiyar ilimin da kika dorani akai.lallashina kawai inna tafarayi.itama tana zubar da hawaye.
Bayan kwana 2 inna ta warke rass,tamkar ba itaba.hakan yasa na koma makarantata.naci gaba da karatuna.sekuma wata sabuwa,bayan befi wata biyuba inna ta fara wani irin ciwo,cuta me tsanani.ko hannunta bata iya dagawa.sedai akwantar atayar.gashi babu me jinyarta ni kuma alokacin nayi kankanta.ummace take dawainiya damu da sauran makotan arziki.'yan uwan innata na kauye sunzo amma basu wani jimaba,suka koma.ciwofa yakici yaki cinyewa.babansu saleemat ne yakai inna asibiti.aiko ana zuwa suka bata gado.babu me jinyar inna,umma kuma ga 'yayanta ga aikin gida,baze yiyu tazo asibiti jinyaba.hakan yasa akace dole wani Dan uwan inna seyazo jinyarta. Dakyar wani kanin babansu inna,yasamu gwaggo a yawon gagarinta.da farkoma datazo cewa tayi baza ta iya jinyaba,amma kuma kome tatuna Daga baya kuma seta amince.nidai banda insaka inna agaba ina kuka babu abunda nakeyi.makarantama dakyar umma ta lallabani na koma.inna tayi watanni a asibiti,a canza mata wannan a maidata wannan.gaba daya dan kudin data mallaka duk ya kare a yawon asibiti.amma cuta dai tananan a jikinta.ahaka har na shiga J.S.S 2,nida saleemat.bayan dogon lokaci da inna ta dauka tana jinya.cikin ikon Allah se sauki yafara samuwa har aka sallamota muka dawo gida.murna a gurina kamar me innata ta warke. A lokacin gwaggo ta nuna tanason tafiya amma inna ta hanata.taitai mata fada akan rayuwar datakeyi da girmanta bane dorewa bace.gwaggo tayi aure_aure,amma bata taba haihuwaba.kuma duk auran datayi bata jimawa take fitowa,saboda masifarta da rashin mutuncinta ba kowa ze iya zama da itaba.gashi taita Tarawa mutum kawayenta 'yan duniya a gida.ta yarda ta zauna damu da kyar,duk da badadin zama mukeji da itaba. amma,kullum.seta fice yawonta.inna sedai kawai ta bita da addu'ar shiriya.