Sashe 76
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Washegari, bayan nayi sallar asuba ban koma bacciba, Alqur'ani me girma na dakko na karanta izifi uku nayi narufe na ajiye. Addu'a nayi sosai akan rayuwata, nayi mana addu'a sosai akan aurennan namu da hearbeat senaji duk wani tsoro da fargaba ya kaumun daga zuciya. Ƙarfe bakwai da yan mintuna nafito daga dakina domin na gyara gidan. babu wani datti yananan fess dinsa. kujerun na karkade nashare dan dattin dabaza'arasaba a falon, nagoge dining da tv. Kitchen na shiga shima babu wani abun datti a cikinsa, leda na hango akan karamar freezer dake kitchen din, da dan mamaki nakarasa nahau dubawa, dan jiya dana shigo babu da ita. kaza nagani a ciki har uku, se zuba kamshi takeyi. shiru nayi cikin karayar zuci, araina nace. "Kazar amarci dakowanne ango yake siyowa matarsa ya lallabata yabata taci, amma ni nawa angon saboda baya sona seyazo yadireta a kitchen" kwallace ta cikamun idona, maida ita nayi yanda naganta nafito daga kitchen din zuciyata namun kuna. "Yaushe bawan Allah'n nan zesoni? kamar yadda aliya tace, anya kuwa zanga wannan ranar ba yaudarar kaina nakeba kuwa? abun da kamar wuya" natambayi kaina hawaye na zubomun daga idona. Knocking din kofar falon akayi yasani saurin goge hawayennawa, kofar na nufa na bude batare da tambayar wayeba. Umaimah ce tsaye hannunta dauke da basket da kayan breakfast a ciki, ammi ce dazata kawo da kanta umaimah tace tabata takai musu, dan a zatonta mustapha ne ze bude kofar amma setaga Maryam. bata rai tayi sosai ta wani hade fuska, ko sannun da Maryam ta mata bata amsaba. matsa mata nayi ta wuce ciki nima nakoma na zauna akan kujera bankara kallon koda inda takeba harta fice danna lura yar rainin hankalice. tana fita na tashi na kulle kofar, inajin yunwa gaskiya dan tun jiya da rana rabona da abinci. Flates na dakko da cups nadibi abinda zanci nanufi dakina, Allah sarki ammi nasan wannan duk aikintane. koda nagamaci banfitoba wanka nayi na kwanta ina tunanin yanda zamanmu zecigaba dashi. seda goma ta wuce nafito Falour'n dauke da kwanukan danayi amfani dasu, nasan zuwa yanzu kam yafita. kan dinning na kalla naga shima kwanukan dayayi amfani dasu a gurin, da alamama bejima da fitaba danga kamshin turarensanan a falon. Tattara kwanukan nayi duka nakai kitchen na wanke na kara kimtsa wasu abubuwan. sannan naje na gaida ammi cike da jin kunyarta, a tunaninta mustapha yananan befitaba, muna gama gaisawa tace inkoma gurin mijina. Ƙarfe 12 na rana aka kawo mana wuta, dama nagaji da zama ba abunyi sena kunna kallo..... Yaran makota sun shigomun yau sosai harda yanmata kamar ni, dan su mama duk sun sanar amarya tatare. naji dadi kuwa sosai dama kewa ta isheni har bayan la'asar sannan suka tafi. kara gyara gidan nayi naturareshi da turaren wuta me dadi, Aunty zuhurace ta aikomun dashi da yawa a cikin bokiti. se kusan magriba mustapha yadawo gidan, ina zaune a falo ya shigo. Lumshe idonsa yayi saboda wani ni'imtaccen kamshi dayaji falon yanayi. shikam yanason kamshi a rayuwarsa yana kuma san tsafta. A hankali ya kalli inda yaji muryatarta data amsa masa sallamar dayayi, danbe zaci tana falonba. becemun komaiba yawuce dakinshi, ni kuma na bishi da kallo zuciyata cike da shaukinsa. Lumshe idona nayi nafada duniyar tunani, har aka kira sallar magriba inanan zaune inda yabarni. da kyar na yunkura na shiga daki nayi alwala danyin sallah. Da daddare yaya sadam yazo har part dinmu yace inshirya da safe zamuje amun passport za'akai makarantar dazanyi NECO. Wayyo daɗi kamar ze kasheni dan Murna dan da har na fiddarai da karatun......
*2 weeks later*
Munje school din dazanyi exam nida yaya Saddam angamamun komai na exam din. goma ga azumi zamu fara exam din insha Allah. Zamanmu da *heartbeat* jiya ie yau babu abunda yasauya, tsakanina dashi gaisuwa ce, ko abinci bana zuba masa da kansa yake zubawa yaci. Amma yanzu kullum kafin yafita seya duba yanda natashi kafin yayi baccima seyazo ya Dubani. bantaba shiga dakinsaba, koda da sunan gyara danbanga wannan fuskarba. Kullum yana fita ina gama ayyukana zantafi part din ammi muyita hira da Aunty zuhura. Umaimah kuwa bama magana kwata_,kwata, da ina gaisheta naga bata amsawa nadena. Inta ganni setayi ta hararata tana bata rai, niko da ita da banza duk ɗaya na daukesu gurina. duk abunda ke faruwa tsakanin Maryam da umaimah zuhura tana hankalce dasu kuma tasan Umaimah son mustapha takeyi. shima Mustapha'n zuwa yanzu yagane inda umaimah ta dosa akansa. yana zuwa part din ammi zata fara shishshige masa ta kawo masa ruwa da lemo, tana iyayi tana fadin. "Yaya NOOR inkawo maka abinci, kokuma yaya NOOR mezakaci indafa maka" haka zataita masa iyayi da neman suna, shiko yamata banza abunka da miskilin mutum, gashi yarinyar bata burgeshi kokadan. Muna waya da Aunty da saleemat akai akai a wayar ammi, dan har yau besaimun wayarba, yace sena gama exam da ammi ta kuma masa maganar.