← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 128

Sashe 48

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda kuka sani, sunana sulaiman Abdullahi, iyayenmu mu uku kacal suka haifa, nine babba se mebimun isma'il se auta saudart. Mu cikakkun yan kanone muna zaune a unguwar gwammaja. Mahaifinmu tun muna yara Allah yayi masa rasuwa, lokacin banfi shekara 12 ba,shikuma isma'il shekara 8,yayinda saudart take karama sosai danko yayeta ba'ayiba. Mutuwar mahaifinmu bakaramin girgizamu tayiba nida innarmu,tashin hankalin da muka shiga baze faduba, haka mahaifiyarmu ta rungumemo ta cigaba da rainonmu ta kuma tashi tsaye da neman kudi domin ta rufa mana asiri. Nima tun lokacin banzaunaba nafara yan bugegene domin na dinga taimakawa mahaifiyata, dan babu metaimakonta se Allah, kunsan yanda zumuncin yanzu ya lalace, babu mekulaka sekana dashi, yan'uwan mahaifinmu ba wani kula sukeyi damuba,amma duk da haka bamu yada suba muna zuwa mugaishesu nida isma'il. haka muka cigaba da rayuwarmu cikin rufin asirin Allah, harnakai munzalin zama saurayi, lokacin nagama degree na farko,saboda halin rayuwa sena tsaya da karatun haka nacigaba da yan buge_bugena,dan mahaifiyarmu girma yakamata wasu sana'oin duk bata iyasu. Ina da shekara ashirin da hudu, itama mahaifiyarmu Allah yamata rasuwa bayan gajeriyar jinya datayi, A wannan lokacin munshiga tashin hankali fiye da mutuwar mahaifinmu, danni kusan zaucewa nayi seda aka hadamun da rokon Allah sannan nadawo nutsuwata,haka mukacigaba da rayuwa cikin maraici da kuncin rayuwa, wata cousin din innarmu itace tadauki saudart, domin innarmu bata da yan'uwa dasuke uwa daya ko uba daya. Gidanmu yazama daga ni se isma'il muke rayuwa aciki, bani da wasu abokanai hakama isma'il, mune abokan junanmu komai tare mukeyi mu nemi shawarar juna, muhaka mu binne tare. bayan rasuwar innata da watanni nafara zuwa kasuwa da taimakon wani Dan ajinmu damukai makaranta tare me suna sa'idu. wani alh, yahadani dashi nake masa jiran shago anan kasuwar wanbai,Wanda da shi sa'idunne yake masa,sekuma yanzu yasamu wani kasuwancin shine yakaini na maye gurbinsa. cikin ikon Allah tunda nakoma shagon se cinikin shagon ya ninku fiye dana baya, kullum idan aka tashi daga kasuwa sena biya gidan alhajin munyi lissafe lissafenmu sannan nake komawa gida, to a wannan zuwa gidan alhajin danakeyi anan nahadu da atika (mommy) gidansu makotane da gidan alhajin, kullum naje da yamma zanganta ita kuma tadawo daga islamiyya ita da kawayenta, amma fa kullum cikin yin fada take, wataranma harda dambe, danni kaina nasha rabasu. Kuma a lokacin ba yarinya bace, da girmanta danta zama cikakkiyar budurwa zama tayi shekara 19,sedai tana da karamin jiki. Kullum idan ta ganni setayi ta kallona, nikuma bansan meyasaba dariya take bani saboda tsiwarta,se'inta tsokanarta. Watarana bayan nazo mungama abunda zamuyi da alh, nafito zantafi gida segata da gudunta tatareni tabani wata takarda,nace mata ta mecece, tacemun idannaje gida nakaranta nagani. Banyi tunanin komaiba nakarba nazira a aljihu na wuce gida. Ninama manta da wani batun takardar data bani, seda nazo bacci zancire riga najita acikin aljihuna, dakkowa nayi ina mamakin menene, seda naganta kuma sena tuna, warwarewa nayi nakaranta, gabadaya abunda takardar ta kunsa wai atika tana sonane, dariyama ni abun yabani nazauna nayita kyakyatawa danni a lokacin ko tunanin wata soyayya banayi, tunanin yanda zansamu rufin asirin kaina na tallafi rayuwar yan'uwana kawai nakeyi. Isma'il ne yatambayeni mene yasani dariya haka, takardar hannuna nabasa ina basa labarin atika, tsaki yayi bayan yagama karantawa yakada baki yace, "yaya niko zakayi soyayyama bana fatan kayi da irin wadannan marasa kunyar, dandaga ganinta bata da tarbiyya tunda har tana mace ta iya furta maka kalmarso" bance masa komaiba,saboda bandauki zancen gabadaya da wani mahimmanciba nayi kwanciyata bacci. washegari kamar kodayaushe bayan nabaro kasuwa nazo unguwar su atika, ina fitowa kamar kullum muka kara haduwa da ita, ba kunya tatambayeni kona karanta takardar data bani, nace mata eh, seta tambayeni kona amince da soyayyarta, dariya kawai namata nawuce dan a tunanina wasa kawai takeyi itama. Intakaice muku zance,kullum se atika tatareni ta jaddadamun itafa sona takeyi dagaske, tun ina daukar abun wasa harnima naji nafara tausayinta dan wataran har kuka take sanyamun akan insota, batare danayi shawara da kowaba na amincewa soyayyar atika muka fara soyayya, dukda ni jikina yana bani bazamuyi aureba, danni talakane sukuma su atika suna da kudinsu, seda soyayyarmu tayi nisa nakejin labarin ashe atika itama marainiyace babu uwa ba uba, agurin kanin mahaifinta take, kuma anrigaya da anmata miji, yana kasar waje yana karatune shiyasa ba'ayi aurannasuba. banyi kasa a gwiwaba nasanarwada atika akan muhakura da juna tunda anrigaya anmata miji, amma atika tace sam ita batasan wannan zanceba ni takeso kuma ni zata aura. kanin mahaifinta yafatattakeni yace karna kara zuwa gurin yarsa, idanba hakaba seyasa andaureni, tundaga ranar dayamun hakan koda nazo unguwar bana sauraren atika, amma atika taki hakura dani har kasuwa take biyoni shagona, nayi mata rarrashin duniya akan muhakura da juna,amma atika takiji. Atika irin matannanne masu kafiya da taurinkai, rikicin da'aki da atika agidansu akan tahakura dani baze misaltuba,karshema kanin mahaifinta cewa yayi ta zaba koni koshi tace tazabeni, haka yatattaro mata kayanta yakoreta, tana kuka kanwarta na kuka, dayake su biyu iyayensu suka haifa, kafin su rasu, yan'uwa da abokan arziki suka dinga rokon marikin atika akan yayi hakuri tacigaba da zama agurinsa, amma yace yarantse matukar bata canza ra'ayintaba shima bazata cigaba da zaunar masa agidaba, tunda tace be'isa da itaba. itama atika ta kafe akan bakanta. cikin masu bawa kawun atika baki harda wannan alhajin danake zuwa gurinsa, toni kuma ganin atika ta guji kowa nata saboda ni, senayanke shawarar auranta a wannan lokacin, duk da nasan bawani karfi gareniba amma auranta shine kadai halarcin dazanmata akan abunda tamun. bansamu matsalaba agurin magabatanaba danaje musu da zancen zanyi aure, sudai tunda ficikarsu bazatayi ciwoba basu da damuwa, isma'il nema yanunamun kin amincewarsa danshifa atika bata masaba, dakyar nasamu na rarrasheshi ya amince. Ubangidana shine yatsayamana nida atika a aurenmu, ita yay mata kayan daki da kayan amfanin gida, nikuma yahadamun lefe. Gidanmu damuke ciki dama daki ukune kuma bawasu masu girmaba, guda biyu nagyarawa atika dayan kuma na hanyar kofar gida isma'il yacigaba da zama aciki, ubangidana shine yazama waliyyin atika aka daura mana aure atika tatare agidana, gaskiya babu karya atika tanunamun soyayya, tasoni kamarme azamanmu, dafarko bamu samu wata matsala da itaba,seda Allah yayiwa megidana rasuwa magada suka amshe shagonsu. Nashiga tashin hankali bakaramiba, domin bansan wacce Sana'a zankamaba wadda zan rufawa kaina asiriba. Isma'il shima alokacin baya sana'ar komai, hasalima karatu yakeyi ninake daukar nauyinsa, rayuwafa ta sauyamana gabadaya ga atika nadauke da dankaramin ciki a lokacin, abincin dazamucima wataran gagararmu yakeyi, ga atika bata hakuri kokadan akan rashi, kullum cikin mita da masifa takemun akan nafita nasamota abunda zataci, haka nake fita nayi yan buge_bugena daga bayama senakoma yin dako akasuwa, duk dan asamu abun kaiwa bakin salati.

Watarana ina zaune a kasuwa bayan anyi sallar la'asar naji ankira sunana,cike da mamaki najuya jin muryar abokina sa'idu,cikin mamaki nace, "sa'idu dama rai kanga rai" danrabona dashi tunda yasamarmun aiki agurin megidana. "Gashi kuwa munhadu sulaiman, tun dazu nashigo kasuwar inata nemanka se nura yace inzonan zansameka" gaisawa mukayi cikin farincikin ganin juna, se kallon sa'idu nakeyi yanda yacanza daga gani kudi sunzauna masa, tambayata yayi menakeyi yanzu nace masa buga_buga ce kawai tunda alh, yarasu har yau bansamu wata kwakkwarar sana'aba. jimantamun sa'idu yayi sosai, yace idan zan iya zuwa *NIJER* indinga saida takalma zebani jari narasa nadinga kaiwa can, danshima sana'ar dayakeyi kenan acan shiyasama yabarnan, kuma harkar akwai samu sosai acikinta. shiru nayi ina nazari dagacan kuma nace masa, "toyazanyi da iyalina tunda idannace zantafi dasu candinma bani da masauki kuma bani da kudi balle inkama mana haya" murmushi sa'idu yayi yace, "wannan duk ba matsala bace, zakabar iyalinnaka anan gidane, kafara zuwa kaikadai kafin muga abunda Allah zeyi, zuwa lokacin dazaka samu abunda ake fata seka dauketa kukoma can gabadaya, idankatashi sarar kaya sekazo kaikadai kakoma." godiya nayiwa sa'idu sosai nace masa zanje gida nayi shawara tukunna, yacemun ba matsala idannayi shawarar abunda nayanke zezo gobe mu hadu, seyaji. Koda nakoma gida sena nemi shawarar isma'il akan abunda sa'idu yazomun dashi,aiko isma'il yayi murna sosai, kuma yacemun na amince damace Allah yabani,nanemi albarka abun kawai natafi nafara. banfadawa atikaba seda mukagama magana da sa'idu muka shirya komai yanda abun zekasance, har Lagos mukaje muka saro takalman, nanfa atika tatubure sedai mutafi tare dakyar nasamu na lallabata bayan na cikata da kudi, dannasan mutuniyar tawa akwai son kudi, nakuma ajiye musu komai dazasu bukata itada isma'il ishashshe, alokacin nayi niyyar dakko saudart domin tataya atika zama, amma marikiyartata taki bada ita, dansunsan halin atika ba mutunci garetaba.

Cikin ikon Allah,mukaje nijer lafiya nida sa'idu nakuma fara sana'ata itama da taimakon sa'idu. Naji dadin zama akasar nijer sosai, inda cikin dan kankanin lokaci nasaba da mutane, nakai kusan wata biyu sannan nazo ganin gida, anan na tarar da wani mummunan labari na barewar cikin danabar atika dashi, gashi atika tazama jarababbiya kullum se fada da makota da yawon gantali, isma'il yacemun yana iyakacin yinsa wajen ganin yahanata amma taki hanuwa, banyi kasa a gwiwaba nazaunar da ita namata nasiha takuma nunamun tadauka. Tundaga wannan lokacin nakoma safarar takalma daganan gida Nigeria zuwa kasar nijer, kuma alhamdulillah Allah yadafamun ina samun alkhairi sosai acikin sana'ata. Banfi shekara da fara zuwaba nadauke atika muka komacan Inda nakama mana haya a can din mukacigaba da rayuwarmu, tunda zamana acan yafi yawa gwara ace matata tana kusa dani, yan'uwana kuwa ina musu aiken kudi yanda yakamata. tundaga wannan barin cikin da atika tayi bata kara koda batan wataba, gashi ni kuma Allah ya halicceni mutum ne meson yara, kullum cikin addu'a nake, Allah ya'azurtamu da samun yaya. Atika taso dakko kanwarta jamila tadawo hannunta da zama lokacin dazamu koma nijer,amma kanin mahaifinta yace baze bataba.
Chapter 48 · 0% Book details