← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 128

Sashe 34

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..........."innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, allahummma ajirni fil masibati, wa'aklifni khairan minha" naita maimaitawa a fili, cikin dimuwa da razanin kwakwalwa, zuciyata na tsananta bugu. Tabbas babu tantama son mustapha nakeyi, nashiga uku ni maryam wacce kaddarace ta kawoni gidannan ta wahala kota azabar rayuwa zankirata. Mikewa tsaye nayi ina goge gumin dake tsatstsafowa asaman goshina. zarya nafarayi ina kaiwa da komowa,cikin mawuyacin halin dabansan yazan misalta muku shiba. Sonake hawaye yasilalomun ko zanji dadin abunda nakeji acikin zuciyata na damuwa. "Yazama dole nacire soyayyar mustapha daga cikin zuciyata, to tayaya? Natambayi kaina, tunanin maganar damukayi da saleemat na tuno. Babu shakka saleemat tagane son yamustapha nakeyi shiyasa tace nayi nesa dashi. Tahakane kawai sonsa zebar cikin zuciyata, kuma sannan zanyi kokarin ganin na cusa son yayasadiq acikin zuciyata tare kuma dadagewa da addu'a, ta hakanne kawai wannan *kaddararren son* zefita daga zuciyata, wannan wanne irin jarabtace, son Wanda besan kanayiba, bemasan dazamanaba, banda haukan so ta bakin yaya sadiq inani inason yayamustapha. mutumin dabe Masan inayiba, besan daniba. zama nayi ina sauke ajiyar zuciya, aganina nasamu mafitar cire son yaya mustapha acikin zuciyata. tunane tunane nayi tayi har akayi sallar isha'i amma nakasa mikewa nayi, yau tsabar firgici kogaida da daddy banjeba, nama manta. dakyar na lallaba naje nayi alwala nadawo nayi sallar. Acikin sallahta addu'a natayi akan Allah yaciremun son yaya mustapha acikin raina,nama godewa Allah dasonnasa beyi mugun tasiri azuciyata. Ina zaune na rafka uban tagumi, naji ana knocking kofata. Ahankali na mike naje nabude, yaya sadiq nagani tsaye,nishaf namamanta yace zamuyi magana. Kasa nayi dakaina saboda kallon daya tastareni dashi, banason yagano wani abu nadamuwa kokadan. Juyawa yayi yana cewa, "kikaraso muyi magana" cikin sanyin jiki nabi bayanshi batare dana amsaba, na zauna agefensa. Yau samannamu shiru, duk basanan, tunda nadawoma ko mommy banganiba nasan suna part din daddy. Satar kallon yaya sadiq yayi, shima duk ya rame kamar baya cikin nutsuwarsa, duk yayi wani iri. Ko duk sonnawane yamaidashi...... "Maryam naji dadin amincewa soyayyata dakikayi, nayi farin ciki Mara misaltuwa, harna rasa bakin miki godiya. Amma dan Allah inason kifadamun gaskiya, har zuciyarki abunda kike fadamun gaskiyane, kokuma kin amincewa soyayyata dan wani abu, kokuma dan kina ganin idan kikaki amincemun kamar bakiyi halarciba. nibanason natursasaki balle namiki dole akan soyyata, kuma banaso ki cutu, inafatan kingane menake nufi. Gyada masa kai nayi cikin danne damuwata nace. "duk abunda nafada maka yaya, har cikin zuciyata yake, cancantarka da kamatarkace yasa na amince maka. Kowacce mace datasan kanta, zatayi alfahari dakai idan ta sameka amatsayin mijinta, shiyasa nima bazanso damarnan ta subcemunba." Daga haka nayi shiru danbansan mekuma zankara cewa, wadannan dinma dakyar na iya furtasu burina a yanzu kawai insamu kadaici. Cikin jin dadin maganganun maryam sadiq yace, "gaskiya bazance nataba jin kalamai masu dadin wannan arayuwataba,idanma naji toh gaskiya namanta, yau kam maryam kinwarkamun da ciwon dake damuna acikin zuciyata, yau zanyi kwanan farinciki dana dade banyi irinsaba, nagode,nagode, nagode sosai, maryam da amsar tayin soyayyata dakikayi, ubangiji yamiki sakayya da gidan aljanna" "amin" na'amsa ina sauke numfashi nakara da fadin, "ammafa yaya sadiq akwai matsala a soyayyarmu" dasauri yajuyo cikin mamaki yana kallona, yace. "Matsala kuma wacce iri kenan" gyara zama nayi cikin jin dacin abunda zanfada nace,"Yaya sadiq koda ahalinka basu hana soyyarmu saboda talaucinaba zasu hana saboda rashin asalina, ninan dakake ganina bansan mahaifinaba kuma bansan kowa nasaba, dangin mahaifiya kawai gare..." Nakasa karasa zancena saboda kukan dayake kokarin kufcemun. Cikin tsananin tausayawa yaya sadiq yace, "kada kidamu maryam dan wannan, ni sadiq ina sonki ahaka kuma zan iya rayuwa dake ahaka, insha Allahu kuma zantayaki da addu'ar Allah ya bayyana miki dangin mahaifinki. Kuma indai maganar iyayenane, daddy bashi da matsala, shi mutum ne me fuskantar abu da kuma masa duba na fahimta, nasan insha Allahu ze fahimcemu. Ita kuma mommy nasan ta yanda zan shawo kanta,harta amince, kikwantar da hankalinki banason ganin kina damuwa." Ajiyar zuciya nakara saukewa akaro na babu adadi, nace. "Shikenan insha Allah zandena damuwar, sannan kuma yaya ina neman wata alfarma dakai guda daya a soyayyarmu dan Allah kamun ita" "uhm, inajinki fadamun wacce irin alfarmace." Cewar sadiq yana maida hankalinsa duka akan maryam. "Yaya sonake ka boye soyayyata dakai,tayanda babu Wanda ze fuskanta" cikin sauri sadiq yace, "banganeba mekike nufiba?" "Ina nufin midunga soyayyarmu aboye kada kowa nagidannan yasani ko kuma wani awaje har zuwa wani lokaci nan gaba." "To maryam mene fa'idar hakan, akwai wani abu aibune a soyayyar tamu, nikam nafison nanuna miki soyayya agaban kowa ta yanda zaki tabbatar da har zuciyata ina sonki" "kayi hakuri yaya, dan Allah kamun wannan alfarma, ina da dalilin haka, idan lokaci yayi zanfada maka dalili. Shiru yaya sadiq yayi na wasu sakanni, sannan yace. "Shikenan maryam namiki wannan alfarmar, inafatan lokacin bame tsaho bane." "Bawani me tsaho bane insha Allah" "tom shikenan kikoma ciki ki huta naga kamar duk agajiye kike, da safe zamu karasa magana" kai kawai na gyada masa na mike na koma daki, dama nagaji da zaman. Shiko sadiq binta yayi da kallo, cikin so da kaunarta gami da tausayinta, ya lura tabbas akwai abunda yake damunta, a yanzu amma ze tambayeta da safe yaji. Ina shiga daki na kwanta saboda nemawa kaina nutsuwa dan har wani jiri_jiri nakeji yana dibata.

**********

Apart din daddy kuwa, yau yaran gidan duk basu je canba, mustapha yana part dinsa suhailat kuma taje gurinsa,dama sune suka fiya zama a part dinnasa. Mommy ce kawai tare da daddy suke hira. Daddy yana lura da lokacin da maryam take zuwa gaishesa, yauseyaga har lokacin ya wuce bata zoba, har an fara kiran sallar isha'i a wasu masallatan. Duban mommy yayi danyakasa hakuri, domin aduk lokacin dayaga maryam zuciyarsa na kokarin tuno masa wani abu daya manta. Yace, "hajiya yau kinga yarinyarnan shiru batazo gaidaniba ko lafiya" takaicine yaturnike mommy, bedamu da yayansa nacikinsa dabasu zoba sewatacan daban, danne rashin jindadin hakan tayi tace, "kasan jiki da jini, kilan tadawo daga makaranta ta gajine, amma innakoma part din zantambayeta dalili." "Hakane, ai yarinyarma tana da kokari gata da hankali da nutsuwa daga ganinta daga gidan tarbiyya tafito" daddy yafadi haka yana mikewa domin zuwa yayi alwala yatafi masallaci. Wani kallo mommy tabishi dashi batace komaiba, se abubuwan datake kissimawa aranta. Shidai daddy toilet yanufa yayi alwalarsa yafice.

*_________________________________________*
*MUSTAPHA*
*_________________________________________*

Komai na tafiyar masa yanda yakamata, musamman agurin aiki, dasukayi promotion din dazasuyi, amma duk da haka yanzu basosai yake samun kansaba, tunda daddy yana gari. Kullum bayan magriba seyaje sun tattaunawa akan harkar kasuwancinnasu, se can dare yake samun kansa. Yau kam daya dawo akwai aikin dazeyi shiyasa beje part din daddyba sedai waya da sukayi, yana dawowa daga masallaci yadukufa akan system. Suhailat bayan ta dawo daga school da yamma likis kamar kodayaushe. Wanka tayi ta shirya cikin wasu hadaddun kaya riga da skirt yan kanti. Tayi kyau sosai, ta bulbule jikinta da turaruka se tashin kamshi takeyi. Yau sotakeyi ta gigita yayannata, tayanda zata samo yayarda ta tabashi, tayi matukar kewar lallausar fatarsa. Cikin takunta na kasaita da isa ta fito tanufi part dinnasa. Kamar kodayaushe kofarsa abude take, shi mutumne ba'abocin yawan rufe kofaba, saboda yatsani ayi knocking yataso yabude, shiyasa yake barinsu a bude, se can dare yake rufewa. bedroom dinsane kawai idan yana ciki yake kullewa. Afalonsa na kasa tatarar dashi, wata dagowar ajiyar zuciya ta sauke tafara binsa da kallo tamkar zata lashesa. Singlet ce ajikinsa da wando three quarter, kasancewar lokacin zafi yashigo yanzu, danshi Allah yahalicceshi mutum ne mejin zafi ajikinsa, shiyasa baya kaunar zafi kokakan. Sallama ta masa,dagowa yayi da sauri yana kallonta dan besan da shigowartaba, kallonta yayi na wasu sakanni, sannan yamaida kansa kan abunda yakeyi bayan ya amsa mata sallamar. Zama suhailat tayi a gefensa cikin faduwar gaba, domin taga daya ganta maimakon yayi murna sema bata rai dayayi. Kurawa damtsensa da kirjinsa ido tayi, tana hadiyar yawu. Sotake takai hannu tatabasa kotaji dadi amma babu fuska, tarasa meyasa yake mata haka yanzu, baya bata duk wata kulawa data dace ta soyayya. Magana tayi masa amma yashareta, batasan haushinta yake jiba saboda shigar datayi, duk da ita suhailat aganinta tayi shigar mutunci,dan tasan halinsa. Cikin raunin murya suhailat ta kara masa magana da fadin, "haba yaya meyasa kakemun hakane yanzu, baka nemana karage duk wata kulawa da kake bani, idannazo gurinkama kokuma inmun hadu, sedai kaita batamun rai, baka sakarmun fuska, pls yaya idan wani abunnamaka kayi hakuri mu koma kamar da, zuciyata baza ta iya jurar wannan yanayinba, kasan ina tsananin sonka da kaunarka." Takarashe maganar da sakin kuka, domin harga ALLAH soyayyarsa na azabatar da ita. Runtse idanunsa yayi, cikin tausayinta. Shikansa bazece ga dalilin dayasa yake mata hakaba. Suhailat tana bukatar kulawarshi, tunda tana tsananin sonsa kuma itace matar daze aura, shi halayentane bayaso amma idan yatuna ba itace babbar me lefiba, lefin mommy ne, tunda itace bata tsawatarmata seyaji haushinta dayakeji yaragu. Ahankali yakai hannu, ya kwantar da kanta akan kafadarsa batare dayace mata komaiba, yaci gaba da aikinsa. Wasu ajiyar zuciya suhailat tahau saukewa, dama abunda takeso kenan, tasan hakan daya mata alamun rarrashine. Lumshe idonta tayi cikin jin dadi tana shakar kamshinsa. Can kuma ta bude idonta ta kurawa kyakkyawar fuskarsa ido, gaskiya tayi dace da masoyi, abunda yake kara rikitata kenan akansa kyawunsa, tarasa ina yasamo wannan kyannasa, tunda mommy da daddy basu kaisa kyauba, a familynsuma kaf tana tunanin babu me kyawunsa. Badon yagama aikinba ya ture system din yace ta bashi labari,bayan yarabata da jikinsa. Aiko suhailat ansamu abunyi nantaita masa zuba, cikin jin dadi, danma yarage mata jin dadin, daya rabata da jikinsa. seda aka kira sallar isha'i tatafi, shima badon tasoba danma dai yace ze kirata anjimane.

**********
Chapter 34 · 0% Book details