Sashe 70
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallar da aka shiga a masallaci ta tarwatsa zaman, dady da Mustapha suka nufi masallaci. Aunty tana da alwalarta,dadduma kawai zuhura ta kawo mata tatada sallah a falon. Maryam da aliya ne suka shiga daki domin yin Sallah. zaune suke akan darduma bayan sun idar da Sallah. "Mairota how market?" Aliya tafadi haka tana kwashewa da Maryam da dariya, ganin yadda take komai jikinta asanyaye. banza Maryam tamata bata kulataba, dan ita haryanzu zuciyarta takasa yarda wai yanzu aure yashiga yatsakaninta da *heart beat* dinta. matsowa jikinta Aliya tayi ta fara mata magana seriously. "Wlh Maryam, kinyi dace da miji bakadanba domin yaya Mustapha irin mijin dakowacce mace zataso ta mallakeshine, amma ke nasan mene damuwarki akan wanan aurennaku. abu na farko dake damunki saboda kina da wanda kikeso wato yaya Sadiq, na biyu kuma kina tunanin yanda zakiyi rayuwa da wanda baya sonki" da mamaki Maryam ta kalli aliya, tamkar ta shiga zuciyarta dan abunda aliyan tace shine abinda take ta tunani tun dazu. daga mata gira aliya tayi tace, "koba haka bane" numfashi na sauke nace. "Hakane aliya, ni namafi tunanin yaya Sadik, dan yana matukar sona nasan bakaramin tashin hankali ze shigaba idan yaji wannan abun" "gaskiya abun babu daɗi rana daya arabaka da masoyinka dake da yaya Sadik dole zaku shiga damuwa, daman, amma kuma hakuri zakuyi dan bamusan alkhairin dake cikin wannan aurennakuba. shikuma yaya Mustapha kisha kuruminki, dan idan ana kuka akan soyayya seya miki shaɓe_shaɓe har da gunji, nina fada miki kuma." "Hmmm, aliya kenan bana tunanin haka agurinsa tunda shima kinsan yana da wadda yakeso,kawai babu yanda zeyine" tabe baki aliya tayi tace. "Wai ant suhalat kike nufi, tabb aiba wani sonta yakeba,kawai biyayya yayiwa mommy yake kulata, banda haka mezeyi da wata suhalat mace ba kamun kai" shiru namata domin nikadai nasan halin da zuciyata take ciki. baki aliya taita bani akan aurennan da dady yamun tana tausata. batasan nafi kowa murna da aurannanba kawai dai fargabata daya yanda zamuyi tarayya matsayin miji da mata dashi,nasan akwai ja. daga karshe kuma seta koma tsokatana wai zanyi fama da miskilancinsa. Ammi ce dakanta tazo takiramu domin Muci abinci. Da kyar daddy yayarda su tsaya suci abincin dan da cewa yayi tafiya zasuyi, mama ta masa magiyar yabari su kwana da safe sesu wuce, amma yace mata hakan baze yiyuba. Domin bakaramin ayyuka ne agabansaba, dan missed called din dake wayarsama kadai ya ishe sa, ga harkar kasuwancinsa yanaso gobe yakoma acigaba da daga inda aka tsaya. kadan sukaci abincin kowa yace yakoshi, Maryam kam batafi lauma biyuba tace takoshi. Mustapha kam beciba, Aunty ce tacewa ammi haka yake, bedamu dacin abinciba sedai coffee ko tea. ammi bata bata lokaciba ta shiga kitchen ta dafa masa hadadden shayi dayaji kayan hadi, ta kawo masa. tamkar zata bashi a baki saboda kauna. kafin isha'i su dady sungama shirinsu na tafiya. ammi tacikasu da kayan su bagaruwa da dabino datazo dasu daga Saudiyya, suna kewar juna sukayi sallama,bayan sunyi musayar numbobin juna. Maryam se kwakube Aunty take, batasan anan za'a bartaba tunda mijinta bandashi za'a tafi ze zauna gurin mahaifiyarsane. Afarfajiyar gidan Aunty ta tsaidata da fadin. "To, Maryam saduwar alkhairi, insha Allahu gobe kafin na koma kd, zanje gidan gwaggonki na mata bayani, inda halima har kauyennaku semuje da yaya suma mumusu bayani" Maryam bata amsawa Aunty ba, se kuka data fashe dashi tare da riketa. tausayintane yacika Aunty, aliyama se hawaye na tausayin maironta. rungumeta Aunty tayi tana bubbuga bayanta alamun lallashi. cikin kuka tace. "Aunty dan Allah nidai zan biki mutafi" duk dauriyar Aunty seda kwalla ta cika mata ido, domin itama bakaramin missing Maryam zatayiba. maida kwallar data cika mata idon tayi tadago da Maryam daga jikinta. cikin lallami tace mata. "Kiyi hakuri diyata, ai zandawo nanbada jimawaba, kuma aikinyi sabuwar mommy, gaki ga amminki zata miki fiyema da abunda zanmiki, kikwantar da hankalinki kidena damuwa, idan kuma mukayi waya da ammi tacemun kina damuwa tobazanzo intafi dakeba." Aunty ta karashe zancen tana sharemun hawayen fuskata. gyada mata kai nayi alamun gamsuwa. Addu'ar fatan nasara ta mun. rungume juna mukayi da aliya cikin shaukin juna muna kuka, da kyar Aunty ta rarrashemu muka yi shiru. harta juya zata tafi nace mata. "Aunty yaya Sadik fa, inajin tausayinsa." maganar Maryam karaf a kunnen Mustapha daya baro gurin daddy, yazo sukara yin sallama da Aunty. "Karki damu Maryam, nasan mezance masa dabaze damuba" Aunty tafadamun haka tana kallon Mustapha. cikin karayar zuci najuya nakoma cikin gidan dazan fara sabuwar rayuwa a cikinsa,jikina a matukar sanyaye. a zaune nataddasu dukansu a falon sunata maida zance. kaina na kasa na musu sallama, gefen Aunty zuhura datake bawa yaronta nono na zauna. jana ammi da mama suka shigayi da hira duk dan insaki jiki dasu musammanma ammi. seda kusan mintuna 20, suka shude sannan ya shigo falon, bakinsa dauke da sallama. amsa masa mukayi gaba-daya, ammi fuskarta dauke da fara'a ta nunawa mustapha gefenta yaje ya zauna. kallo daya zakayiwa ammi katabbarta da tana cikin tsananin farin ciki. fuskarta cike take da annuri, tarasa ina zata tsoma kanta saboda jindadi da murna. harta kira mahaifiyarta da kaninta tasanar musu. kaninta yace ze kirata anjima ta video call suga mustapha. muna zaune a falon Saddam da mijin A'isha suka shigo. suna zama mama tafara rattaba musu bayanin abunda yafaru...........
*KANO*
Yau suhailat da wani matsananci ciwon kai da zazzaɓi tatashi. jikinta gaba-daya rawar dari kawai yakeyi. misalin ƙarfe 11 na safe mommy tashigo dakin datake tana fadin. "kinanan kina wannan shegen baccinnaki na jaraba ko? kinsandai nan bagida bane babu masu aiki, kitashi kifito kimun shara." Wasu hawayene masu zafi suka zubowa suhailat, ita kadai tasan azabar datakeji ajikinta amma mommy tashigo tana mata masifa, duk mommy tabi ta canza mata yanzu kullum se fada da masifa, kamar ita tadora mata damuwar dake damunta. kan gadon datake mommy ta karasa da nufin tatasheta. tana dora hannu ajikinta taji zafi zau. "suhailat bakida da lafiya ne?" suhailat bata bata amsaba, hawa gadon mommy tayi ta janyota jikinta. da sauri suhailat ta janye jikinta daga na mommy, saboda kamshin turarenta data shaka bemata dadiba. kafin tayi wani yunkuri tuni wani amai yataho mata, kokarin sakkowa tayi daga kan gadon kafafuwanta kawai ta zuru aman ya kufce mata, ta fara kelayashi a nan bakin gadon, tamkar zata amayar da kayan cikinta saboda azabar aman, se haki takeyi tana kelayashi. kallonta mommy tayi cikin wani irin yanayi na alamar tambaya. gaba-daya suhailat din ta canza mata, jikinta har wani yalo yakeyi tsabar fari, ga cika data kara sekace wata matar aure, seyanzu ta lura da hakan. jan jiki tayi takoma kan gadon ta kwanta tana sauke numfashi,bayan aman ya tsaya mata. "Sannu" mommy tace mata adakile. dole ta mike tahau gyara gurin tanayi tana tsaki, bayan tagama gyara dakin ta gogeshi tass. ta dakko room freshener ta hau fesawa. suhailat na shaka wani aman yakara taso mata, da gudu tatashi tanufi toilet ta fara kakari. tsayawa mommy tayi cak tana kallonta zuciyarta cike da fargaba gami da wasiwasin meke damun suhailat din take ta kwara amai haka. wani tunani tayi dasauri tafice daga dakin taje dakin datake taɗauki wayarta takira likitanta ta mata bayani atakaice. Address din gidannata ta tura mata. da rarrafe suhailat ta fito daga toilet din, jikinta gabadaya ya mutu babu kwari kokadan a bakin toilet din ta kwanta, domin ko kan gadon bazata iya karasawaba. mommy data shigo taganka a haka tana numfarfashi se tausayinta ya tsirga mata. dagata tayi ta kaita kan gado ta kwantar, suhailat kam se toshe hanci take dan batason turaren mommy kokadan daga mata hankali yakeyi bakadanba. yanda jikinta yayi zafi zau se mommy ta rage mata kayan jikinta, towel ta dakko da ruwa ta daddanna mata ajikinta, se zafin jikinnata yaragu,amma se rawar sanyi take. lulluba mata blanket mommy tayi bajimawa bacci yadauketa. fita mommy tayi tafara rage ayyukan gidan. wajen 12/30 doctor din tazo. Bayan sungaisa mommy tamata jagora zuwa dakin, har lokacin suhailat baccinta takesha. duddubata ta shigayi, tanayi tana tambayar mommy yanayin yanda taga jikinnata. jininta ta diba tace, zataje asibiti ta auna seta dawowa da mommy da result din. godiya mommy ta mata, sukayi sallama ta tafi...........✍️
*By*
*zeey kumurya*
*ABINDA KASHUKA....*
*5️⃣0️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
.........A ɓangaren Sadik kuwa yau da wani matsanancin ciwon kai yatashi wanda ko idansa yakasa budewa saboda azabar ciwon kan, hakanne yasa besamu yafito ganin Maryam ba, kamar yadda yaci alwashi jiya. daga ciwon kai jikinshi gaba-daya yaɗauki wani irin zafi, da kyarma. tun yana iya sanin duniyar dayake ciki harya fice daga hayyacinsa........
********************
*DARMANAWA*
Saleemat ce zaune adakinta da waya a hannunta yau wurin sati guda kenan tana trying number'n Maryam amma a kashe. cikin takaici tafito daga dakinnata ta nufi dakin umma. ''umma wlh haryanzu wayartata a kashe, kuma su ba matsalar NEPA ba, bare nace caji ne babu a wayartata." saleemat ta fadi haka bayan ta daga labulen dakin. umma tana dubanta tace, "toko matsalar network ne, saleema?" "gaskiya umma bana jin network ne, wayarce dai a kashe" "to Allah yasa dai lafiya" "lafiya kalauma insha Allah, nafi tunanin wayarce ta samu matsala" "to Allah yasa muji Alkhairi" "Ameen, umma bari nakarasa ninkin danakeyi naje gidan gwaggo nasanar mata dakaina" murmushi umma tayi tace, "saleemat ba kunya, kawo kayan lefennaki zaki fada mata da kanki" dariya saleemat tayi tace, "Aiso nake na kunnota kwana biyu shiruma banjitaba" umma tace, "nimun hadu da ita jiya, dana fita, naga tanata sauri ne, shiyasa banfada mata kawo kayan ba."....