← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 128

Sashe 8

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watarana,danar dabazan taba mantawa da itaba arayuwata, na dawo daga school da murnata,saboda a makaranta anzabemu nida saleemat acikin wadanda zasuyi J.S.S.C.E EXAM. Saboda kokarinmu.base munyi j ss3,ba kawai zamu tafi senior class.kamar kodayaushe idannadawo daga makaranta gwaggo batanan,yauma haka,dakinmu na nufa,inna tana kan sallaya azaune tana lazimi.
"Innata! Innata! na shiga kwada mata kira tare da fadawa jikinta. "Oh ni,fateemah maryam koyaushe zaki girma.dariya nayi nace "kai inna na girma mana,amma agurinkine bana girma,tunda ni kadaice bani da kani.murmushi inna tayi ta shafa kaina tace. " idan baki da kani maryam,ai wataran uwa zaki zama,dan ko yanzu akai miki aure zama zakiyi. Rufe fuskata nayi da hannuna,cikin jin kunya. "Kai inna aure kuma,nidai ban girmaba.sonake nayi karatu me zurfi,na zama likita idan baki da lafiya base munje asibitiba,nizan baki magani da kaina,in miki allura. Murmushi inna ta karayi tace."Allah yasa maryam dita,Allah ya cika miki burinki,nima burina naga kinyi karatunnan maryam. " Ameen innata,yawwa inna,nazo miki da wani daddadan albishir. A makaranta yau aka kawo mana form din makarantar science ta kano,shine aka zabemu hardani da saleemat,nanda watanni kadan zamu zana. "Wacce makarantar science din kuma maryam?. "makarantar da usainan bayan gida tayi me fararen uniform da ratsin Kore. " to aike,maryam naga yanzu aji biyu kike,shine kuma za'akaiki babbar sakandire,ai bakiyi aji uku ba. "Principal din makarantarmuce,ta kirawo mu harda 'yan aji 3,shine aka mana wata 'yar jarabawa kuma naci,makina haryafi na 'yan aji ukun. "Toh shikenan maryam,Allah yabada sa'a ya taimaka. "Ameen inna,nafadi hakan ina mikewa zuciyata cike da murna.na fara cire uniform dina.wani kallo naga inna tana bina dashi Wanda nakasa gane kona mene. " inna lafiya naga kinamun wannan kallon. "Babu komai maryam.mikewa tayi taci gaba da jero nafilfilolinta.lafiya kalau muka wuni da inna,munata hirarmu cikin nishadi. Amma anayin magriba,tacemun kanta yana mata ciwo.ta kwanta,dakyar ta samu tayi sallar isha'i. Ta kara kwanciya.

Cikin dare naji inna tana wani irin nishi,sama_sama nakeji cikin baccina,tun tanayi a hankali harnaji ya hanani bacci.tashi nayi na lalubi makunnin kwan dakin na kunna.

Inna nagani,hannunta dafe da kirjinta,numfashinta na fita dakyar."inna meyafaru,meyasameki.innalillahi.......kanta kawai take girgizamun tanamun nuni da hannunta,tana kokarin yimun magana amma ta kasa.dakyar nagane ruwa take bukata.da sauri na fita na dakko mata me sanyi na kawo mata. Seda tashanye Tass,natambayeta na karo mata tacemun A'a.

Gyara mata kwanciyarta nayi,saboda ganin numfashinta ya fara daidaita.ina jera mata sannu.hannunna ta kama cikin muryar marasa lafiya tafaramun magana."maryam! Kidauki duk kaddarar datazo miki arayuwa,kada ki butulcewa Allah.jikina yana bani bazan kara wasu kwanaki masu yawaba.ki riki gaskiya aduk inda kike,sannan kuma jigon zaman duniya,hakuri. Kiduba kasan gadona,akwai wata akwatin karfe.cikin wata jaka,zakiga wata takarda da wasu hotuna.hotunan mahaifinkine Dana mahaifiyarki,takardar kuma mahaifiyar kice ta rubuta tace abaki.kirjina yanamun ciwo sosai maryam,tamkar andoramun dutse haka nake jinsa inaji ajikina ajalin......da sauri na rufewa inna bakinta ina sakin kuka,"inna kidena cewa haka,bazaki mutu yanzu ba insha Allah,kinyi cutama datafi wannan kuma gashi kin warke,wannanma insha Allah nasan zaki warke. Inna ta bude baki zatamun magana wani tarine ya sarketa,ta fara yinsa ba kakkautawa.tamkar numfashinta ze fita.da gudu na fice daga dakin na nufi dakin da gwaggo take kwana,na fara bubbuga mata kofa da karfi. Dakyar gwaggo ta tashi,cikin masifa take tambayata menene.cikin kuka na mata bayani tataimakeni mukai inna asibiti.amma gwaggo seta rufeni da masifa tana zagina,rokonta nakamayi amma Sam gwaggo taki yarda tace bacci takeji da safe, akaita asibitin babu abunda zefitar da ita cikin darennan.jikina a sanyaye na koma dakinmu.shiru na tarar da inna idonta,a rufe.abunka da yarinta,sena sauke ajiyar zuciya ina cewa,tama samu bacci ya dauketa. Bargo na lulluba mata,nima na kwanta,amma Sam nakasa bacci juyi kawai nakeyi.har asuba. Amma abun mamaki senaga inna bata tashi sallahba,kyaleta nayi saboda naga bata da lafiya.har gari yafara haske inna bata tashiba.kuma abunda yaban mamaki yanda ta kwanta haka take ko juyi batayiba. Tashinta na farayi ina bubbuga jikinta,amma shiru inna ko motsi.hannunta na daga naji yakara nauyi,ina sakinshi naji ya koma sharaf.wata irin bugawa zuciyata tayi,wani gumi yafara tsatstsafomun.kiran sunanta na farayi da karfi ina jijjigata da dukkan karfina,amma shiru.ihu na kurma,na nufin dakin gwaggo ina bugawa inacemata tazo inna ta suma,mukaita asibiti.amma gwaggo tana fitowa ta tsinkamun mari, wai tun cikin dare na hanata bacci.idan ban tafi na bata guriba seta babballani.

Ina gunjin kuka,na zare sakatar gidanmu,na nufi gidansu saleemat.gidan abude yake,idan babansu yaje masallaci baya kara rufewa.ko sallama banyiba saboda rudewa kafata ko takalmi babu,umma tana kokarin hura gawayi saboda yan makaranta ta hangoni nashigo a hargitse. "Maryam lafiya dasassafennan? "Umma kitaimakamun mukai inna asibiti ta suma,kuma babu inda yake motsi ajikint...ai umma bata bari na karasaba tayi hanyar fita,dama da hijabinta ajikinta.bin bayanta nayi.muna zuwa naga ta kara kunnanta akan hancin inna, duddubata naga tanayi.batacemun komaiba,kawai gani nayi taja bargo ta lullube inna har fuskarta.

Janyoni tayi jikinta idanuwanta na zubar da hawaye,sonake nayi magana amma na kasa,saboda nidai nasan Wanda ya mutu kadai ake lullubewa.dakyar na iya tambayar umma cikin rawar murya."umma,bangane me hakan yake nufiba,umma dan Allah kada kicemun innata ta mutu,wlh nima mutuwa zanyi.cikin San kwantarmun da hankali,umma tace"innarki bata mutuba,bari na fadawa baban salermah,yasamo mota mukaita asibiti. Ajiyar zuciya na sauke.umma ta rabani da jikinta ta fice daga dakin.intakaice miki zance,baban saleemah yazo,da wani likita har dakin inna,karshe dai likitan ya tabbarmana,Allah ya karbi baiwarsa inna,ya mata rasuwa.

Cakumar likinta nayi,ina kuka nace."karyane innta bata mutuba,innata bazata taba mutuwa tabarniba.janyeni umma tayi daga jikinsa,itama tana kuka tace."haba maryam, kefa musulmace,kuma kinsan dukkan merai mamacine,ki yarda da kaddara,yanzu inna bata bukatar kukanki addu'arki kawai take bukata. "Yanzu umma kema kinyarda inna ta mutu,wlh bata mutuba suma tayi,damafa bata da lafiya mukaita asibiti,wancan karanma haka tayi,umma kitaimakeni mukaita asibiti,nasan zata tashi,inna bazata mutu ta barniba.kuka kawai nakeyi na fitar hankali,ina maganganu marasa kan gado.hannuna umma ta kama muka fice daga dakin. Duk wannan abun da akeyi gwaggo tana daki tana barci,har lokacin bata fitoba.

Kafin karfe 7 na safe,gidanmu ya cika da mutane anata koke koke,makuta da abokanan arziki domin inna ta kowace,kowa seyabonta yakeyi.se'alokacin gwaggo ta fito ta kama kukan munafurcinta,babu Wanda yabi ta kanta. Nidai ina zaune nayi jigum,kukanma babu ya dauke,zuciyata ta kekeshe.duk da ni yarinyace a lokacin amma nasan dacin mutuwa.bin kowa nake da kallo,domin ni banyarda inna ta rasuba,nasan suma tayi kuma zata farfado. Seda 'yan kauyenmu suka karaso sannan,aka mata sutura.nidai ina daki umma ta rikeni gam taki sakina.wata 'yar uwarsu innace,dasukazo daga kauye tazo ta kama hannuna,ta kaini dakin inna.wata irin harbawa zuciyata tayi saboda ganin inna,kwance a cikin makara,kwace hannuna nayi na fada kan makarar ina sakin kuka."wayyo innata,dan Allah kitashi,karki tafi ki barni,kitashi kice musu baki mutuba,inna bani da kowa seke,meyasa zaki tafi kibarni,kece uwata,kece ubana,kekadai nake gani inji dadi araina,innaaaa!!!..... Kuka yaci karfina. Janyeni akayi,su baban saleemah da wasu 'yan uwan inna,suka kinkimi makarar. Wani karfine yazomun na tashi da sauri, na kankame makarar,ina ihu ina fadin baza'a fitarmun da innataba,amma inaji ina gani aka janyeni aka ficemun,da sanyin idaniyata,me tallafar rayuwata.

Bankara sanin meyafaruba,se farkawa nayi na ganni akan cinyar umma,tanamun firfita,idanta yayi luhu_luhu alamun taci kuka ta koshi.yunkurawa nayi dakyar,na tashi zaune.sannu mutanen dake dakin suka kama yimun,kaina kawai na iya daga musu.saboda wata muguwar sarawa da kaina yakemun.dole na hakura nadau dangana,akan tabbas inna ta rasu.amma tashin hankalin da rudanin da zuciyata ta shiga baze misaltuba.kowa yazo ya ganni seya zubarmun da hawaye.nasiha sosai umma tamun.akan yadda da kaddara.nayi kukan fili Dana zuciya.Mara adadi akan rashin inna.haka akayi sadakar uku aka watse,a lokacin mutuwar inna tadawomun sabuwa.bana ci bana sha,se aikin kuka.dakyar umma take sani nakecin kwayoyin abinci,suma jinsu nakeyi tamkar madaci.komai ya tsayamun cak.kunci da damuwa sun taru sun mun yawa.hakan ya haifarmun da matsanancin ciwon kai,Wanda ko idona dakyar nake motsawa.karshedai har kwanciya nayi a gadon asibiti saboda ciwo,mutuwar gwaggo ta dakeni sosai,kuma har yau bata bar dukanaba,idannatunota inajin tamkar yau abunyafaru.

Ahankali ahankali komai yake wucewa na duniya,haka innata ta shude ta zama sedai tarihinta,ahankali rashinta yafara bin jikina,nabawa zuciyata hakuri da dangana akan rashin innata.addu'a kawai nake mata nasan shine abunda tafi bukata.'yan uwan inna,sunso tafiya dani kauye amma gwaggo tace"zata rikeni anan,saboda makaranta ta,badan sunsoba,suka hakura suka barni,awajenta.

Gwaggo ta gaje,gidan innata,tagaje komai nata.ta koma dakinta ma da zama ni kuma ta koroni dayan dakin.gwaggo bata bani abinci,babu ruwanta da cina balle shana.shargoriyarta kawai takeyi.tatara kawayenta su cika gidan,su kunna kida suyita rawa wataranma har maza take kawowa.mutuwar inna ko'ajikinta.umma ce,take bani abinci da duk wani Abu danake bukata.kudin makaranta kuma babansu saleemat ne yake bamu tare.ahaka rayuwa taita tafiyarmun babu dadi kokadan.cikin ikon Allah muka zana jarrabawa,kuma duk munci nida saleemat.nayi farin ciki sosai,danaci, kuma naji dadi.shine Abu na farko daya sanyayamun rai bayan mutuwar inna.amma naso inna tananan tatayani murna. Babansu salermat ne yamana,komai tun daga uniform,littattafai da duk abubuwan da'ake bukata.duk da shima bawani karfine dashiba,sedai rufin asirin Allah.

Nafara makaranta,kuma inajin dadinta sosai,tana debemun kewa.amma term 2 kawai naje,gwaggo ta hana.tacemun tagaji da zama ba Sana'a dole inzauna,indinga mata Sana'a agida.nayi kuka,na roki gwaggo,amma gwaggo taki hakura.akan haka har fada sukayi da umma.baban saleemat yace"umma ta kyaleta saboda shi bayason fitina.tun daga lokacin gwaggo ta maidani tamkar jaka,ko wata baiwa.nice,wankinta,shara,wanke_wanke,girkin gida dana kayan sana'arta.baruwanta da kankantar shekaruna haka take tulamun uban aiki.bani da Hutu kwata_kwata se cikin dare.Tun inayi ina kuka saboda rashin sabo da gajiya,harna saba.mugunta kala_kala nashata a wajen gwaggo,ta rabani da kowa,har umma ta hanani zuwa wajen ta,sedai na saci hanya naje,bata saniba.naci wahala bakadanba,awajen gwaggo.duk abunda zan mata,bata gani sedai ta sakamun,da duka koda zagi,ko mugun alkaba'i.gwaggo bata da imani,kokadan muguwace ta karshe,kanta kawai tasani arayuwarta.indai zata samu kudi ko menene zatayi,makota kowa kuka yakeyi da ita.saboda munanan dabi'unta.

Ajiyar zuciya,nasauke ina duban baaba talatu,data kuramun ido kawai tana saurarona,idanuwanta na zubar da hawaye.nima hawayen fuskata na share,nace"wannan shine takaitaccen labarina.naso fayyace miki komai,amma lokaci baze barmuba,kuma banason tuno wasu abubuwan da suka faru dani.
Chapter 8 · 0% Book details