← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 128

Sashe 114

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*By*
*Zeey kumurya*
*ABIN DA KA SHUKA...!*

*7️⃣6️⃣*

........... Zama nayi a kan gado na dunk'ule guri ɗaya bance masa komaiba, jin shirun yayi yawa Mustapha ya juyo ya kalleta, keɓe fuska tayi tana turo baki gaba kanta a ƙasa, bece mata komai ba shima ya tashi ya ƙarasa gurin wardrobe ya buɗe ya dakko kayansa ya shirya, ƙofa ya nufa ganin haka Maryam tace, "yaya mezan saka?" batare daya juyoba yace "ki tashi ki dakko mana" bejira amsar taba ya fice, ɗakinta yaje ya dakko mata kaya da duk wani abu zata buƙata, inanan inda ya barni ina tunanin yanda zan iya fita a haka ya dawo, a ƙasan mak'oshi yayi mun sallama, nima na amsa masa a zuciya. Ƙarasawa yayi kan gadon ya ajiye kayan a gabanta, kallon kayan nayi na kalleshi nace "Nagode" ya gyada mun kai kawai, kasa shiryawa nayi duk da ga kayan a gabana, gashi ya ƙuramun ido kuma ya haɗe rai kamar ba shiba. Ganin tana ɓata masa lokaci yace "ke nake jirafa" nace "to ka fita inshirya Please" be tankamun ba, be kuma ɗauke idonshi daga kaina ba, turo bakina nayi hawaye na zubomun na fara shiryawa, tabe baki yayi ya tashi ya ɗauki wayoyinsa ya shiga latsawa, bayan tagama shiryawa tana d'aura ɗankwali ya dubeta yana murmushi yace "kinyi kyau sosai" nima kin kulasa nayi, murmushi yayi me sauti ya ƙaraso inda nake ya kama ɗankwalin yace "kawo in daura miki me kyau" sakar masa nayi, kasancewar kayan nata yadi ne me ɗan santsi saiya kasa daurawa, riƙeshi kawai yayi batare dayasan yanda ze fasaltashiba, cukurkuda mata yayi ya daura mata yace "nagama, kuma bakiga yanda ya miki kyauba sosai" nayi murmushi nace "Nagode bari na gani" na tashi na kalli madubi, dariya ce ta kusan kufcemun saboda wata inyamura dana koma, na danne dariyartawa nayi murmushi nace "kayi ƙoƙari amma bari na gyara maka" yace "ki mace banyiba" murmushi nayi na kunce daurin na sake wani. kama hannuna yayi muka fito falo, wayarsa ce ta fara ringing cikin sound me dadi, bebi takantaba ya zauna akan kujera tare da zaunar dani akan cinyarsa, wayar ya duba yabi bayan kiran ya kara a kunnensa. Ammi tayi masa sallama ɗaga ɗaya ɓangaren, ya amsa mata ya ƙara da faɗin "ina kwana ammi" ammi tace "lafiya kalau, NOOR naga har 10 ta wuce, ga breakfast ɗinkunan nagama tun dazu kazo ka daukar muku, danni bana iya fita idan ana ruwa, umaimah kuma bacci tace" yace "toh ammi ganinan" tace "toh" tare da kashe wayar, ya shafi fuskar Maryam datake kallonsa, a hankali nace "zan bika" yana saukeni daga jikinsa yace "part din ammi zani, na karbo mana break" nace "muje tare kaji" yace "ana ruwan zaki fita" ya ƙarasa zancen yana nufar ɗakinsa, Umbrella ya ɗakko ya fito ya tafi, be wani jimaba ya dawo, da kansa yayi sarving ɗinmu, ya ciyar dani, yace yau bazanyi komai ba shizemun. Soyayya,kulawa, da tarairaiya Maryam tasha su yau a gurin mustapha fiye da koyaushe tun auransu, ita kuwa se shagwab'a da taɓara take zuba masa, ya dakko wayar daya siyo mata ya bata, Maryam murna kamar ta kasheta......

*Bayan sati uku*

Mustapha ne zaune yana kallon labarai a TV, lolaci zuwa lokaci yana kallon kofar ɗakin Maryam, tunda ya dawo daga sallar magriba bai sata a idonsaba, tana ɗaki wai fushi take akan yaƙi siyo mata sweet, sosai shan zakinta ya karu yanzu fiye da da, wanda ya kawo mata daga Kano basu fi sati ɗaya ba ta shanye, ya ƙara siyo mata wasu harta ƙara shanyewa, gashi batason cin abinci yanzu sai yayi mata dagaske yake ta samu taci. wayarsa ce tayi ƙara, ya ɗakko ya duba, Aunty ce take kiranshi ɗagawa yayi da sallama, bayan sun gaisa Aunty tace, "Muhammad, dan Allah inason na haɗa ka da suhailat kuyi magana, kwana biyunnan ta dameni bata da zance sai naka, ko abinci bata ci wlh, sai aikin kuka, damuwarta kuma matsala ce a halin yanzu, because of another reason." Mustapha yayi shiru na wasu sakanni kafin yace, "Aunty me zance mata kuma?" Aunty tace "just took to her koma mene Please!" yace "shikenan amma sai dai muyi chat" Aunty tace "why?" ya mata shiru, dan shi bayajin ze iya ƙara yin magana da suhailat a rayuwarsa, gwaradai chat ɗin, Aunty jin yayi shiru tace "ohk, kuyi chat ɗin" yace "Tom" sukayi sallama ya kashe wayar.
Chapter 114 · 0% Book details