← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 128

Sashe 59

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan 40 minutes binta ta karaso gidan da mommy take, bayan tafito daga motarta sungaisa da megadi take tambayarsa ina mommy, dantaga gidan part 2 ne. jagora megadi yamata har bakin part din da mommy take, godiya ta masa ta karasa bakin falon tayi knocking. Ajiyar zuciya mommy ta sauke jin ana knocking, dantasan bintace ta karaso. "A shigo" tafada atakaice domin kofar abude take. turowa binta tayi tashigo taname bin falon da kallo, kafin tace, "atika wannan gidanfa,gidan waye?" mikewa tsaye mommy tayi tace, "bashine abun damuwaba binta ahalin yanzu. Ina cikin matsala kikaraso muyi magana ina bukatar shawararki." binta batayi musuba ta karasa cikin falon tazauna akan kujera ta fuskanci mommy tace, "Atika inajinki wacce irin matsalace gareki, kinsa hankalina gabadaya ya tashi" shiru mommy tayi nakusan mintuna uku kafin tafara magana kamar haka."binta inason ganin bayan mustaphanah, da sulaiman mijina, inason ayau ba gobebe nashafe labarinsu a doron duniya, ke atakaicedai inason nakashesune.!"
cikin tsananin mamaki binta take duban mommy baki bude, kafin tayi karfin halin fadin, "atika! Kinsan mekike fada kuwa, kokinfara haukane, danki da mijinki kikeson ganin bayansu,kikeson kashesu kuma akanme to?" "Akan kudi" mommy tabata amsa agadarance. "Kudi kuma atika, kudinme to?" gyara zama mommy tayi tace, "labarine me tsaho amma zantakaita miki shi nabaki" ........... Labari mommy tabawa binta tundaga ranar dasuka samu mustapha har kawo yau. baki hangame binta take kallon mommy, tama kasa magana saboda dinbun mamaki, gani takeyi tamkar mommy kirkirar labarin tayi kawai tabata, yaron datake matukar sonsa fiye da komai a duniya amma ita take fadin ta masa mugayen abubuwa irinka,gaskiya ta jinjinawa hali irinna mommy, domin duk shedanancinta bazata iya abunda mommy tayiba. Jikinta a sanyaye tace, "Atika!, dagaske kike wannan labarinnaki,nifa kwanyata ta kasa dauka,amma tayaya kika gudanar da duk wadannan ayyuka batare da sanin kowaba tsahon shekaru?" taune lips mommy tayi tace, "kinga alamar wasa akan fuskata dazan miki karya. dagaske nake mustapha badana bane nacikina, kuma ina gudanar da aikinane cikin sirri a wannan gidan nida sadiq, abunda yasa babu wanda ya'ankare tsawon lokacin dana dauka inayi, saboda sadiq nake aikawa gurin boka tsidau, ninayi shekaru banje gurinsaba sedai idan sadiq yaje ya hadamu a waya. ko zuwa gidannan damukeyi babu wanda yasani, danse yamma lis nake zuwa kuma ta get din baya muke fita. Abundai da kawai yarana da megidana suka sani inada wannan gidan kuma ina zuwa lokaci zuwa lokaci ina dubashi." wani dogon numfashi binta taja sannan tace, "yanzu ke Atika duk daular dakike ciki, gamida kudaden da kike juyawa wanda har karshen rayuwarki zasu isheki, amma shine kika aikata haka, gashi yanzu asirinki yatonu, batare da kincinma kudirinkiba. mene amfanin hakan, gaskiya Atika duk tsagerancina gamida son duniyata da shu'umancina amma nasara miki gami da jinjina miki" wani murmushi mommy tayi tace. "Lallai binta haryanzu bakigama sanin Atikaba, tokisani nawuce duk yanda kike tunani indai akan cikar burinane babu abunda bazanyiba arayuwarnan. Dakike maganar kuma duk dukiyar danake ciki, amma senayi hankorin wata. Namiki uzuri, bakisan tarin dukiyar da golds din mustapha sukayibane shiyasa zakice haka"...... "Amm"....."dakata binta" mommy ta katse binta ta hanyar daga mata hannu kamar yadda itama ta katseta. "Bana kirakibane muyita ja'inja kokuma jan maganaba, nakirakine kawai kibani shawara domin kaina gabadaya ya kulle, narasa mafita. gashi kuma boka yamana gargadin dazarar aiki ya lalace karmu koma gurinsa" Ajiyar zuciya binta tasauke tace, "yanzu yakikeso ayi?" mikewa mommy tayi tsaye tadanyi taku sannan ta tsaya tace, "sonake mustapha, menasara da wannan tsinanniyar yarinyar maryam su mutu ayau. Shiru binta tayi kafin yadago kai ta dubi mommy dake kallonta tace. "Kidawo kizauna sena fada miki yanda za'ayi" babu musu mommy tadawo tazauna suka fuskanci juna binta tafara bata shawara.....

suhailat bayan taci kukanta ta koshi bacci yadauketa adakin mommy batare data shirya masaba. se wajen 2 tafarka. tashi tayi dasauri tafito falo,tana mamakin baccin datayi. tsit taji falon babu alamar mutum acikin part din. Dakin aunty ta nufa tana kwala mata kira, amma taji shiru. handle din dakin ta murda tajishi a rufe, tayi knocking ma taji shiru. maryam dake ciki tana bacci batamasan metakeba. duddubawata tayi har kitchen batagantaba, har dakin maryam ta leka. "To ina aunty tatafi, ko itama tatafi tabartane?" tatambayi kanta. kasa ta sauko inda tatarar da daya daga cikin masu aikin gidan a falo. Tambayarta tayi ina aunty, tace mata sunfita ita da su faruq. mamakine yakama suhailat akan ina kuma suka tafi suka barta ita daya agida.sama takoma dasauri ta shiga dakinta tadakko wayarta, number mommy tayi dialing. mommy suna zaune ita da binta sunata sakawa da kwancewa har lokacin kiran suhailat yashigo wayarta. dakkowa tayi taduba ganin sunan Sweet daughter nayawo akan screen din wayar yasata dagawa dasauri. cikin kuka suhailat tace, "mommy, kintafi kinbarni suma gashi suma sunfita dukansu seni kadai agidan" mikewa tsaye mommy tayi tace, "what? daughter banganeba suwaye suka tafi?" "Daddy, da aunty da yaya, dasu yafaruq da wannan yarinyar" muryar mommy narawa tace, "ina suka tafi?" "Bansaniba mom, danbasu fadaminba, nima asabe ce takefadamun" yawun bakin mommy ne ya kafe kaf, murnarta ta koma ciki, dafe kanta tayi, dakyar ta iya kokarin cewa. "Kihada kayanki yanzu zansa adakkoki akawoki inda nake" "to mommy" jefar da wayar mommy tayi, batare data katse kiranba, kotaba suhailat amsaba. "Lafiya Atika mekefaruwa kuma?" binta tatambayi mommy cikin mamakin ganin yanda yanayinta yasauya lokaci daya, harta fara zufa. wani numfashi mommy taja mehade da huci tace, "wai su sulaimanne sukayi tafiya yanzu basa gidan, se suhailat kadai,kenan hakan nanufin zasubar garinne kokuma yaya?" "tafiya kuma, zuwa ina?" binta ta tambayi mommy. "Oho, inazansani inanan" mommy tafadi haka akufule tana share zufar data tsatstsafo mata a goshinta. shiru binta tayi ganin mommy a kidime take. ita kuwa mommy zarya tahauyi a falon tsahon wasu mintuna, kafin ta dauki wayarta dasauri. number sadiq ta lalubo takira, tayi sa'a kuwa tashiga sedai bedagaba harta katse. tamai missed call yakai 5,amma yakidagawa. dole ta hakura takira driver dinta, akan yadakko suhailat yakawota gidan da take.........✍️

*BY*
*zeey kumurya*
*ABUNDA KASHUKA*
_*(shizaka girba)*_

*4️⃣1️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

.........Daddy ne zaune a office din wani doctor yana masa bayanin abunda kedamun matar dayaka buge. "Yallabai ka kwantar da hankalinka ba wata matsala bace babba, buguwa kawai tayi a kanta, kuma alhamdulillah munshawo kan matsalar,fatanmu kawai Allah yasa ta farka cikin hayyacinta. sekuma dogon suma datayi. yanzu zaka iya shiga kaganta, da yardar Allah zata farka zuwa nanda awanni biyu munmata allaurar baccine" wata doguwar ajiyar zuciya daddy yasauke bayan doctor yagama masa bayani. se'alokacin hankalinsa yafara kwanciya yawu ya hadiya dakyar yace. "Shikenan doctor nagode sosai" "babu komai, yallabai. fatanmu kawai Allah yabata lafiya yakuma kiyaye gaba" "ameen,ameen" daddy ya amsa. Paper doctor yamikawa daddy ta magungunan daza'asiyane. sallama daddy yamasa yafita bayan ya karbi paper. dakin da'aka kwantar da direban nan daddy yanufa, yayi sa'a kuwa ya farka har nurses sun cire masa karin ruwan da'aka masa. da sallama daddy yashiga dakin, amsa masa direban yayi yana kokarin mikewa zaune. taimaka masa daddy yayi yazauna yana jera masa sannu. shidai direban mamakin daddy kawai yakeyi yanda yake nuna damuwa da kulawa agaresu tamkar ba shahararren me kudiba,da wanine sedai yabiya kudi yace amsusu dukkan abunda yadace tunda yana da halin yin hakan, shikuma yakama gabansa. Kuma ga dukkan alamu shima yana saurine ze gudanar da wani uzurinnasa. daga ganinsa rayuwarsa bashida damuwa,ko girman kai irinna wasu masu kudin. lallai samun kamar alh, mai nasara se"..... "Sannu, yajikinnaka" daddy yakatse masa tunaninsa da tambayarsa. ajiyar zuciya yasauke yace "dasauki Alhaji" zama daddy yayi akan kujerar dake fuskantarsa yace, "Allah yakaro sauki, yasa kaffarane" "Ameen Alhaji" "yawwa, zuwa yanzu yakamata ace kakira gida kasanar dasu halin da'ake ciki" "nayi yunkurin yin hakan tun dazu, amma Inata kiran number maigidanta ita hajiyar bata shigaba" "Allah, sarki, tokuma babu wani dazaka kira seshi, kota yayantafa" dan jimmm, direban yayi kafin yace. "Ai bata da yaya ranka yadade, sedai yayan yayanta dasuke zaune gida daya, sukuma gaskiya bani da number dinsu" jinjina kai daddy yayi yace. "To ita ina wayarta semunemi number mukira, kaga ai baze yiyu ace haryanzu wani nata besaniba" "hakane, Alhaji, wayartata tana cikin Jakarta, kuma ina tunanin mun barota a cikin motar mu" daddy bekara cewa komaiba se wayarsa daya dakko daga aljihun gaban rigarsa yakira bakaniken daya tura yadauki motartasu, yace masa yaduba motar idan yaga jaka aciki yadakkota yabada akawo masa asibitin aminu kano yanzu. Amsa masa bakaniken yayi cikin girmamawa sannan yaduba, yana dubawa kuwa yaga jakar, a take yabada aka kawowa daddy. Number da matar tayi waya da ita last, ita daddy yakira. wata kawartace dazatayi bikin yarta, bikinma matar tataho, kuma wannan shine karonta na farko zuwa kano daga garin *jos*. kawartata ta rude sosai, dama tanata kiran wayarta taji kota karaso bata shiga, cikin hanzari suka kimtsa ita da wasu yayanta suka nufo asibitin. ansamu number maigidannata ta shiga shima ansanar masa. masallaci daddy yanufa domin yin sallah, bayan yagama kiraye_kirayen wayar zuciyarsa cike da mamakin abunda yatsaida su aunty karasowa asibitin haryanzu..........
Chapter 59 · 0% Book details