Sashe 23
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abangaren mustapha kuwa besan sanda bacci yayi awongaba dashiba. Wajen 1 na dare, yafarka a matukar firgice bakinsa dauke da addu'a saboda wani mugun mafarki dayayi,wanda yakasa fahimtar me mafarkin yake nufi. Gaba daya yahada wata uwar zufa, duk da fankar dake kadawa a dakin, danya kashe a.c tun kafin yakwanta. Sosai mafarkin ya firgitashi amma yakasa tuno komai acikin mafarkin. Ajiyar zuciya yake saukewa akai_akai, abunda kwakwalwarsa ta iya tuno masa shine yaga wata yarinya a mafarkin, da wasu mata da wani namiji, kuma duk kamar yasansu a mafarkin,amma yakasa tunosu azahiri. Korar tunanin mafarkin yayi daga ransa, dan mafarki ba gaskiya bane. Mikewa yayi cikin sanyin jiki ya nufi toilet yadauro alwala,yadawo yafara jero nafilfili kamar yadda yasaba a kowanne daren Allah........
Abangaren sadiq kuwa, tausayin maryam gabadaya yacika masa zuciya, baya kaunar halin mahaifiyarsa dana yan'uwansa kokadan,dandai babu yanda zeyine. Da tunanin maryam ya kwana aransa cikin wani irin bakon yanayi me wuyar fassaruwa agareshi........
*WASHEGARI*
Mustapha kamar yadda yasaba, kullum bayan yafito daga masallaci ya nufi part din mommy, dakin mommy yafara shiga suka gaisa sannan ya nufi dakin aunty. Aunty na zaune akan darduma tana lazimi yashigo dakin, zama yayi agefenta. Yana fadin, "asamu a addu'a aunty" murmushi aunty tayi tace, "insha Allah, addu'a ai kullum cikin ymuku ita mukeyi." Cike da kaunar kanwar mahaifinnasa yagaisheta. Amsawa aunty tayi tare da gyara zama tace, "dama tun jiya inason magana dakai, sekuma bamu haduba" maida hankalinsa yayi duka ga auntyn amma bece komaiba. Cigaba da magana aunty tayi. "Mustapha meyasa jiya ka mari suhailat, nayi mamaki gaskiya dan nasan hakan ba halinka bane?" "Aunty nikaina bansan sanda na maretanba,Abunda tayine ya matukar konamun rai shiyasa" yafadi ahaka muryasa adakile. "Shikenan mustapha amma adai, kiyaye gaba, dan wataran ma'aurata zaku zama kaida ita, jirama nake yaya yadawo kasarnan, ayi maganar aurenku, shekarunku sunja,karatun ta karasa adakinta. Danyanzu ko su haidar da zannurain sun isa aure, balle kuma kai." Kwantar da kansa yayi ajikin aunty yace, "duk yanda kikace haka za'ayi little mom, Allah yatabbatar mana da alkhairinsa." Shafa kansa aunty tayi, tace "ameen" cike da tsananin kaunarsa da tausayinsa, tarasa meyasa takejin tausayinsa aranta, kuma tun yana karami takejin hakan akansa, alhalin babu abunda yanema yarasa arayuwarsa. shiyasa duk miskilancinsa seda tajawoshi jikinta sosai, haryayi matukar sabo da ita, yake kuma sanar mata da duk wata matsalarsa. Hira suka dan taba akan kasuwanci da kuma halin rayuwa, duk da karfin hirar aunty cekeyi. Sannan yatafi....
Duk murna da dokin danakeyi na zuwa school, duk babu dana tashi saboda da bacin rai na kwanta. Ciwon kan dake damuna yasauka sosai, yanayin danake jima kafin na kwanta duk babu, amma zuciyata ce sam babu dadi. Ina idar da sallar asuba, nafara ayyukana, sharar falo nayi da mopping sekuma wanke_wanken kayan da'aci abinci dadaddare. Inagama wanke_wanken nashirya komai tsaf, tare da shareshi shima nayi mopping. Ina kokarin fita daga kitchen din, kuku yashigo, sama_sama muka gaisa dashi bakamar kullumba dayake tsayar dani da surutunsa, duk da hausarsa ko fita batayi,amma munashan hira dashi. harna koma dakina aliya baccintatake, dama tana idar da sallah ta koma. Toilet na nufa na wanke, sannan nayi wanka. Uniform din makarantar na dakko da nufin shiryawa, riga da wadone rigar har gwiwa, se wani karamin hijabi iya kafada.
Tsayawa kawai nayi ina kallon kayan, ina tunanin tayanda zansakasu, harna iya fita dasu ahaka. Ganin lokaci yana kuremunne yasa kawai na daure nasaka, sunkoyi dass ajikina, tsayawa nayi agaban mudubi ina karewa kaina kallo, kayan sunyimun kyau sosai,sedai rigarce ta kamani daga kirjina. Dankwali na daura,nadakko hijabin danayi sallah nafito falo. Kuku begama breakfast ba, gashi har 7/30 tayi. Babuma Wanda yafito acikin gidan. Dakin aunty nanufa, knocking nayi tabani izinin shiga. Da sallama nashiga. Zama nayi akan carpet din dake gaban gadon, ita kuma aunty tana kan dadduma da'alama karatun alkur'ani takeyi, saboda kur'anin dana gani agabanta. Gaisheta nayi ta amsamun cikin fara'arta. Bayan mungama gaisawarne, cikin ladabi nadubeta nace, "Aunty dama nashiryane zamu tafi makarantar, kuma naga haryanzu ko abincin kuku begama hadawa balle nayi serving dinku, kuma yaya sadiq 7/40 yacemun zamu tafi." "Badamuwa maryam, kije kutafi schl din, tunda kinga yau zaki fara zuwa karki fara da latti, aliya tayi serving dinnamu, amma kafin ki tafi kishiga kisanar da aunty atika" "tom aunty nagode senadawo" "yawwa maryam, Allah yakiyaye yabada sa'a, kikula sosai kinji, banda kawaye barkatai,kiyi karatunki kawai" "insha Allah aunty zankiyaye" nafadi haka ina mikewa, tsaidani aunty tayi, hang bag dinta naga ta dakko, kudi ta dakko naira 500 ta mikomun. Girgiza kainayi nace, "kibarshi kawai aunty" batarai aunty tayi tace, "bansan musu maryam, bakici komaiba zaki tafi sannan kuma kiki karbar kudi, kiduba inda ake ajiye kayan snacks a kitchen kidauka kihada da yoghurt wannan kudin kuma kyayi break dashi" amsa nayi namata godiya nafice, cike da kaunarta dakuma yabon halinta. Cikin tsoro nanufi dakin mommy danbansan da fuskar dazata tarbeniba, amma abun mamaki senaganta kamar babu abunda yafaru, takarbeni kamar kullum fuskarta babu yabo ba fallasa, dana fada mata abunda kefaruwama tace muje bakomai, Allah yabada sa'a. Kitchen nashiga na dakko cake da yoghurt kamar yadda aunty ta umarceni, dakina na koma domin dakko school bag dina. Aliya natar tana waya.
Murmushi kawai na mata, cike da mamakinta ko gajiya batayi da waya. cire hijabin jikina nayi, na dakko karamun na makarantar nasaka. "Wow maryam, wlh bakiga yadda uniform dinnan ya miki kyauaba" "aike dama komai kyau yake mun" nabata amsa ina rataya jakata. "Allah dagaske nake maryam, yamiki bala'in kyau, karkijefa ki tadawa malaman makarantar hankali" hararta nayi na dauki hijab din dana cire nakara mayarwa, dangaskiya bazan iya fita hakaba, inajin kunya. Idannaje bakin get nacire naninke nasa ajaka. "Yaya sadiq nefa yakirani yanzu shinema yatasheni daga bacci, yace yana waje yana kiranki,tun dazu." "Ohk,bari nakarasa, sena dawo, bye" "Allah yakiyaye I will miss u wlh" cewar aliya tana marairaicewa. murmushi namata nace, "nima zanyi kewarki sosai da surutunki" dariya mukasa dukanmu namata sallama, na tafi. A bakin part dinmu, naci karo da yaya sadiq, yana kokarin shiga. Cikin mutuntawa mukagaisa, yana sanarmun dama yanzu yake shirin shiga yakirani yaji shiru. Duk da hijabin dake jikina,amma seda yaya sadiq yace kayan sunmun kyau sosai. Godiya na masa cikin jin kunya. Muna tafe muna hirarmu akan makarantar, harmuka karasa parking space. Damuka shiga motane yake kara bani hakuri, akan abunda yafaru jiya, nuna masa nayi bakomai ninama manta. Duk da abun yana raina, musammanma yanayin dana baro yaya mustapha, haka kawai tun jiyan naji badadi saboda fushin dayayi, yauma da kwadayin son ganinsa natashi, inason naganshi naga halin dayake ciki. Harmukaje makarantar tunaninshi kawai nakeyi. Seda muka fara zuwa office din principle sannan akasa wata tarakani class dinmu. Yaya sadiq ma yabani kudi,tun a mota. Duk dagewar danayi bazan karbaba, nakuma sanar masa aunty tabani, amma yabata rai yace dole sena karba. Ganin ransa ya baci sena karba namasa godiya. Bansan yazan misaltamuku yanda nakejin zuciyataba ahalin yanzu, wani irin yanayi take ciki kamar nadamuwa. Amma hakan behanani yin farin cikiba, saboda ganina a makaranta a kuma aji. Ajin yankadan natarar time din dana shiga, kuma mata da mazane a ajin, duk senaji kunya ta lullubeni danni nasaba makarantarmu matane zalla,gashi nacire hijab dina, sekarami na makarantar kawai. Sallama naiwa matan dana tarar a ajin, se bina sukeyi da kallo, duk senaji na tsargu. Watace tamun magana da fara'arta ta kuma nunamun kusa da ita, tace nazo na zauna. Godiya na mata nazauna, tambayata tayi sunana nafada mata. *MARYAM AHMAD* ita kuma tacemun sunanta, *ZAINAB ILYAS MIJINYAWA* banfi 5 minutes dazamaba, malami yashigo ajin..........
Gaskiya makarantar ana karatu sosai, gashi ajin babu yawa. Wani abunnagane wani kuma banganeba, saboda matsalar turanci daba komai nake jiba. Zee mijinyawa tana da kirki sosai, da'aka fito break duk abunda banganeba ita takaramun bayaninsa da hausa,nakuwa gane sosai. Ban fita ko'inaba cake dindanazo dashi naci, itadai zee tafita. Naji dadin makarantar sosai gaskiya, banfuskanci wata matsalaba kodaga gurin sauran yan aji. Malamaima kowa yashigo seya tambayeni sunana, tare damun welcoming. Karfe 2/15 ake tashi daga makarantar. Da'aka tashi tare muka fito da zee da wasu kawayenta, bayan tabani aron books dinta nayi copy note a gida. Kamar yadda yaya sadiq yacemun direba zezo yadaukeni, hakance ta kasance kuwa. Ta gurin number motar nagane shi, saboda duka motocin gidan anrubuta *MENASARA* .yana bakin gate yana jirana kuwa, sallama naiwa su zee nashige muka tafi gida, zuciyata cike da farincikin yau gani na koma karatu,da yardar Allah zancika burina,dana innata.
Mintuna kalililan muka karasa gidan,dama makarantar babu nisa,koda kafama zan iya dawowa. A parking space nakara maida hijabina, danga masu aikin gidan sunata kaikawo, a makarantar ma dan babu yanda zanyine. Aunty da mommy da aliyane, zaune a falon sama. Da sallama nashiga. Atare duk suka amsamun suna kallona, dagudu aliya tataho ta rungume ni, aunty na mata fadan kardai ta kadani. Nima rungumeta nayi cikin murnar ganinta. Jakata ta karba, sannu da gida naiwa su aunty, aunty tamun sannu da zuwa da tambayata ya karatun, mommy kuwa sedai kallonnanta muka shige daki. Aliya kamar ta lasheni, dan murnar dawowata waidama tagaji da zaman kadaici. Kozama banba nashige toilet na watsa ruwa tare da dauro alwala nafito nayi sallah. Kafin na idar aliya harta kawomun abinci,da ruwa. Allah sarki aliya masoyiyar asali, komai nata idan tayi tana tunamun da salimat ne, itama haka take nunamun irin wannan kaunar. Ina cin abinci ina bata labarin school din. Bayan nagama cin abincin na dakko jakata, kudin da aunty da yaya sadiq suka bani nanunawa aliya, cewa tayi na ajiye watara zasumun amfani. Rabawa nayi nabata rabi, amma tacemun wlh bazata karbaba. Cikin jin haushinta na'ajiye kudin, na dakko littafaina na fara kwafar note, itama aliya wani ta dakko tana tayani. Rubutun dayawa, dan anyi nisa a term din. Har bayan magriba muna note din, sallah ce kawai ketadamu. Badon mungamaba,sedon hannunmu dasuka gaji muka bar note din haka gobe nakarasa. Tun dayamma yaya sadiq yakira aliya, wai yaji kona dawo gida. Banima wayartayi mukayi magana, ya tambayeni ya school din da kuma karatu. Nace masa komai lpy klu,sai godiyar Allah.....