← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 128

Sashe 116

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

..........Kallonsa nayi da sauri ina tashi daga jikinsa zuciyata na wani irin bugu, _"baby suhailat"_ na maimaita sunan a raina, kallonta yake shima ganin yadda take binsa da wani kallo kamar na tuhuma, yanda ta kura masa ido ko kiftawa babu ya gane da akwai wani abu, ƙoƙarin janyota jikinsa yayi taƙi yarda, cikin mamaki yace "mene ne wai kike kallona haka?" banza na masa na runtse idona, ina jin wani irin tuk'ik'i a cikin raina, na manta da suhailat kwata_kwata a rayuwata, kenan ashe har yanzu suna tare basu rabu ba suna soyayya, wasu hawaye masu dumi ne suka zubomun daga ido na, mustapha dake kallonta tamkar ya samu TV yaji wani irin zafi a ransa, bayason zubar hawayenta ko kaɗan, datasan yanda yakeji a ransa data dena kuka kwata_kwata a gabansa, janyota jikinsa yayi da ƙarfi yace "meyafaru ne?" janye jikina nayi daga nasa nace "ka kyaleni kaje kacigaba da chat da baby'nka" sai kuma na fashe da kuka, sosai kalamanta suka taɓa zuciya tare da bata masa rai, sai yanzu ya gane akan me take masa haka, latsa wayarsa yayi dan ya duba yaga ko akwai inda ya cewa suhailat wani abu na soyayya ko baby, numfashi ya sauke da yaga sunan da yayi sarved number'n suhailat da shi, a haka Aunty ta turo masa da number'n, shikuma dayazo sarving a wayarsa be canza ba shima yayi sarving a haka, ajiye wayar yayi ya matsa kusa da ita, rungumeta yayi ya fara mata cikin taushin murya yana bata hakuri, amma Maryam taƙi saurarensa kukanta kawai takeyi, rarrashin duniya ba wanda mustapha bewa Maryam ba amma taki ji, yasan dama dole sai yayi fama, amma beyi zaton zata tirje haka ba, ƙarshe ma sai ta bar jikinsa ta koma can ƙarshen gado ta cigaba da kukanta, kyaleta yayi yana jin zuciyarsa babu daɗi ko kaɗan, kansa harya fara sara masa, wayarsa ya ƙara ɗauka, missed voice calls din suhailat ya tarar rututu da taita zuba masa ganin yayi offline, kashe datarshi yayi ya kashe wayar gaba-daya, a hankali na ƙara dawowa kusa dashi, kaina na dora akan kafadarshi ina cigaba da kukana, yana jinta ya mata shiru duk sautin kukan ta na ƙara bata masa rai, yasan shiya mata lefi domin koma ba ita ba, ko wacce mace ce taga haka zata nuna kishin ta, amma shi bega abun ta zauna taita masa kuka ba, bayason kukanta ko kaɗan, amma ita kamar an mata jajjagen albasa a ido, abu kaɗan sai kuka. juyowa yayi a hankali ganin bata niyyar dena kukan cikin tsawa yace "kimun shiru haka" dif ta ɗauke kukannata tana ƙara kankameshi, sosai ta tsorata dashi daya mata tsawar, ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi, a hankali ya janyota ta fado kan cinyarsa, rungumeta yayi tsam a kirjinsa yana sauke numfashi, cizon shi tayi akan brest d'insa, murmushi yayi kawai duk da yaji zafin cizon, dago ta yayi daga kirjinsa yana shafa Brest dinta yace "in rama?" lumshe ido tayi tana turo baki gaba, ya ɗan muntsineta kaɗan, ta kebe fuska kamar zatayi kuka, kissing lips dinta yayi yana murmushi ya jata suka koma kan gadon suka kwanta tana manne a jikinsa, juya masa baya tayi ta matsa daga kusa dashi, janyota yayi tare da juyo da ita cikin lallami yace "am sorry, kinsan bazan iya bacci bakya jikina ba" cikin shagwaba tace "bakai ka mintsineni ba" yana shafa kanta yace "to rama" gashin kirjinshi ta shiga ja tana muntsinin shi akan Brest d'insa, ita a dole ramawa take, cire hannunta yayi da zafi ya isheshi yace "ai kin rama" tace "nidai ban...." bakinsa daya dora akannata yasata yin shiru, ta shiga sauke numfashi, saida yayi kissing dinta sosai sannan ya kwantar da kanta a kirjinshi, ƙara kankameshi tayi tare da dora bakinta akan nipples d'insa tana tsotsa, numfashi yaja sosai saboda baƙon yanayin da yaji a jikinsa, bajimawa bacci ya ɗauketa. Ajiyar zuciya ya sauke ya lullubesu tare tofa musu addu'a. Washegari, kamar yadda ya faɗa suka fita da Maryam ta jido kayan zakinta, sannan suka biya ta capay aka duba mata result ɗinta, yayi kyau Alhamdulillah an samu abunda ake fata.

Yau Monday, misalin ƙarfe 6 na safe Aunty ce zaune a dakinta tana shiryawa domin tafiya Jos, suhailat na zaune a gefen gado tana kallonta, tun da Aunty ta ce mata zatayi tafiya jikinta ya bata Jos zata duk da bata faɗa mata, a karo na babu a daɗi tace "Aunty dan Allah wai ina zaki?" Aunty a kufule tace "inda kika aike ni" suhailat tace "Please Aunty zan biki" Aunty tace "a hakan zaki bini gidan mutane?" suhailat tayi shiru batace komai ba, Aunty tacigaba da shirinta, can suhailat ta ƙara cewa "toh Aunty zani Kano Please" Aunty tayi shiru tana tunanin yakamata kuma suhailat ɗin taje Kano, ko dan damunta da Daddy da su haidar suke da tambayarta ita, amma kuma dole saidai suje tare dan tayiwa Daddy bayanin cikin dake jikin suhailat ɗin, Aunty ta dubeta tace "ki bari idannawo sai na kaiki, tunda ba jimawa zanba a inda zani, gobe zan dawo" suhailat cikin jin daɗin Aunty ta amince zata je Kano, tace "toh" kafin ƙarfe 7, Aunty ta gama shirinta tsaf ita da mamy zasu tafi, amma mamin bata ƙaraso gidantaba, a hanya zasu haɗu, saida tajawa Aliya kunne akan kome suhailat zata mata karta kulata, dan ma yanzu Aunty taga suhailat ɗin kamar tayi hankali. Saukar rana su Aunty sukayi, Maryam tana part ɗin ammi lokacin dan mustapha tun safe ya fice, muna zaune a falo naji sallamar Aunty, da gudu na tashi naje na rungumeta, itama rungumenin tayi cikin murnar gani na, sakinta nayi ina faɗin "Aunty sannu da zuwa" Aunty dake bin Maryam da kallo cikin jin daɗin ganin yanda ta ƙara kyau ba kaɗan ba, tace "yawwa Maryam ɗita" na bata guri ta shige na gaida matar da suka zo tare, ta amsamun cikin fara'a. ammi ta taresu da fara'a itama, bayan angama gaisawa nace "Aunty ina aliya?" Aunty tace "tana gida na baro ta" nace "meyasa baki taho da ita ba?" Aunty tace "saboda school, amma itama taso zuwa" nace "wannan satin zani biki Kano, idan angama bikin insha Allah zan biyo Kadunan" Aunty tace "Allah ya kaimu lafiya" muka amsa da "Ameen" Aunty ta dubi ammi tace "akwai kaya a mota, kuma suna da yawa, akwai wanda ze iya shigo dasu?" Ammi tace "ehh, bari nayiwa mai gadi da mu'azu magana" Aunty tace "toh, direbobin da suka kawo mu suna gurin sai su buɗe musu motocin" ammi ta amsa mata tare da fita waje, tashi nayi na kawo musu ruwa da juice, aunty bin maryam da kallo kawai take, ganin irin canzawar datayi bata wasaba, jikinta ya ciko sosai musamman kirjinta, ga farin data ƙara, kwanciya nayi bayan na kawo musu ruwan domin yanzu nafi jin dadinta fiye da komai, dakin ammi su Aunty suka shiga danyin sallah, ammi ta dawo su mu'azu na biye da ita a baya da manyan jakunkuna a hannunsu masu matuƙar kyau pink colour waɗanda ake zuba kayan lefe a cikin su, suka ajiye suka ƙara juyawa suka kwaso wasu, ɗai_ɗai,ɗai sai da suka shigo da guda goma sha biyu da wasu k'atun_k'atun ɗin leda guda biyu, da mamaki muke kallon kayan nida ammi, amma dai bamuce komai ba, sai da su Aunty suka idar da Sallah sannan take mana bayanin wai kayan lefe nane, mu buɗe mugani. sosai na cika da mamaki domin ban taɓa zaton haka ba, ammi kuwa farin ciki ne ya cikata ba kaɗan ba, domin dama tana da niyyar haɗawa Maryam lefen tunda ba'a mata ba, kaya na alfarma masu kyau da tsada Aunty ta haɗa, dan fiye da rabin kayan order'nsu aka mata ɗaga Dubai, kuma itama tasa kuɗinta a lefen, sosai lefen yayi kyau komai yaji enough, kayan sawa, takalma, mayafai hijabai, kayan bacci, unders, ƙananun kaya, abayoyi, kayan shafe_shafe dana kwalliya, turaruka jakunkuna ɗankunnaye da sarkokinsu, duk dai gasunan, sarkar gold har biyu ta sako ta zobe ɗaya, kallon kayan nake cikin tsananin farincikin wai duka nawa ne, abunda ban taɓa tsammanin zan samu koda kwatan_kwatansu ba, ammi ta rungume Aunty cikin farin ciki tana zuba mata Godiya, kimarta da kaunarta na karuwa a cikin ranta, domin duk wanda zai so ɗanka irin haka babban masoyinka ne. Aunty tace "kidenamun godiya haka ammi, domin nima mustapha ɗanane, duk abunda zanwa su aliya zan masa shima" ammi tace "hakane, Allah yabar zumunci mai ɗorewa a tsakaninmu, ya raya miki zuri'a" Aunty tace "ameen" matsawa nayi jikin Aunty a hankali nace "Aunty nah, nagode sosai Allah yasaka Alkhairi" Aunty ta shafi kuncin maryam tace "mijinki zaki yiwa godiya, dan kuɗin sane" nayi murmushi cikin jin kunya. kafin yamma kowa na gidan yaga lefen banda umaimah saboda batanan, har makota da ake mutunci duk sun shigo sun gani, kowa sai sam Barka da Masha Allah yake.
Chapter 116 · 0% Book details