← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 128

Sashe 16

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina cikin baccina naji andakamun duka abaya,da sauri na bude idona saboda dukan ya shigeni. Tozali nayi da aunty suhailat dataketa zabgamun uwar harara. "Sannu hamshakiya kinzo kin kwanta kina bacci,ina abunda nace miki kihadamun?." "Kiyi hakuri aunty suhailat banmasan baccin yadaukeniba,nahada miki drinks din yana fridge." Wani banzan kallo ta jefeni dashi,tace, "to kina nufin dakaina zan dakko drinks din nakaimasa koyaya?." Sakkowa nayi daga kan gadon ina girgizamata kai,hijabina na dauka nasaka nabi bayanta zuwa kitchen. Acikin wasu hadaddun jug na zuzzuba masa drinks din. Bayan su salame tace nabi zuwa inda ta saukeshi,sukuma suna dauke da kayan abincine zasu kaimasa,suna gaba ina binsu abaya. Da nisa gaskiya daga part dinmu zuwa part din da'aka saukeshi. Nidai har yanzu mamakin girman gidannan nake, gida kamar unguwa,gashi part part din gidan yayi yawa. Kamal yana zaune yana latsa wayarsa suka shiga suka ajiye masa kayan abincin,nice ta karshen shiga. araina nace,ji uban kayan da'aka shiryamasa shikadai, kuma idan yatashidai kadan zeci iya cikinsa. wani talakan kuwa yanacan abunda zecima bashi dashi.Tunda na shiga naga yadago ya kuramun ido, yana kallona. Tsaki naja kasa_kasa domin ni natsani kallo arayuwata. Gaishesa nayi ina ajiye masa kayan akan center table din gabansa, amsawa yayi yana bina da wani mayen kallo. Harna juya zanfita yatsayar dani da fadin, "Yan mata baki karasa ladankiba,baki zubamun drinks dinba." Dawowa nayi zan zuba masa, amma bance komaiba, Karamin Kofi nadauka nafara tsiyaya masa,raina yafara baci da kallon dayake bina dashi,duk nabi na tsargu. Shiko kamal se lasar lips dinsa yake tundaga ta shigo falon yaganta yajita masa,aransa yanacewa ina suhailat ta samo wannan yarinyar kyakkyawa, danya shakaf da ita,duk da acikin hijabi take amma daga gani tana da manyan kayan aiki. Yanzu kuwa data tsugunna seya kurawa fuskarta ido,yana ganin yanda taturo dan karamin pink lips dinta gaba, aijiyayi tamkar ya janyota jikinsa ya tsotseshi,daga gani zeyi taushi da dadi. Tundazu nake mika masa cup din,bayan na tsiyaya masa lemon kwakwar amma naji yaki karba,dago kaina nayi dannaga meyahanashi karba,senaga kallona kawai yakeyi sekace ze cinyeni. Kara bata rai nayi nace, "Karbi" adakile nayi maganar. Kamar Wanda ya firgita ya miko hannu da niyyar karba, kawai jinayi ya hada da hannuna ya damke da cup din. Kokarin kwace hannuna nayi amma yaki sakarmun se wani murmushi yake jifana dashi. Kawai jinayi kwalla ta cikamun idona,saboda bakin ciki da takaici,na bude baki zanyi magana aunty suhailat ta shigo falon..............✍️

```Kuyi hakurifa 2 days kunjini shiru,nayi busy ne.amma yanzu komai ya daidaita zaku dinga jina yanda yakamata insha Allah ```

*BY*
*zeey kumurya*

https://chat.whatsapp.com/Fjc94fL7wBLAM29Wl7L1FB
*Masu bina p.c, in'sasu a group din abunda kashuka....yacikane. Amma ga sabonan na bude sekuyi joining. Amma dan Allah,dan girmansa badanniba banda maza mata zallah, kuma idan kinsan ba comment zakiyiba karkishigomun,idan kina group din REAL ZEEY KUMURYA KO ABUNDA KASHUKA..1 shima karki shiga pls and pls.🙏🙏*

*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

```BANI DA BAKIN GODIYA, A GAREKU MASOYANA,SABODA YANDA KUKA NUNAMUN KAUNAR BOOK DINNAN,ALLAH YABAR KAUNA A TSAKANINMU ME DOREWA,ALKHAIRIN ALLAH YAKAIMUKU A DUK INDA KUKE,A FADIN DUNIYA🥰😘.KAMAR YADDA NA MUKU ALKAWARI FARKON WATANNAN ZANCIGABA,GASHINAN NA CIKA ALKAWARINA, SEDAIFA BA KULLUM ZAKU DINGA JINABA.🤗```

*TUKWICI AGAREKI AUNTY ZAINAB ALIYU JIGAWA, NAGODE DA KAUNARKI DA KULAWARKI AGARENI,ALLAH YA BARMU TARE HAR'ABADA😘*

_*THIS PAGE IS FOR YOU,UMMUL AMINA,KIYI YANDA KIKESO DASHI🥰*_

*Bismillahirrahmanirrahim*

1️⃣4️⃣

...........Da sauri na saki cup din dake hannuna bayan yacikamun hannun, cup din ya fadi kasa ya tarwatse cikin tsananin tsorata na mike tsaye, shima mikewar yayi da sauri saboda kar lemon yabatasa. Wani mugun kallo aunty suhailat take bina dashi, cikin tsana dajin haushi. Tana karasowa gabanmu ta daga hannu da nufin ta kwadamun mari, runtse idona nayi cikin tsammanin jin saukar mari, amma har wasu sakanni suka wuce banjiba. Ahankali na bude idona, senaga Ashe bakonnatane ya rike hannunnata yana girgiza mata, kai.cikin tsananin bacin rai ta fara magana. "Haba kamal yazaka hanani hukunta wannan matsiyaciyar yarinyar, baka ganin abunda tayine, sekace mahaukaciya zata wani sakar maka cup, idan da yabata maka jikinkafa" ta karasa maganar cikin karaji da daga murya. "look baby, ai itama tsautasayine batasan hakan zata faruba, haba bakiga yarinya bace kidena mata magana haka mana" wani kallo ta watsama masa batace komaiba, Nidai ajiyar zuciya kawai nake saukewa, cikin hanzari na nufi kofar fita, saboda ganin yana kokarin janyota jikinsa. Zama kamal yayi yadora suhailat akan cinyarsa, yace. "Haba baby bagirmanki bane kidinga daga murya akan abunda bekaiyakawoba." "Hmm, bazakaganebane kamal natsani yarinyarnan over, haushinta nakeji" murmushi kamal yayi aransa yace, "dole kitsaneta mata tunda tafiki komai da komai." Amma a fili seyashiga lallashinta yana tattabeta.......

Da sauri nake tafiya tamkar zantashi sama, tsayawa nayi abakin kofar falo ina daidaita nutsuwata. Ahankali na bude kofar falon na shiga, mommy ce kadai zaune a falon. Sallama na mata kawai na shige dakina. kan gado na fada ina maida numfashi tunanika kala_kala araina, ga haushin wannan dan akuyar yacikamun zuciya,haka kawai ze rikemun hannu wlh, Allah ya isana. Arayuwata na tsani namiji dan iska. Agefe guda kuma ina mamakin aunty suhailat,yanda take mu'amala da dan iska, haryana tabata. Mtss naja tsaki a fili cikin takaici,nakawar da tunaninsu daga araina. Mikewa nayi na dakko rigar *oga* dankarna manta,nakara wani lefin dannaga ya kulu akan rigarnan. Tasss na wanke masa ita a toilet dina, natisa wankinta yakai sau biyar, sedanaga tayi kal sannan na barta. A toilet din nashanya masa.Alwalar sallar la'asar na dauro na fito, dan anyi sallar tun dazu.

Bayan na idar da sallar nafito domin zuwa part din su baaba talatu. Mommy nagani zaune afalo, da suhailat da bakonta. Bata fuska nayi sosai sabida kallon gefen idon dayake bina dashi. Aunty suhailat kuwa se uwar harara take zabgamun, kusa da mommy na durkusa nace, "mommy zanje gurin baaba talatu" kallona tayi na wasu sakanni, batacemun komaiba,harnayi tunanin bazata barniba senaji tace, "ki dauki lemon kwakwa a kitchen zaki ganshi na zuba a jug,kikaiwa my son,seki wuce daganan" "toh mommy nagode." Na'amsa mata cikin ladabi. Kitchen din nashige na dauka, zuciyata nadan bugawa nanufi part dinnasa, harga Allah tsoron bawan Allah nan nake,tsoroma kuwa bana wasaba. A falon kasa na tarar dashi yanada aiki a system dinsa,yacanza kaya zuwa kanana. Sannu namasa, batare daya dagoba ya amsamun dakai, harzankai lemon kan dinning, sekuma naga dacewar na ajiye masa agabansa, akan center table din gabansa na ajiye masa, ina satar kallonsa. Harna juya zantafi yatsaidani da fadin, "exucuse me pls" juyowa nayi ina kallonsa, da hannunsa yanunamun wata kofa a falon yana fadin, "help me with cup" "ohk sir" na'amsa masa cikin ladabi. Kofar dayanunamun na nufa na bude, kitchen din hadadden shima, bantsaya wani kare masa kalloba na nufi inda naga kofinan, seda na daurayesu sannan na kawomasa na fice daga part din.

Ajiyar zuciya nasauke ganin yanzu mun rabu lafiya, part din da baaba talatu ta kwatantamun naje, karamin part ne, yana dauke da babban falo da se dakuna. Gasu salame nan zaune da sauran 'yan aiki, kowa yana sabgar gabansa gaishesu nayi na tambayesu baaba talatu,wani daki suka nunamun godiya na musu nashiga da sallama. Baaba talatu zaune take akan dadduma tana lazimi, zama nayi agefen katifar dake dakin ina jiran ta karasa. "Maryama, ashedai zakizo Aida nayi tunanin bazakizoba" baaba talatu tafada bayan kammala laziminta. "tun dazu nakeson zuwa baaba sekuma nayi wani aiki danagama kuma bacci yadaukeni" "ayya sannunki, aikina da kokari ya aikin,kinadai jin dadinsa" "eh baaba, ai aikinma babu yawa nariga nasaba fiye da haka agida." Gyara zama nayi sosai nace "baaba talatu, dan Allah kikaramun Karin haske akan abunda kikafadamun wlh kullum cikin zullumi nake, da tsoro acikin gidannan" "maryama ki kwantar da hankalinki insha Allah, babu abunda ze faru dake, kedai kawai kidage da addu'a kuma kiyi takatsantsan da kowa na gidannan." Numfashi nasauke nace, "to baaba talatu kincemun lokacin da'akeyin wannan mummunan abun duka yaran gidan basanan towa kike zargi kenan?" "Bawai ina nufin dukansu basananbane kawata_kwata, a'a,lokacin daza'ayi idan wannan yananan to wannan bayanan, zakiga wani lokacin da'akayi mutum ukun sunanan kokuma hudu kokuma biyu,inafatan kingane." Jinjina kai nayi nace, "eh nagane baaba amma ni abunda yafi tsoratar dani dakikace duk wadda akayiwa fyaden mutuwa takeyi" "Eh to gaskiya kuskuren danayi kenan dana fada miki haka, saboda bansan na sauranba,ammadai tabbas na jikata hakance ta kasance." "To shi megidan baaba meyasa bazedau matakiba, kodan gudan bacin sunansa a idon jama'a, musamman dayakasance ana fadar alkhairinsa sosai agarinnan" "bansaniba gaskiya maryam, domin tabbas alh mutumin kirkine" ajiyar zuciya nasauke, nidai har ga Allah zaman gidannan a tsorace nakeyinsa. "Amma baaba da lefin hajiyama, kuma ni tana aikena part din danta ko tunanin wani Abu yafaru batayi. Murmusawa tayi tace, " Aishi wannan gaskiya bana zarginsa saboda kafinma kiganshi a part din hajiya ana jimawa, kuma wannan abunda akeyi adakin masu aikin akeyi harnan akebinsu, shikuwa daga gurin aiki se part dinsa,befiya zuwa nanba gaskiya,amma ai bata aikenkipart din sauran yarannata?" "Ehh,baaba bata aikena." "Yawwa" Munsha hira da baaba talatu sosai, takuma kwantarmun da hankali, Allah yanaji yana gani, kuma baya barci shize kareni,babu wayo ko dabarata. Seda nayi sallar magriba nabar part dinnasu, har kofar part din hajiya ta rakoni. Tambayarta nayi akan zan iya tambayar hajiya zuwa ganin gida, tatabbatarmun dazan iya kuma hajiya zata barni.

Babu kowa a falo yanzu, dakina nashige, rigar yaya dana wanke nadakko harta bushe, dama bata dawani nauyi. Tunda nazo gidan naga iron sabo adakina, bantaba guga dashiba seyau nace bara nagoge masa rigar. Jonawa nayi nafara gogewa, ina gugar ina tunanin maganarmu da baaba talatu, ban'ankaraba tsautsayi ya afkamun iron din yakwashe wani guri agaban rigar kuma dayawa ya kwashe. Wani gumine yafara tsatstsafomun duk da a.c da fankar dake dakin, "nashiga uku ni maryam, meyakaini goge rigarnan, tsautsayi ko karambani yanzu gashi na kona masa, nasan idan yaji lefin dana aikata masa sedai wata baniba" wata hautsinawa cikina yayi, matsanancin tsorone ya lullubeni. Ninke rigar nayi cikin rashin sanin mafita, addu'a nakeyi araina Allah yasaukakamun duk hukuncin dazemun. Adaren yau kam abincima kadan natsakura naci, saboda zullumi. Inayin serving dinsu na kwanta dama nayi sallah ta, addu'a nashigayi araina ga tsoron zaman gidannan ga tsoron gamuwata da oga kwata_kwata,baccinakam adaren ragaggene, dandaima baccin barawone,bansan sanda yasaceniba.
Chapter 16 · 0% Book details