Sashe 123
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Misalin ƙarfe goma da ƴan mintuna na dare, ina kwance akan gadon yaya inacin dabino, shi kuma yana ƙasa yana operating system, isata dabinon yayi na tashi na ajiyeshi akan bedside, sakkowa nayi na zauna a kusa da yaya ina kallon fuskarshi, a hankali ya dago ya zuba mata narkukkun idanunshi, na matsa jikinsa sosai na kwantar da kaina a kafaɗarsa, ya shafi fuskata yace "har kin gama cin dabinon?" Nace "ehh, ya isheni" wuyanta ya taɓa yace "jikinki da zafi fa jewel" na lumshe ido bance komai ba sai ƙara manne masa jiki da nayi, a hankali nace "yaya zanci kaza gashashshiya" yace "kaza kuma a darennan" na ɗan turo baki nace "uhm" ya shafa ɗamamman cikinta yace "baby kin koyi ci da yawa, yanzu duk abubuwan da kika ci baki k'oshi ba?" cikin shagwaba nace "nidai dan Allah yaya kasiyomun" yace "ki bari gobe idan Allah ya kaimu, yanzu kinga aiki nake kuma dare yayi" nace "a'a nidai yaya ina son ci sosai, idan banci ba bazan iya bacci ba" ya sauke numfashi yace "shikenan ɗauko hijabinki muje" na tashi da murnata na saka hijabi muka tafi, da ƙyar muka samu gurin sai da kazar tunda har yau shima ba gama sanin garin yayi ba, guda uku ya siyo mun yace inta ci, tun a Mota na fara ci dan ina ganin kazar yawuna yayi wani irin tsinkewa, baifi rabin ɗaya ba naci naji na k'oshi, adana abata nayi nace da safe zanci, ina gama ci nasha ruwa na kwanta bacci a jikin yaya, cikin dare cikina yace baisan zance ba ya dinga murdamun, tun inajin abun kaɗan_kaɗan har ya farkar dani daga bacci, juyi na shigayi akan gado ina addu'a, wani irin amai naji yana tasomun da gudu na tashi nayi toilet hakan ya farkar da yaya, amai na shiga kelawa, sai da na amayar da kazarnan tass yaya na zuba mun sannu, ya taimakamun na wanke bakina da fuskata ya dawo dani d'aki, shi kuma ya gyara toilet d'in, da nayi aman naji daɗin murdawar cikin harna samu bacci ya kuma ɗaukeni. Sai dai me kafin asuba na tashi aman ya kai sau huɗu, sai da na amayar da duk wani abu da naci kafin na kwanta, duk jikina yayi laushi ga wata kasala gami da jiri da suka lullubeni, Mustapha hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, tausayinta gaba-d'aya ya gama cikashi, gashi sai kuka take masa sannu kawai yake zuba mata kamar shima zai mata kukan, yana jin tamkar ya dawo da ciwon jikinsa, ruwa ya samu ya tofa mata addu'a ya bata tasha, Allah ya taimaka aman ya tsaya ta samu bacci ya ɗauketa da asuba.
Kafin ƙarfe takwas sun gama shirinsu na zuwa asibiti, asibitin su Dr husnah zai kaita yama kirata tace yazo asibitin ya sameta, yau banyi musun zuwa asibitin ba, danni kaɗai nasan me nake ji a jikina, yau ko aikin gida ban iya yi ba, shi yayi komai, ya sakamun hijabina ya kama hannuna muka tafi, part ɗin Ammi muka nufa, tana kitchen suna aiki, zama nayi akan kujera dan bazan juri tsaiwaba, Ammi ta fito jin sallamar su, kallo ɗaya tayiwa Maryam tasan ba lafiya ba, Mustapha ya gaisheta nima na zamo daga kan kujerar na gaisheta, ammi ta amsamun ta ƙara da faɗin "ɗiyata lafiya kike kuwa?" Mustapha ne ya bata amsa da faɗin "bata jin daɗi ne, yanzuma asibiti zamu na shigo na faɗa miki" Ammi cikin tausayawa tace "Ayya, Allah ya ƙara sauƙi, wanne asibitin zaku kuma?" yace "Asibitin su Dr, husnah dannama kirata tace insame ta ƙarfe 8" Ammi tace "kasan asibitinne?" Yace "A'a driver'n kune ze kaimu, aishi ya sani ko?" Ammi tace "ehh yasani sosaima" Mustapha ya duba tsadadden agogon hannunsa yace "zamu wuce 8 ɗin ta kusa" Ammi tace "saikun dawo, Allah yakiyaye" muka amsa da Ameen, na tashi ina taune lips ɗina, Ammi tace "sannu kinji ɗiyata, Allah ya baki lafiya" na amsa cikin sanyin murya tare da ficewa, yaya ya biyo bayana. ya kama hannuna cikin tausayawa yace "sannu baby" na gyada masa kai kawai yace "har yanzu cikin na murda miki?" nace "a'a bakina ne kawai kemun ɗaci, sai jikina da babu kwari" yace "sorry zai dena insha Allah, ko in d'aukeki nace "a'a, zan iya tafiya" muka ƙarasa parking space yana zubamun sannu, bayan ya kira direban ammi muka shiga motar, muka shiga baya nida yaya ina kwance a jikinsa. Ba nisa asibitin sosai cikin wasu yan mintuna muka ƙarasa, kiran Dr husnah Mustapha yayi ta masa kwatancen office dinta, da tambaya suka gane gurin, sai da muka ɗan jirata ta ƙaraso, dan sanda mukaje bata zoba, bayanta muka bi kamar yadda tace har cikin office dinta muka zauna a kujerun gaban table ɗinta. Dr husnah na duban Maryam tace "amarya ya jikinnaki?" kaina a ƙasa na amsa mata, suka gaisa da Mustapha nima na gaisheta, ta dube ni da kyau tace "me yake damun kine ko kuma ince ya kike jin jikinki?" a hankali nace mata "ina jin jikina babu kwari ga jiri dake damuna, sai kuma zazzaɓi kaɗan_kaɗan, jiya kuma harda amai. Mustapha kallon Maryam kawai yake, yadda take faɗar abunda ke damunta amma shi ko sau ɗaya be taɓa sani ba, kullum sai ta dinga lafiyar ƙalau take. Dr husnah yace "yaushe rabon da kiyi period ɗinki" nayi shiru dannama manta da wani abu period, batare da tunanin komai ba nace "tun azumi" Dr husnah tayi murmushi tana duban Mustapha tace "zamu ɗauki jininta da kuma sauran gwaje_gwaje sai mu gano abinda ke damunta." yace "ok badamuwa."
Anyiwa Maryam duk abunda ya dace, inda sakamako ya bayyana tana da shigar ciki na sati 8, Mustapha jin abun yayi tamkar a mafarki ya rungume Maryam ɗinsa cikin tsananin farin ciki da murna, yayiwa Allah godiya babu a daɗi, alheri mai yawa ya cika Dr husnah dashi sannan suka dawo gida, suna dawowa gida ya bata abinci taci tana gama ci sai bacci, su ammi duk sun shigo sun dubata. Tattalin Maryam sosai Mustapha yakeyi baya barinta tayi komai na aiki, shi yakeyin komai duk da ita batasan hakan tafiso tayi aikinta amma yaƙi barinta, ko Part ɗin Ammi baya barinta zuwa saboda wai idan taje zata iya yin aiki a can, sai dai inya fita ta samu taje. Yau juma'a wanda ya kama babbar Sallah saura sati ɗaya, yau kuma k'anin Ammi da iyalansa da mahaifiyarsu zasu zo, dama suna Dubai yana harkar kasuwancinsa kusan watansu guda kenan a can, yau kuma zasu iso naija da yardar Allah........✍️
*Allah kanunamun ranar da zan gama book ɗinnan🥺.*
*By*
*zeey kumurya*
*ABIN DA KA SHUKA....!*
*8️⃣1️⃣*