← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 128

Sashe 12

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina fitowa ɗaga kitchen suhailat na shigowa falon, seda zuciyata ta buga saboda tsoronta,amma ko kallona batayiba ta nufin gurin mommy ta rungumeta Tana tsallen murnar dawowar yayanta.ƙara rungumeta itama mommy tayi Tana dariya.ɗakina na wuce ina mamakin wannan murna da mommy da suhailat sukeyi akan dawowar wannan bawan Allah,kai zanso naganshi.hijab din jikina na cire,na fara zuge zip din rigata.daƙarfi aka buɗe kofar ɗakina.Dasauri na kalli bakin ƙofar suhailat ce ta shigo,babu sallama. Atare zuciyoyinsu suka buga.saboda nidai nasan ba alkhairi ne ya kawotaba. Ita kuma suhailat saboda tsananin mamakin ganin dirin jikin da Allah yayiwa maryam. "Kutmar haka yarinyarnan take da surar jiki me kyau.suhailat ta faɗi hakan aranta.wani baƙin ciki,da hassadane ya mamaye zuciyarta.yanzu duk yadda takeji da kanta,amma wannan ƴar matsiyatan ta fita kyan ƙira.jibi wani uban shap tamkar ita tayiwa kanta,ga manya_manyan nonuwa tsayayyu.munafuka shiyasa kullum take fama da hijabi,wata tsanar maryam ce ta ƙara lulluɓeta.ni kuwa rigata na fara kokarin mayarwa cikin sauri saboda har takai ƙasa,dan ma da under wear da vest ajikina,amma duk da haka banjo daɗiba data ganni ahaka.wani mugun kallo ta wurgomun Tana hararata. "Ke dabba! Kije ga kayana can ki wankemun.cikin ladami na'amsa mata da "toh".duk da Kalmar dabba,data kirani dashi ya matukar bakantamun rai,nakasa sabawa da muzantanin datakeyi.idanuwanane ya cicciko da kwalla,kokarin mayar da ita nayi,na juya na nufi toilet,bayan ta fice ɗaga ɗakin.

Cikin 10 minutes nayi wankan, shiryayawa nayi,sallar la'asar na tayar.seda na idar na nufi ɗakin suhailat. Itama time din fitowarta kenan ɗaga toilet Tana daure da towel iya Rabin cinyarta ya tsaya,da'alama wanka tayo. kunyar ganinta nayi ahaka,duk kasancewarta mace ƴar uwata,amma aganina hakan bedaceba.juyawa nayi zan fice naji muryarta ta dakamun tsawa."gidan uwar waz aki? Juyowa nayi kaina akasa ina wasa da yatsun hannuna. Cigaba tayi da maganarta cikin faɗa. "Tun yaushe naje na kiraki amma se yanzu zaki zomun,saboda tsabar iskanci kema kin waye kinzo kinfara cin daula,dama shi talaka be iya samun guriba. "Kiyi hakuri aunty suhailat,wanka nayine.nafaɗi hakan cikin sanyin murya. Dariya naga takamayi tamkar wata sabon kamu,da mamaki nake kallonta. Karasowa gabana tayi tanamun wani kallon wulakanci. "Wanka,wankafa kikace,ahakan kikai wanka kina fama da tsami da warin dauda,ke dama dena wankan kikayi dan ba fita kikeba."Dall,ni wuce kimun abunda nasaki wawiya kawai nonsense. Jikina a matukar sanyaye na wuce zuwa toilet dinnata,zuciyata cunkushe da baƙin cikin kalamanta. Aƙasa na hango pants dinta da bra dinta,girgiza kaina nayi cikin takaici, ga gurin saƙale kaya amma bazata saƙaleba,sedai ta zubar a ƙasa tsabar sakarci,daga yanayin suhailat irin matannanne da babu abunda suka iya. Kwashe kayan na farayi ina zubawa a bucket. Saboda nafi ganewa wankin bucket akan na washing machine. Ina ɗaga wai pant dinta naga jini,da sauri na yardashi cikin ƙyanƙyami,araina nace kobatasan ta hadamun dashiba,domin wannan abun ai sirrin mutum ne,ina ƙara daga wani shima naga jinin harma ya fara bushewa. Matsar dasu nayi gefe zuciyata harta fara tashi,na wanke mata bra din na shanya,na fito.har lokacin Tana gaban mudubi,tanata shafe_shafe towel din jikinta ya kunce ya kusa faɗuwa,amma ko'ajikinta. "Aunty suhailat nagama" batare data kalleniba tace. "Barina na duba nagani koya fita,dan idan befitaba sekin sake.tsayawa nayi kawai bance komaiba. Kusan 5 minutes sannan tatashi ta nufi toilet ɗin. dasauri naga ta fito ta ƙaraso gabana"Kan ubannan,kagamun matsiyaciyar yarinya ahakan kikecemun Kingama,shikuma wancan dakika warefa uwarkice zata wankemun.runtse idona nayi,wlh harga Allah nagaji da zagin da takemun. "kiyi haƙuri aunty naga da najasa ajikinsu ne,kuma...wani wawan mari ta tsinkamun. "Lallaima yarinyarnan harni kike faɗawa da najasa,nufinki dai bazaki wankemunba.to meye marabarki da najasar,to bari kiji shi abunda kike cewa nasaja yafimun ke daraja agurina domin shi daga jikina yafito.dan haka kiyi sauri ki shiga ki wankemun,kafin na saɓa miki kamanni. Hawayene kawai yake bin kuncina,duk kuwa da yanda naso mayar dasu amma seda suka zubo.Marin datamun bemun zafiba kamar yadda ta dangantani da najasa.inaji ina gani haka nakoma nafara wanke mata,gani Allah yayini da ƙyanƙyamin wannan abun.nawama ƙyanƙyaminsa nakeyi balle na wani.ina wankewa ina kuka,kukan abubuwa da yawa.ga wani mahaukacin tashi da zuciyata takemun.Allah,Allah nakeyi nagama karnayi mata amai a toilet. nakara jawa kaina wata masifar. Ina gamawa na fito ko kallon inda take banyiba,saboda raina yayi matukar baci,muzantar tayi yawa. Dan kawai ubangiji ya halittoka a talaka,seka zama wulakattacce da kai da banza duk ɗayane a wurin mutane. Da gudu nakarasa ɗakina saboda aman dayaketa tasomun,Allah ma yaso babu kowa a falon.sosai nayi aman,duk da bawani abun kirki acikina,tunda rabona da abinci tun breakfast.kuskure bakina nayi,na fito na kwanta.ina maida numfashin wahala.tare da takaicin wannan wahalalliyar rayuwar danakeyi ta ƙasƙanci,bansan sanda wani baccin wahala ya kwasheniba dama da tarin gajiya ajikina.......

Karfe 5 saura gaba ɗaya ƴan gidan sun hallara domin zuwa taro babban yaya,suhailat anci kwalliya kamar ba gobe,cikin wata red gawn me adon black,wadda ta matuƙar kamata jikinta se rawa yakeyi acikinta,tayane kanta da wani Dan karamin veil black,tayi kyau sosai tamkar ka saceta.farin ciki da murnar datakeyi yau baze misaltuba,kwana 4 dinnan dabayanan jitake tamkar sati 4. Tayi matuƙar kewarsa. Haidar da zannurain kuwa bawani farin ciki sukeyi da dawowarsaba,saboda ze katse musu jin daɗi.dan fitar nan dasukeyi ta ɗare ze katse musu ita.mota biyu sukayi,ɗaya mommy da suhailat ne abaya,se kuma driver a gaba.ɗayar kuma,haydar ne yake driving se zannurain a front seat,baya kuma faruq da sadiq. 4:55 pm,a filin saukar jirgi na malam aminu kano,ta musu.

Dafe zuciyarsa yayi saboda tsananta bugu datake masa,Wanda besan daliliba, ahankali yake sakkowa daga matattakalar jirgin janye fa trolly ɗinsa,idanuwansa ya lumshe saboda shakar iskar garin mahaifarsa da yayi,yana jin farin ciki sosai aransa,na dawowarsa gida *kano ta dabo tumbin gwiwa* tafiya ya farayi cikin gentle dinsa,fuskarsa babu fara'a kamar koda yaushe.su mommy suna tsaye suna baza ido ganin anata fitowa.suhailat ce ta fara hangoshi. Taɓo mommy tayi,"laaa mommy kinganshi ya fito." Kamar yaji metace shima ya kalli inda suke,bazasu iya jira yaƙarasoba,hakan yasasu nufar inda yake.tunda yafito yan matan dake gurin suke binsa da kallo,cike da burgewa kowacce tanaji aranta dama wannan hadaddan guy din yazama mallakinta.murmushi yasaki kadan,saboda hango yan'uwansa kuma guɗan jininsa sun nufo garesa.da gudu suhailat ta karasa garesa ta fada ƙirjinsa,cikin tsananin murna da doki.shima beyi ƙasa a gwiwaba,ya mata masauki a faffadan kirjinsa,tare dasa tausasan hannayesan yazagane bayanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya suhailat ta sauke,lumshe idanuwanta tayi Tana shakar daddadan kamshinsa. Saboda tsabar jaraba,har yanayinta ya fara sauyawa,shafa bayansa tafarayi tama manta a inda suke. Daidai lokacin su mommy suka karaso,raba suhailat yayi daga jikinsa wadda ta kasa magana, da hannu yake amsawa yan uwansa,welcoming din dasuke masa,hugging dinsa sukayi one,by one. Mommy kamar ta maidashi ciki,haka takeji. Duk da baifaɗaba,amma fuskarsa ta bayyana yana cikin farin ciki,sadiq ne ya karbi trolly dinsa suka nufi mota.hannun suhailat ya kama,wadda taketa kallonsa tamkar zata cinyesa,ya matukar yi mata kyau,ya kara wani fresh. duk da fuskarsa tayi fayau alamun ya ɗan ji jiki.Hannunta ya murza,tare da ɗage mata gira,yayi mata alama da hannunsa alamun yadai yaga tayi shiru. Lumshe idanta taƙari tare da lasar lips dinta. Kwantar da kanta tayi ajikinsa,batare da tayi maganaba.saboda itakaɗai tasan metakeji jinta datayi,ajikinsa.ahaka suka ƙarasa motar, front seat yashiga sukuma suna baya kamar yadda sukazo.mommy se tambayoyi take masa,akan ciwonsa,da'abunda yake damunsa. Atakaice yace mata zazzabine....

Direct part ɗinsa ya nufa,duk da mommy taso yaje part ɗinta amma yace mata seya huta zezo.dole haka tasa ƴan aiki suka kwashi kayan data shirya masa zuwa part ɗinsa. Mommy dakanta ta haɗa masa ruwan wanka yashiga.kafin ya fito duk sun fice daga part ɗin,domin sunsan halinsa bayason hayaniya,musammanma daya kasance yau ya dawo.bayan ya ɗauki wasu mintuna ya fito,shiryawa yayi cikin ƙananan kaya,wayarsa ya dauka ya fito falonsa. dinning ya nufa koze samu abunda yake buƙata,amma beganshiba.tsaki yaja,kobi takan liyafar da aka shiryamasa beyiba,ya koma ɗakinsa,text yayiwa mommy akan yana bukatar coffee....

Wata mahaukaciyar yunwace tatasheni ɗaga bacci,toilet na shiga na wanke bakina sannan na fito zuwa kitchen, ina addu'ar Allah yasa babu kowa a falo. Amma kash!,addu'ata bata karɓuba dukansu suna falon amma banda mommy. Suhailat tana ta tsokanar su yahaydar akan yayanta ya dawo, su kuma sunata kukkumbura. Kamar na juya na koma,sekuma naga rashin dacewar hakan tunda sun Riga dasun ganni. Kaina akasa na fara tafiya cikina na kiran chiroma.sannu na musu,amma ko kallo ban ishesuba,yayasadiq ne kawai ya amsamun. Ina shiga kitchen mommy tana fitowa hannunta ɗauke da wani basket me matuƙar kyau,ban kalli mene acikiba,saboda hankalina yanaga aɗɗa'ami. Kafin nayi magana,mommy tarigani. "Yawwa maryam dan kaiwa my son wannan,part dinshi yana gaban namu daga right side dinki,idan kin fita.kiyi sauri dan Allah Dan bayason jira, dama tunanin me kaimasa nakeyi su salame duk sunyi part ɗinsu, su suhailat kuma duk sun gaji......✍️

*BY*
*zeey kumurya*
*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

*Bismillahirrahmanirrahim*

1️⃣1️⃣
Chapter 12 · 0% Book details