← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 128

Sashe 50

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

seda yakarashan ruwan sosai sannan na'ajiye guntun ruwan. bekarayin kukanba hakanyasa na kwantar dashi akan kafadata ina shafa bayansa, abunda yakara burgeni da yaron yanda yake tsaf sewani daddadan kamshi dake tashi ajikinsa. Kallon atika nayi nace tabiyoni dakinta muyi magana, masifa tahauyi wai maganar mezamuyi ita kawai nafada mata inda nasamo yaro, maimakon nakawo mata abinci sedai kawai taga nashigo mata gida da yaro. Juyin duniya atika tashiga daki muyi magana amma taki, dole haka namata bayani atsakar gida. Bala'i da masifar da atika tamun adarennan baze misaltuba tijira kala_kala akan sena fita da yaron daga gidan,kilama wata naje nayiwa cikin shege ta haifamun dan shine zanzo inhada karyata gata wacca batasan metakeba akawomata rainon shege gida. maganganunta sunbatan rai amma dai haka nadaure naki kulata nashige dakina nabarta atsakar gida tanata hayagaga makota najinta.

dakinma bantsiraba haka tabiyoni taitamun tijara. Halaccin da atika tamunne kawai yasa adarennan bantsige igiyar aurena akantaba,amma raina yabaci matuka danne zuciyata kawai nayi bankulataba. Ranar yanda naga dare haka naga rana,ga kukan dayaron yashigayi shima tamkar ana zarar numfashinsa nasan yunwace take damunsa. Seda asuba nasamu yayi bacci, harnaje masallaci nadawo betashiba. Alokacin banhakuraba nakara zuwa dakin atika nabata hakuri dannasan kowacce macece rana tsaka mijinta yakawo mata jariri gida da tunanin dazatayi, da kyar nashawo kan atika tahakura zamu rike yaronnan,amma seda namata uwar magiya daban baki gami da rantse_rantse akan abunda nafada mata shine gaskiyar al'amari. Aranar da duku_duku nafita Neman abunda zamuci, cikin kudurar Allah wani makocinmu yakaini wani guri nayi aikin safiya nasamo dan abunda ba'asaraba. Cikin tsananin farinciki na auno abunda zamuci da kayan hadi na kawo gida, shikuma yaron na auno masa madara gwangwani daya. Koda nakoma gida yanda nabar yaron adakina haka nashigo nasamesa yanata tsala kuka, atika ko kallon inda yake batayiba, cikin sauri nanufeshi nadaukeshi nahau jijjigashi dama ina wajene amma gabadaya hankalina yana kansa. danayiwa atika maganar tanajinsa yana kuka amma ko daukarsane aitayi. Seta kada baki tacemun ita bata haifi daba bazatayiwa wata bautaba, itakuma tanacan tana hutawa. bankulataba nadama madarar danashigowa da yaron da ita nabasa yasha, dannasan yunwace ke dawainiya dashi. bansaniba ko yunwar dake damunsace kokuma danda ruwan sanyi nadama masa yana gamasha se amai. hankalinafa yatashi danbansan mezan kuma bashiba. Ruwa nabashi yasha sannan na masa wanka nagoyeshi abayana bajimawa bacci yadaukeshi. Atikadai sedai ta kalleni tatabe baki. Intakaice muku zance, nikadai nayita wahala da yaronnan inda nasa masa suna *Muhammad mustapha* nayita wahala sosai dashi, dan dafarkoma har rashin lafiya yayi kamar baze rayuba, sedaga baya yasamu lafiya. banfi wata dafara rikonshiba nasamu aiki a wani guri, shinema hankalina yadan kwanta dannasamu sana'ar dazamu dinga kaiwa bakin salati. atika tsana kururu take nunawa mustapha, tun yana yaro haka zatayi ta daka masa tsawa shiko bemasan metakeba. nine wankansa, inbashi abinci, tsarkin kashi da fitsari duk nine tare muke kwana tashi. Sedai innafita atika taga yadameta da kuka sannan zata bashi abinci, tana bashi tana zaginshi wataranma hardasu dungure masa kai. Nikuma Allah yadoramun matsanancin so da kaunar mustapha, bana gajiya da daukarsa inta masa wasa, wannan abun yana kara bakanta ran atika gami da kara mata tsanar mustapha aranta.

Watarana ina daki inayin karatun alkur'ani da sassafene, lokacin mustapha yayi kusan wata takwas ahannunmu, yanata rarrafensa atsakar gida yana wasansa. Atika kuma tanata kokarin hada mana abunkari domin fitar wuri nakeyi zuwa gurin aiki, shayi ta sauke atukunya kafin tajuye a flaks, abunka da yaro yana ganin ta ajiye tukunyar ya rarrafa gurin da gudunsa, ina daga daki ina hangoshi banyi tunanin komaiba dannaga atika tana gurin nasan bazata barshi yataba tukunyarba, sunkuyar dakaina nayi nacigaba da karatuna. Ihun da mustapha ya kwallane yasani dagowa dasauri, hangoshi nayi yabude murfin tukunyar yatsoma hannunshi acikin ruwan shayin atika na kallonshi tacigaba da aikinta. dasauri nafito daga daki nadaukeshi cike da tsananin tausayawa, gabadaya ya gigice se kuka yakeyi da dukkan karfinsa. ruwa nadebo nashiga kwara masa ahannunnasa seda nazuba masa ruwan sosai, sannan nadakko gishiri na barbada masa natottofamasa addu'oi. dakyar nasamu bacci yadaukeshi bayan yaci kuka yagode Allah, muryarshi hardashewa tayi, se faman ajiyar zuciya yake saukewa. Har hawaye seda namasa alokacin tsabar tausayawa. bayan naje na kwantar dashi adaki nafito nasamu atika datake ta aikinta hankali kwance nace mata. "Kin kyauta atika, yau nakara tabbatar da imaninki ragaggene kina kallon yaron harya bude tukunya da ruwan zafi aciki amma kigagara daukeshi. Toya kone hankalinki ya kwanta, zanfita idan kintashi duk abunda kikaga dama kimasa kokasheshinema kiyi,amma kisani Allah baze barkiba, *Abunda kikashuka shizaki girba* kema bakisan ahannun wanda danki ze rayuba nangaba, zaki iya haihuwa kimutu kibar dan, domin babu wanda yasan zeyaru da dansa har abada, itama uwarsa batasan wannan kaddarar zata sametaba aduniya, kuma ki sani zalintar marayan Allah kikeyi,kikiyayi gamuwarki da ubangiji" inagama fada mata haka najuya nafice daga gidan raina a tsananin bace.

Hakadai mukacigaba da rayuwa a garin nijer ina rainon mustapha, yaro me tsananin hakuri idan kaji kukansa tobakaramin abubane, atika tamasa mugunta kala_kala duk abunda zecutar dashi koda tana gani bazata hanaba, yasha zuba yaji a idonsa kokuma yaji ciwo da wani abun. Amma duk da haka yaron Kallon mahaifiya yakewa atika, danyana ganinta sefara wangale mata baki yana mikamata hannu alamun tadaukeshi. Ko yarane suka shigo namakota idan kiwarsa tatashi seyaki zuwa gurinsu yayita binta,ita kuma intaga dama ta daukeshi tana dungure masa kai, idanbatagadamaba kuwa ko kallonsa batayi sedai yayi abinsa shikadai yagama. Mustapha befi shekara dayaba ahannunmu atika tafara laulayin ciki, murna da farincikin danaji bazata misaltuba, duk da ina kallon mustapha amatsayin dana amma nima inason naga dana nacikina, atika tayi murna sosai taita yada habaici ga yaron dabemasan me duniya take Cikiba, dan ita a ganinta danbani da dane yasa nakeson mustapha yanzu kuwa tunda zansamu nakaina sena rage sonsa. batasan abunbahaka bane soyayyar mustapha acikin jinina take, ina kaunarsa sosai gami da matsanancin tausayinsa. Alhamdulillah zuwa wannan lokacin nasamu rufin asirin kaina, natara kudadena. Harna fara tunanin dawowa kasata dazama gabadaya kodan yawan Aiken danakesha daga gurin yan'uwana musammanma Isma'il kanina.

Wataranar juma'a dabazan taba mantawa da itaba arayuwata, bayan ansakko daga masallaci dama ranar juma'a bama fita aiki. Lokacin cikin jikin atika yayi wata hudu, ina zaune adakina ina ware kayana masu amfani damarasa amfani danbanajin zankara sati biyu a nijer. Jakar danake ajiye abubuwa nasauko senajita da nauyi sosai, mamakine yakamani domin ni namamanta da batun jakar da babar mustapha ta bani, tun ranar kuma bankara dakko jakarba. cike da mamaki na ajiye jakar na budeta, tozali nayi da jakar se'alokacin natunata,to jarabar atika kadaima ta isa tasa tamanta da ita. Banyi kasa agwiwaba na dakkota, yarkaramar jakace me gurare ajikinta. Kananun zip din nafara budewa, a wani naga azurfa babba bata danyatasaba ta tsintsiyar hannu, sekuma wani abu kaman tambarin gidan sarauta kona wani abu dai, anyi rubutu da yaren French ajiki, ajiyesu nayi agefe na bude babban zip din jakar, abunda nayi tozali dashi acikin jakarne yakusa zautar dani............✍️

*Ba editing🥺😋*

*TO MASOYA WANNAN SHINE LAST PAGE DINMU KAFIN AZUMI, SEKUMA IDAN ALLAH YAKAIMU BAYAN SALLAH,ZAMU DORA A PAGE 37 INSHA ALLAH, NAGODE MASOYAN ABUNDA KASHUKA ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU ADUK INDA KUKE AFADIN DUNIYA*

*By*
*zeey kumurya*

*ABUNDA KASHUKA....*
_*(shizaka girba)*_

*3️⃣7️⃣*

*INAWA DAUKACIN AL'UMMAR MUSULMI BARKA DA SALLAH, DAFATAN ANYI SALLAH LAFIYA. ALLAH YA MAIMAITA MANA YA AMSHI IBADUNMU,AMEEN*🙏🥰

*Bismillahirrahmanirrahim*
Chapter 50 · 0% Book details