Sashe 110
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ai" be ko kalleniba balle ya tankamun, sallama muka yiwa ammi muka fice, garin da haɗari sosai ga iska me ƙarfi tana kadawa, riƙe hannuna yayi muka ƙarasa part dinmu da ɗan sauri saboda ɗan yayyafin da aka fara, ɗakin shi ya nufa damu, satar kallonsa nayi amma bance komaiba, seda muka shiga ya saki hannuna, bakin gado naje na zauna, shikuma ya ƙarasa gaban mudubi ya cire agogon hannunsa ya ajiye, wayoyinsa ya zaro daga aljihu ya ajiye su suma akan mudubin, ɗaya daga cikin ledodin daya shigo dasu ya dauko ya ajiye a gaban Maryam yace, "ga sweet dinki nan shazumama, na cika alkawari ko?" Murmushi nayi nace "eh mana, Nagode sosai" maballin rigar jikinsa ya fara cewa yana faɗin, "kijirani na watsa ruwa, idan na fito akwai maganar da zamuyi" nace "Toh"ina dudduba ledar daya bani, wata ƙatuwar choculate na ɗakko na buɗe na fara sha cikin jin daɗi, ya ɗan daɗe a toilet din kafin ya fito sanye da bathrobe a jikinsa da ƙaramin towel yana goge sumar kansa, kallonta yayi yaga ledodin data faka a gefenta duk ta shanye abubuwan ciki, alawarta take sha hankali kwance ko kallonsa batayi ba, girgiza kai kawai yayi yawuce gaban mudubi, ina ganin ya matsa na ɗauki ledodin dana zubar na miƙe na fice daga ɗakin, ban dawo ba seda na tabbatar da zuwa lokacin yagama kimtsawa, zaune na sameshi akan gado yana waya, zama nayi agefensa, be wani jimaba sukayi sallama ya kashe wayar kallona yayi yace "Daddy na gaisheki" ɗan ɓata fuska nayi nace "meyasa baka bani shi mun gaisaba? kace ma idan kaje zaka haɗa mu muyi waya" yace "meyasa duk sanda nakira ammi kinyi bacci, ko kuma bakya part ɗin ta? dazuma kafin na taho nakirata bakyanan" nace "bakomai" yace "baccinki kike ko kewatama bakyayi?" na ɗan turo baki gaba nace "to ai kaine baka kira da wuri" yace "ƙarfe goma aiba dare bane sosai, kuma ke Meyasa baza ki karbi wayar ammin kikirani ba ke, kafin kiyi baccin?" Ta kallesa tana fito da manyan idonta waje alamun mamaki. be ƙara ce mata komaiba akan batun, juyowa yayi ya fuskanceta sosai yace "ina son na Miki wata tambaya" nace "Toh" shiru ya danyi na wasu sakanni yana kallonta kamar me nazarin wani abu sannan yace "ya kuke da gwaggo?" kallonsa nayi da sauri dan ban taɓa zaton tambayar daze munba kenan, kauda kaina nayi nace "kakata ce" yace "sure?" Nace masa "eh" gyada kai yayi ya ƙara cewa "ta wajen baba ko mama?" wani abu naji ya tsargamun mara daɗi a cikin zuciyata daya ambaci baba, cikin sanyin murya sosai nace "mama ta" ganin yanda yanayinta ya sauya lokaci se yace "am sorry idan tambaya ta ɓata miki rai" girgiza kai nayi ina maida kwallar da cikamun ido nace "A'a" numfashi ya sauke ya kama hannayena suka biyu ya riƙe cikin nasa yace "zaki iya bani tarihin rayuwarki a yanzu?" sosai tambayar tasa ta daki zuciyata, ban taɓa tunanin ze taɓa mun irin wannan tambayar ba a zamanma auranmu, kallonsa nayi cikin sanyin murya nace "Meyasa ka tambayeni?" "Saboda mun zama abu ɗaya" ya bani amsa cikin tarar numfashina, wata ajiyar zuciya na sauke nace "ehh, zan baka" ya ɗan murza hannuna yace "ki faɗamun komai da komai, kada ki rage ko ki boyemun wani abu daga cikin tarihinki Please" cikin raunin murya nace "insha Allah" be ƙara cewa komai se ido daya zubamun alamun Ni yake sauraro kawai, gyara zama nayi tare sauke wani gwauron numfashi, na bashi tarihin rayuwata tun daga farko har ƙarshe, kallonta yake cike da tsanananin so da kaunarta gami da wani tausayinta me tsanani daya cika masa zuciya, kuka takeyi tamkar ranta zai fita domin an famo mata ciwon dake damunta a cikin zuciya shekara da shekaru, kwantar da kanta yayi akan kafadarsa batare da yayi yunƙurin hanata kukan datake ba, runtse idonsa yayi tare da taune lips ɗinsa, yasan zafin mutum ya taso ace basan danginsaba musammanma dangin mahaifi, domin tunda yake a rayuwarsa be taɓa jin irin zafi da kunar zucin dayajiba lokacin da yaji labarin basu Daddy ne suka haifeshi ba, yasan ɗacin datakeji ranta ya ninka wanda yaji a lokacin, danshi ya taso cikin soyayyar marikansa saɓanin ita data taso cikin kunci da matsin rayuwa gami da maraici, wani irin haushin da zafin gwaggo yake ji a cikin ransa, musamman idan ya tuna mugunta da azabtar da Maryam datayi, da Kuma kai Maryam aikatau datayi wanda badan Allah ya kare taba da tuni bata numfashi a doron duniya, ko kuma kodama tana rayen cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa sanadiyyar aikatau ɗin, a hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa da suka kaɗa sukayi jajur ya saukesu a fuskar Maryam da har lokacin kuka take me ban tausayi, tattausan tafin hannunsa yasa ya fara share mata hawayen fuskarta ciki tausayawa, ji yake shima tamkar ya zubar mata da hawayen, kamar ƙara zugata yayi share mata hawayen da yake maimakon ta dena kukan sema wasu sabbin hawaye ne masu ɗumi suke ƙara kwaranyowa daga idanunta, kamar zeyi kuka yace "Please ki dena kukannan yana taɓa mun zuciya sosai, Please I beg you!" Maryam cikin sheshsheƙa tace "dole nayi kuka, domin kukanne kawai ze ragamun radadin da nake ji acikin zuciyata" shiru tayi tana cigaba da kukan kafin ta shiga girgiza kai tace, "bansan mahaifina ba, bansan kowa nashiba, ban kuma san randa zan sani...." kuka ne yaci ƙarfinta ta kasa ƙarasa abunda take son faɗa, ɗago fuskarta yayi daga jikinsa ya matso da ita daf da tasa, cikin wata irin cool sexy voice yace, "ki dena kuka, na miki alƙawari zan maye miki gurbin baƙin cikin da ke cikin zuciyarki da farin ciki a sauran rayuwarki tanan gaba insha Allah, i promised this" buɗe idona nayi na kalleshi zuciyata na tsananta bugu, idanunshi ya sanya cikin nawa yana mun kallon ido cikin ido kamar ze haɗe idanunnamu guri guda, murya can ƙasan makoshi cikin wani irin salon karya harshe me narkar da zuciya yace *"I LOVE YOU"* kamar wadda aka tsikara haka nayi wata irin zabura domin ban taɓa tunanin jin wannan kalmar daga gareshi ba a yanzu, wata irin harbawa zuciyata tayi, bin fuskarsa na hauyi da kallo cike da tsananin mamaki, jinjinamun kansa yayi alamun tabbatarwa sannan ya ƙara cewa *"I LOVE YOU SO MUCH MARYAMMMMMM.....!"*........✍️