← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 128

Sashe 71

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwaggo tana zaune adakinta tanata lissafe kudinta na adashi dana aikatau din Maryam. tanayi tana mitar sabon wata yashiga amma shiru bataji alert na aikatau din Maryam ba, gashi tanata kiran number'n lami bata shiga. sabuwar me aikin datayi me suna laure ce tashigo dakin ko sallama babu. zabura gwaggo tayi tashiga boye kudin akasanta. tana fadin, "ubanme yashigo dake dakina babu sallama, kinga laure kikiyayeni" tabe baki lauren tayi tana jijjiga kafa tana jifan gwaggo da kallon raini tace. "Kekika sani dai, uwar mako da rowa, wannan uban tumulin kudin ina kikasamoshi gwaggo?" cikin harzuka gwaggo tace, "bansaniba uwata, nace bansaniba, kujimun yarinya da fitsara haifata kikayi dazakizo ki titsiyeni da tambaya, to a gidan uwarki nasamo" "badai uwataba gaskiya" laure ta fada tana kauda kai gefe. "bazan kulakiba dannasan uwarki bata baki cikakkiyar tarbiyyaba, ina fatan kingamamun ayyukana. "Cabb, wannan uban ayyukan sekace wata jaka, nayidai iya abinda zan iya" rike haba gwaggo tayi tace, "aa..lallai laure rashin kunyartaki kullum kara gaba take to wlh baki isaba sekinmun duka ayyukan gidannan, zandinga biyanki kudin aikine a banza bakyamun aiki yanda Yakamata. wani kallon banza laure tayiwa gwaggo sannan tace. "Nawane kudinnaki da har kikemun iko akansa, akan 20,000 din dako kayan kwalliya bata isata na siya" "kinsan da haka meyasa kikazo mun aikin, Ai da sekiyi zamanki uwarki ta dinga baki" laure zatayi magana wayarta dake kan cinyarta tayi kara, fita tayi domin ta daga wayar. gwaggo ta bita da harara. kullum sesunyi sa'insa da laure, yarinyar da inda ta haihu setayi jika da ita. amma ta rainata laure bata da tarbiyya kokadan, duk fadan gwaggo da masifarta laure tafi karfinta, duk iskancin dataga dama shitakeyi kuma gwaggo bata isa ta hanataba sedai kallo da ido. kullum se gwaggo tashiwa Maryam albarka tana cewa, "yarinya me biyayya da hakuri bakamarkiba laure" a duk sanda gwaggo ta fadi haka se laure tatabe baki tace da gwaggo. "To kinsan da itan kika daukeni, kije ki dawo da ita mana" a kauye lami tasamowa gwaggo laure, dududu batafi wata da zuwaba amma ta gallabi gwaggo, ga yawon bin samari. gwaggo tanata cigaba da lissafinta na kudadenta, zuciyarta fari kal kamar takadda tatara kudin komawa Saudiyya. Ashe fitar da laure tayi tana waya, wani saurayinta ɗan daba ne yakirata wanda sukayi magana tun jiya zasuzo da abokansa suyiwa gwaggo fashi. tunda ta kyallara ido taga kudin gwaggon takirasa ta fada masa, amma da sharadin bayan sun kwaci kudin itama zebata nata kason. Bayan befi 40 minutes ba, suka karaso unguwar. Laure ce tafita dakanta ta tarosu ta musu jagora har kofar dakin gwaggo.(fashi da ranar Allah🤔)

Gwaggo kawai jitayi an banko mata daki anfado babu ko neman izni, susu biyarne. suka tsaya mata cirko_cirko ai. zabura tayi, ta mike tsaye tare fadin. "Subhanallahi suwaye ku, wadannan samudawa daku zaku shigomun gida har daki. lafiya?" daya daga cikinsune yace, "lafiyar ce takawo haka" wuka da yafito da ita daga aljihunsa tare da karbar wani mulmulallen karfe a hannu wani yana muzurai yacewa gwaggo. "Ki bamu kudin dake cikin gidannan ta lallami kokuma na fardeki na kwata" "wanne kudi kuma, uwarku ta bani ajiyan...." "Ke!" wani daga cikinsu yadaka mata da tsawa yana zaro wuka shima daga aljihunsa yana nuna gwaggo da ita. duk da gwaggo ta tsorata amma bakinta be mutu ba, kuma tace kome zesu mata bazata basu dukinba. ganin tana bata musu lokaci, wanda ya mata magana da farko ya kwada mata ƙarfen hannunsa akafa sau biyu, gwaggo ta hau ihu tana neman taimako. Toshe mata baki sukayi sannan suka datsa mata wuka agefen kafadarta, ga azabar yanka gata rufe mata baki da hanci da sukaimata, nanfa numfashinta yafara sarkewa daga karshema se numfashin ya dauke dif. Kasan gadonta kawai suka daga sukaga kuɗin acikin leda babba sekuma wani a cikin tarkacen kwanukanta, seda suka kwace kuɗin gwaggo kaf, ko sisi basu barmataba sannan suka tsallaketa suka fice. suna fita laure tabi bayansu da kunshin kayanta dama tagama hada komai nata.

Saleemat bayan tagama abunda take tayi wanka ta nufi gidan gwaggo. tundaga soro take zuba sallama amma taji shiru, tsayawa tayi a tsakar gida dan basa shiga dakin gwaggo. sallamar tacigaba dayi amma taji shiru. kofar banɗaki ta kalla taganta abude babu kowa a ciki. "Ko gwaggo batananne?" Saleemat ta tambayi kanta. amma kuma ai ko fita zatayi tana rufe dakinta koda tabar gidan abude. dakinnata ta shiga da sallama dauke abakinta, atunaninta ko gwaggo bacci take. yanayin dataga gwaggo bakaramin firgitata yayiba, kwance taganta baki a daure cikin jini, ga dakinta duk a birkice. cikin kidima ta fice da sauri taje ta sanar da umma, tare suka dawo gidan da umma. bakaramin gigita ummantayiba itama, fita tayi tasamu wani makocinsu ta masa bayani, saboda suna ganin girman umma mazan unguwar shiyasa ya yarda ya shiga gidan gwaggo amma badan itaba. hankalinsu umma a tashe ta kira baban saleema ta fada masa halin da'ake ciki. Napep aka samu akasaka gwaggo aka nufi asibin AMINU KANO da ita.............

Likitar mommy bata dawo kawo mata result dinba seda yamma bayan ta tashi daga aiki, kafin tazo suhailat tayi amai yakai sau hudu, kuma taki cin komai, amma zazzaɓin jikinnata yasauka, se Rashin kwarin jiki kawai kedamunta, har wanka ta iya yi da kanta. likitan ta girgiza dataga abun dake damun suhailat din. Jiki a sanyaye ta nufo gidan mommy, gaisawa sukayi da mommy dake zaune a falo tana waya, sannan tatambayeta ina suhailat ta nuna mata dakin datake da hannu. suhailat na kwance, Dr ta shigo dakin da sallama. Amsa mata tayi tare da yunkurin tashi zaune. "Sannu patient ya jikinnaki? cewar Dr, bayan ta zauna akan stool din mudubi. tace "Da sauki Dr," "Masha Allah, yanzu i nane yake miki ciwo?" Dr, tatambayeta tana tsareta da ido. Tana yamutsa fuska tace, "kaina sekuma jikina da babu kwari inajin kasala sosai, sekuma jiri da tashin zuciya" Dr, tace. "Sannu, yaushe rabon dakiga period ɗinki?" dan jimm suhailat tayi tace. "Gaskiya namanta" "ohk, bari nasa Miki drip dinnan" Dr, ta fadi haka tana janyo jakar kayan aikin datazo dasu. Allurai taiwa suhailat na tsaida aman, sannan tasa mata karin ruwa. magunguna ta rubuta tabawa suhailat. addu'ar Neman sauki tamata sannan ta fice daga dakin cewa zuciyarta cike da tausayinta. Har lokacin mommy bata gama wayar datakeba. zama tayi taɗan jira mommy'n. katse wayar mommy tayi badan ta gamaba sedan ganin Dr ta fito. tace "Sannu Dr, harkun gama?" Dr, tace "Ehh, Hajiya namata allurar tsaida aman nakuma samata ruwa" "ok, babu magungunan daza'a siya?" "Akwai na rubuta nabata" "yawwa Dr, Nagode, amma babu kuɗi cash a hannuna, amma insha Allah anjima zanmiki transfer" "babu komai Hajiya, nizan wuce, ga result ɗin abunda ke damunnata" Dr, ta fadi haka tana mikewa. karba mommy tayi ta'ajiye akan kujera batare data dubaba, kokuma tatambayi Dr, abunda ke damun suhailat dinba, hankalinta nakan wayar dasukeyi ita da Binta akan zuwansu gurin boka gobe. sallama sukayi da Dr, tafice. daukar wayarta mommy tayi takira Binta suka cigaba da maganarsu........

Su dadddy sun sauka a garin Kano lafiya. daddy zuciyarsa fess yakejinta yau yasauke dakon dake kansa na shekaru masu dama. Aunty a part din su baaba talatu ta sauka, anan sukayi sallah itada Aliya,baaba talatu ta kawo musu abinci sukaci sannan Aunty tatara ma'aikatan gidan mata tace musu za'a sallamesu gobe, badon sunyi lefin komaiba. amma za'acigaba da biyansu albashinsu, godiya sukayiwa Aunty duk da basusan dalilin hakan ba. abunda yasa Aunty tayi haka, a ganinta bedace suci gaba da zama agidanba tunda babu mata a gidan, bazeyiyu su zauna daga su se ya'yan gida da megidaba. seda suka kebe a daki sannan Aunty tayiwa baaba talatu bayanin abunda yake faruwa atakaice kamar yadda ta bukata. sosai baaba talatu tacika da rudu, da al'ajabin wannan abu. Amma batayi mamakiba dantasan halin mommy ciki dabai. amma bata taɓa zaton ba ita tahaifi Mustapha ba.

Aunty tana fitowa daga part din su baaba talatu ta nufi part din su Sadik, dan yau ta kudurcewa ranta seta ganshi taga halin dayake ciki, ai hannunka baya taba rubewa ka yanke kayar. su faruq duk suna part din daddy. knocking din dakinnasa ta shigayi, data murda handle din tajita a rufe. bubbuga dakin taitayi amma bebudeba, dole ta hakura ta kyaleshi. part din daddy ta zarce, nan suka hadu sukaita hira dasu faruq cikin nishadi, daddy da Aunty nabasu labarin abunda yafaru a jos. sunyi farin ciki sosai dajin yayansu yahadu da mahaifiyarsa. Amma fa zasuyi missing yayansu sosai............✍️

*Kuyi manage da wannan, muhadu gobe idan meduka yakaimu*

*By*
*zeey kumurya*
*ABINDA KASHUKA....*

*5️⃣1️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

...........Mommy bata tashi duba result din da Dr, ta kawo mataba se bayan magriba. wani irin zabura tayi ta mike tsaye daga zaunen datake lokacin da taga abunda ke rubuce a jikin takardar. gani tayi kamar idontane benuna mata daidaiba, dakinta ta nufa da sauri ta dauki glass dinta ta saka sannan ta kara duba takardar abunda tagani da farko dai shita kara gani, da sauri ta fito falo hartana tuntube ta dauki wayarta tayi Dialing number doctor, ringing uku Dr, ta daga da sallamarta. batare da mommy ta amsa mataba tace: "Dr, Rahila yanaga wani result daban gane masaba, kodai bana suhailat din bane?" Cikin girmamawa Dr, tace. "Hajiya shine mana, natane" mommy na haki tace, "to ai bangane meke damunnatabane kimun bayani yanda zangane" numfashi Dr, taja tace: "Hajiya am sorry to say suhailat na dauke da ciki na tsawon sati shid......" "What" mommy ta katseta cikin karaji tare da yarda takardar hannunta. "Dr, kinsan mekike fadamun kuwa, suhailat din tawace take da ciki?" "Yes mah" abinda Rahila kawai tace mata kenan dan ta san duk bayanin dazatayiwa mommy a yanzu baza ta taɓa fuskantartaba.
Chapter 71 · 0% Book details