Sashe 109
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..........Ana idar da Sallah ya nufo gida, wani irin farin ciki yakeji a cikin zuciyarsa zaiga meronsa da amminsa, ƙara gaisawa sukayi da maigadi ya ƙara masa sannu da zuwa Sannan ya karbi kayansa ya wuce cikin gidan, garin yayi lum_lum alamun haɗari, part ɗinsu ya nufa direct zuciyarsa cike da muradi gami da ɗokin ganin Maryam, a hankali ya tura ƙofar falon ya buɗe, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonsa yana shaƙar daddaɗan kamshin turaren huta dana room freshener dake tashi a falon, ga sanyin AC daya ratsashi, a hankali ya buɗe idonsa yana bin falon da kallo, kamar yau ya fara shigowa cikinshi yayi 3 minutes yana kallon falon sannan ya fara taku ya nufi ɗakinshi, da sallama ya shiga duk yasan babu kowa, ledodin hannunsa ya ajiye a gaban mudubi yana bin dakinnashi da kallo cike da burgewa, ganinshi fess dashi se tashin kamshi yake, murmushi yayi cikin jin daɗi ya juya ya fice daga ɗakin ya nufi dakin Maryam, Maryam na ajiye darduma a cikin cover ya shigo ɗakin da sallama cikin daddaɗar muryarsa, Jin muryarsa a dodon kunnena yayi dai_dai da wata irin bugawa da zuciyata tayi, lumshe idona nayi inajin wani sanyi na ratsa zuciyata tun kafin na kaiga kallonshi, a hankali na juyo bisa umarnin zuciyata data azabtu da kewarsa, mustapha kuwa tsayawa yayi a jikin kofa yana kallonta ya harde hannayensa a kirjinsa, yana sakin tattausan murmushi akan fuskarsa, wani nauyi da kirjinsa ya masa yaji yana raguwa a hankali, sanyi da farin ciki na maye gurbinshi a zuciyarsa, kamshin jikinta dana ɗakin ya haɗu ya bada wani kamshi me daɗin gaske wanda ya saukar masa da nutsuwa, ɗago da idanta tayi a hankali ta kalli fuskarsa shima kallonnata yake hakan yasa idanunsu ya harɗe guri guda, ƙara buɗe lumshashshun fararen idanunsa yayi ganin wani irin kyau data masa yana bin surar jikinta da kallo, wani yawu ya haɗiye yana jin wani abu na bin dukkan ilahirin jikinsa a kanta, be san yayi kewarta dayawa ba seyanzu daya ganta a gabansa, ita kuwa Maryam suna haɗa ido tayi ƙasa da kanta tana ɗan turo bakinta gaba, kasa jurewa yayi ya ƙarasa inda take, daf da ita ya tsaya yanajin bugun zuciyarsa na sauyawa, wani dogon numfashi yaja saboda kamshin jikinta daya shaƙa, nima lumshe idona nayi saboda daddaɗan kamshinsa daya cika hancina ina sauke ajiyar zuciya, a hankali yasa tattausan tafin hannunsa na dama ya shafi kuncina, cikin wata irin siririyar murya yace, "Ummuuuuu....!" yaja sunan wanda hakan yasa naji tsigar jikina tayi wani irin tashi yarrrr, ƙara ƙasa nayi da kaina bandagoba kuma ban motsaba, balle na amsa masa, hannunsa yasa ya ɗago haɓar ta, idanuwansa yasanya cikin nawa yana jifana da wani fitinanne kallo ƙoƙarin kauna nawa idon nayi daga nasa amma yaƙi bani damar yin hakan, runtse idona nayi da sauri saboda bazan iya jurar kallon kwayar idonsa ba, kwallar da bansan kota menene ba ta cikamun ido, ɗan yatsansa yasa yana shafa saman idona cikin wani irin salo, murya ƙasa_ƙasa yace "kinyi kyau sosai" ya ƙarashe zancen tare da busa mun iska daga cikin bakinsa a fuskata, wani gwauron numfashi na sauke hawayen daya cikamun ido na kwaranyowa ta gefen idona, runtse idonsa yayi yanajin zafi na ratsa zuciyarsa sanadiyyar ganin hawayenta, a ɗan rude yace "me nene?" Ko bakiyi farin ciki da dawowataba?" girgiza kai nayi alamun a'a, ina ƙoƙarin haɗiye kukan dake neman kufcemun, rungumeta yayi tsam ajikinsa, a tare suka saki ajiyar zuciya me ƙarfi, shafa bayanta yake a hankali, lumshe idonsa yayi yana shaƙar kamshin jikinta daya saukar masa da kasala gami da tada masa feeling a kanta, nima luf nayi a jikinshi ina ƙara kwantar kaina a kirjinsa cikin tsananin farin ciki, ajiyar zuciya kawai nake saukewa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa me saukar mun da nutsuwa, sunyi kusan 5 minutes a haka kafin ya rabata da jikinsa a hankali, bece komaiba yaja hannunta suka ƙarasa bakin gado, zama yayi ya zaunar da ita akan cinyarsa, bakinsa yakai saitin kunnenta cikin wata irin murya me narkar da zuciya yace "I MISSED YOU" lumshe idona nayi ina saukar numfashi amma bance komaiba, be damu da yanda take masa shiru da, dan yau wani abu yakeji a zuciyarsa game da ita dabe taɓa jin irinsaba, juyo da fuskarta yayi yace "yan mata ba magana ne, ko in koma inda na fito?" girgiza kai nayi alamun a'a ina turo baki gaba, shafa lips dinta daketa zuba kyalli yayi yana murmushi yace "toh meyafaru?" a hankali nace "kai ne" kwantar da kanta yayi a kirjinshi yana shafa gefen fuskarta yace "me nayi?" Idona a lumshe nace "katafi ka barni, kuma jiya naita jiranka baka dawo ba" karan hancinta yaja yace "am sorry" dago kaina daga kirjinshi nace "sannu da zuwa, dafatan ka dawo lafiya?" hararar wasa yamun yace "seyanzu?" Murmushi nayi cikin jin daɗi nace "A'a, yasu Daddy?" Yace "sunanan kalau" nace "Masha Allah, ya jikin yaya Sadiq?" wani kallo naga yamun bece komaiba, ya saukeni daga jikinsa, mikewa yayi ya kama hannuna yana faɗin, "muje ki rakani gurin ammi" sakin hannunnasa nayi na tafi na dakko mayafina, ƙura mata ido yayi sosai ganin yanda take tafiya mazaunanta na juyawa, ina jin yanda idanunsa ke yawo a jikina, harna dakko mayafin na yafa na juyo be bar kallona, seda na matso kusa da shi nace "muje" Ajiyar zuciya ya sauke ya ƙara kama hannunta suka fice daga ɗakin, tafiya muke amma ni yake kallo kawai baya ganin gabansa, muna haɗa ido ya sakarmun murmushi yace "kinyi kyau sosai" murmushi nayi cikin daɗi nace "Nagode" zukatansu cike da tsananin farinciki kasancewa tare suka nufi part ɗin ammi, sosai mustapha yake kallon Maryam kamar yau ya fara ganinta, a kwana biyun dayayi basa tare ta sauya masa ba kaɗan ba, ta ƙara kyau da haske da cika, sunzo steps din dazasu shiga part ɗin ammi yayi tuntube, saboda kallon Maryam daya ke, kallonsa nayi ina dariya, ganin yanda yayi da fuska kamar wani yaro nace "sannu" keɓe fuska yayi ya matse hannuna dake cikinnasa, yana kallon fuskarta, sosai dariyar datakeyi ta ƙara mata kyau, munzo shiga part ɗin ammi nayi ƙoƙarin kwace hannuna amma yaƙi sakarmun sema ƙara matseshi da yayi, da sallama muka shiga falon, umaimah ce kaɗai a zaune a falon, ɗago kanta tayi da sauri ta kallesu, bugun zuciyarta na sauyawa, wani bala'in kyau da dacewa Maryam da mustapha suka mata, kasa dauke idonta tayi daga kansu, sukuwa daga sallama basu ko kalli inda takeba suka shige ɗakin ammi, umaimah ta sauke wani dogon numfashi bayan sun shige ɗakin, tanaji aranta dama ita ce suka jero da mustapha haka ya riƙe mata hannu, gaskiya dole ta dage dan ganin ta mallaki mustapha a matsayin miji itama, ammi tana murmushin farin cikin dawowar ɗannata ta amsa musu sallamar da sukayi, sakin hannun Maryam mustapha yayi ya ƙarasa gareta yayi hugging dinta, ammi ta shafa sumar kansa still fuskarta ɗauke da murmushi tace, "welcome Noor" sakinta yayi ya zauna a gefenta sannan yace "thanks You ammi" ammi tace, "dafatan ka dawo lafiya, ya hanya?" Yace "lafiya kalau" ammi tace "yame jikin fa, dasu daddy'nnaka?" Yace "da sauƙi, su dad sunanan lafiya" ammi tace "Masha Allah" kwantar da kansa yayi akan kafadarta a hankali yace "I missed you ammi nah" ammi tayi murmushi kawai ta shafi kansa batace komai ba, amma zuciyarta cike fal take da farin cikin dawowar ɗannata, Maryam tana zaune a kan carpet din gaban gado, tana kallonsu cike da ban sha'awa da burgewa, sun ɗan taɓa hira da ammi sannan ammi tace ya tashi yaje yaci abinci, duba time yayi ya ga lokacin sallar isha'i ya kusa, mikewa yayi yace "bari yaje masallaci ya dawo" ammi tace "toh sekadawo" hannunta ya sumbata sannan ya fice bayan ya kashewa Maryam ido. Ammi ta bisa da kallo cike da tsananin kauna, kwana 2 da yayi a Kano ba ƙaramin kewarshi tayi ba, batasan kuma yazatajiba randa akace ya koma Kano da zama gaba-daya, maida kallonta tayi ga Maryam tana murmushi, ta mata kyau sosai ba kaɗan ba, aranta "Tubarakalla Masha Allah" ba jimawa da fitarsa aka kira sallah, da alwala hijabin ammi kawai na zira na tada sallah, ana idar da Sallah a masallaci kowa ya fara watsewa saboda haɗarin daya ƙara hadowa ga iska dake kadawa me daɗi, tare suka dawo gida shida yaya Saddam, babu kowa a falon Ammi daya shigo yana ƙoƙarin shiga ɗakinta ammi ta fito da hijabin da tayi Sallah a jikinta, murmushi ammi tayi tace "yanzu nake shirin kiranka a waya naga garin kamar da haɗari" yace "ehh, haɗarinnema a garin sosai" ammi tace "Allah ya kawo mana ruwa yau, kwanakinnan seya hado kamar za'ayi ruwan seya baje" yace "ameen" ammi ta nufi dinning yabi bayanta, kujera taja masa tace "zauna kaci abincin kar ruwa ya sauko kunanan" zama yayi ammi ta fara saving dinshi, kallon abubuwan datake zuba masa kawai yake, bayan ta gama ya dubeta yace "wai ammi duk wannan abubuwan cikina zasu shiga?" ammi tace "eh mana, kuma seka cinye duka" murmushi yayi kawai ya ɗauki glass cup ya tsiyaya ruwa yayi bismillah ya fara sha, ammi ta wuce ɗakinta, tacewa Maryam taje gurin mijinta, cike da kunya Maryam ta fito falon, tunda ta fito yake kallonta yana taunar ferfesun kayan cikin rago a hankali, kaina a ƙasa na ƙarasa gurin dinning din, saboda kallon kurillan dayake mun, harna zauna a kujerar gefensa be dena kallona ba, kallonshi nayi ina na turo baki gaba amma bance komaiba, ferfesun ya debo a cokali ya kai bakina yana tsareni da ido, buɗe bakinnawa nayi a hankali ina kallon ƙofar dakin ammi ya zubamun, ajiye spoon din yayi yace "nima bani" waro idona nayi waje na nuna masa dakin ammi da hannuna, dage kafaɗarsa yayi alamun ko ajikinsa, murmushi nayi na debo ferfesun a cokali nakai bakinsa, buɗe bakin yayi yana jiran na samansa, sai na ɗauke cokalin na kai bakina na zuba ina murmushi, kallona yayi sai kuma yayi murmushin shima, bece komaiba ya karbi spoon din ya cigaba da cin abincinsa, kaɗan_kaɗan ya taɓa komai da ammi ta zuba masa yasha drinks yace intashi mu tafi, tashi nayi ina faɗin "ina zamu, Ni anan nake kwana