← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 128

Sashe 27

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya ma'aikatan gidan sun hadu a harabar gidan suna jiran karasowarsa, suna shigowa kuwa suka nufo motar tasa da musty yake driving domin yimasa sannu da zuwa. Yanadaga cikin motar yake miko hannu suna gaisawa cikin fara'arsa dabata yankewa afuskarsa. Domin shi mutum ne me yalwar fara'a. Har kofar part dinsa musty ya kaisa, sannan yafito dasauri ya bude masa kofa yafito. Daddy kuwa sesamasa albarka yakeyi. Dukansu suka dunguma zuwa part dinnasa dayasha gyara se tashin kamshi yakeyi. Mommy tana gefenshi tanata zuba masa kissa, domin mommy macece me kissa kisisina, duk da tagama mallake daddy se'abunda tace yakeyi, Amma duk da haka yanashan kulawa da tarairaya agurinta. Dakanta ta hada masa ruwan wanka yayi, sannan yadawo falon. Ko zama mommy bata bari yayiba ta kama hannunsa zuwa dinning, zama yayi yana fadin, "kai atika ko yar hirarnan ta yaushe gamo bazaki bari muyiba zaki zarto dani cin abinci, Allah yadawo dani yanzu zakita dirkamun abinci duk nabi na kara kiba.'' Dariya mommy tayi tace, "naji din ai gwara kayi kibar, kokafiso inta barinka da yunwa,kanabin restaurant cin abinci'' murmushi yayi kawai bece komaiba, kamshin abinciccikan gabadaya yagama badade hancinsa. Mommy dakanta tayi serving dinsa, sauran abokanansama dinning din suka dawo, mommy tasa suhailat tayi serving dinsu. Hira sosai sukesha da iyalansa, musamman suhailat auta, databi ta manne masa se shagwaba take zuba masa, shikuma yana biye mata. Sallar la'asarce tatadasu suka nufi masallaci..........✍️

*BY*
*Zeey kumurya*

*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

*Bismillahirrahmanirrahim*

2️⃣2️⃣

........Nima kiran sallar da'aka kwallane yatadani daga barcina badon bacci ya isheniba, ina lumlumshe ido saboda bacci nanufi toilet na kuskure bakina tare da dauro alwala nadawo nayi sallah, addu'ata na dakko nakaranta cikin sauri bayan na idar da sallah. Inagamawa na dauki kayan lesson dina nafita. Babu kowa a falon yayi shiru tsit, a falon kasa nema naga wata me aiki guda daya tana kallo, gaisawa mukayi nafice. Yauma kamar jiya me lesson din haryazo, gaisheshi nayi mukafara abunda ya kawomu. Alh menasara basu koma cikin gida da wuriba daga masallaci saboda gaisawa da jama'a, ya kara fiye da minti talatin sannan suka koma gida. Aka baje afalonsa anata shan hira, alh, menasara mutum ne mejan yayansa ajikiajiki Da nuna musu kauna tsababa,amma shi gaskiya bakamar mommy ba yana tsawatar musu idan sukayi badaidaiba. Masu aikin gidan mata sunata zuwa gaishesa. Sadiq ganin bega maryam tazoba ya mike yafita domin kiranta itama tayiwa daddy sannu da zuwa. Muna cikin yin lesson dinne yaya sadiq yazo gurin da muke, sallama yayi mana muka amsa, yakara da fadin, "maryam daddyfa yadawo tun dazu, anata zuwa yimasa sannu da zuwa amma bangankiba. Dafe kaina nayi nace, "oh am sorry yaya sadiq nayi zaton koyana hutawane yanzu, kar'aje adamesa.'' " A'a babu wani damu kije kawai yanzu anata zuwa yimasa sannu da zuwa'' "gaskiyadai maryam yakamata kije kugaisheshi yanzu" cewar memun lesson daya karbe zancen. "Ohk to malam nagode, bari naje se wani satin kenan ko?" "Ehh maryama Allah yakaimu darai da lafiya." "Ameen" nafurta haka ina mikewa da littafafai ahannuna. Musabaha yaya sadiq sukayi da malam tare dayin sallama muka tafi. Seda nakoma na'ajiye kayan hannuna sannan nafito muka tafi. Muna tafe yaya sadiq namun hira nikuma zuciyata se bugawa takeyi kadan_kadan. Suna cigaba da kwasar hirarsu cikin jindadi muka shigo falon da sallama. Yaya sadiq nagaba ina binsa abaya. Gabadayansu shiru sukayi suna kallonsu maryam sundai amsa musu sallamar dasuka musu. siririn tsaki suhailat taja aranta tace, "narasa meyasa yaya sadiq yake shishshigewa wannan figaggiyar yarinyar, waishi sarkin tausayi." Mommy kuwa kallon data sababin maryam dashi tabita dashi. Su haidar da zannurain kuma da kallon tsana, faruq shidama bedamu da al'amarin kowaba sabgar gabansa yakeyi. Mustapha kuwa kallonsu kawai yakeyi, yana karewa maryam kallo, soyake yagano me fahad yagani ajikin wannan kwailar yarinyar dayabi yarude jiya ya addabeshi da zancenta. Daddyma kallonta yakeyi cikin rashin sani, dan kwata_kwata beyi tunanin me aiki bace. Wani ido naji yana yawo ajikina Wanda yasanyamun wata kasala da mutuwar jiki, bugun zuciyatane yakaro, kasa dago kaina nayi na kalli kowa duk senaji na tsargu. Har gaban daddy yaya sadiq yajani, tsugunnawa nayi agabansa cikin sanyin murya nace, "Ina wuni?" Cikin fara'a daddy ya amsa da lafiya kalau yan'mata ya mutunen gida da karatu?" "Alhamdulillah" daga haka nayi shiru danbansan mezance masaba. Abokanansa danagani na gaisar suma nayiwa mommy sannu da gida. Daddy daketabin maryam da kallo cikin sha'awa, daga gani yarinyar tana da hankali. Maida kallonsa yayi ga sadiq yana murmushi yace, "Abubakar yasunan surukartawane?" Danshi daddy yadauka maryam budurwar yaya sadiq ce. Wata zabura suhailat dake gefen daddy tayi tace, "haba daddy, Allah yasawwake wannan kucakar tazama surukarka,Allah yakiyaye jibetafa daddy wata kazama da ita" "idan tazama kuma sekiyi yaya?" Cewar mustapha yana jifan suhailat da wani irin kallo. Gabadayansu juyawa sukayi suna kallonsa,nima dagowa nayi cikin matukar mamaki na kallesa, ko a mafarki naji muryar datayi maganar sena gane, saboda tana saukarmun da wani yanayi najin dadi ajikina. Tsit suhailat tayi bata kara cewa komaiba, sedai bakin ciki da tsanar maryam daya cika mata zuciya. Mommy kuwa galala tayi kawai tana kallonsa amma takasa magana, se tambayar kanta datakeyi aranta me kalamansa suke nufi akan maryam. Shiko sadiq yaji dadin amsar da yayannasa yabawa suhailat, dan kaf falon babu Wanda ya isa ya tsawatarwa da suhailat mommy ta barshi, harshi kanshi daddy kuwa, mustaphannede kawai. Shiko gogan badawani Abu yafadi hakaba kawai amsa yabawa suhailat danta bashi haushi,bayason adinga muzanta dan'adam. tabe baki yayi yadauke kansa daga kan kowa ganin yanda suka zuba masa ido,sekace Wanda yaci musu bashi. "yaya sunanki yanmata?" Cewar daddy yana tsare maryam da ido, yanda ta dago tayi da idanunta, seyaga tamkar yasan fuskarta kokuma wata mekama da ita,kokuma wani me irin kallonta. "Sunana maryam, kuma nice me'aikin part din hajiya a gidannan" nabashi amsa a kagauce saboda na matsu nabar falon. "Maryam!" Mustapha ya maimaita sunan aransa, betabajin sunantaba seyau inma ankirata agabansa bejiba, shikam tunda yatashi arayuwarsa yakeson sunan maryam, haka kawai kuma yaji yanason sunan, shiyasa da maryam ta fada ya maimaita sunan aransa. "Masha Allah maryama, Allah yayi albarka yataimaka." "Ameen nagode, se'anjima a huta lafiya" nafadi haka ina mikewa gyadamun kai yayi nikuma nafice daga falon. Daga ganin farko nafuskanci alh.menasara yanada kirki bakamar mommy ba, kamar yadda ake fadar halayensa agari, na taimako da yawan sadaka ga marasa karfi. Shiyasa yaya sadiq yake da kirki Ashe halin mahaifinsa garesa kamar yadda kamanninsuma yazama daya.

Maganar mustapha tamun tsaye azuciyata tamkar yanzu yafada se kuwwa takemun akunne, "muryarshi akwai dadi, nafadi haka araina ina lumshe ido. Harna karasa part dinmu,tunaninshi manne a zuciya ta. Dakina nashige na dakko littafina na lesson nashiga dubawa. Acan falon daddy kuwa cigaba sukayi da hirarsu suka manta da wani batun maryam, amma banda sadiq da tunaninta ke tsaye kyam acikin zuciyarsa, da kuma suhailat da haushinta ya cika mata zuciya,gashi akanta mustapha yaji haushinta, tasan setaci kwa_kwa kafin ya hakura. Har dare basu dawo part dinba seyaya sadiq ne kadai yazo yakawomun waya wai aliya takira tace yabani mugaisa. Daganan kuma yazauna muka dan taba hira akan makaranta, naji dadin zamanshi kuwa dan dama atsorace nake da zaman nikadai, dandaima falon kasa da masu aiki, asamane nikadai. Se wajen karfe 9 yatafi yace naci abincina na kwanta su a part din daddy zasuyi dinner. Abincin na debo naci, nakoma daki nayi kwanciyata bacci bayan na bame kofata.......

****************************

Kwanaki nata tafiya rayuwa tana shudewa dadadi babu dadi ga kowanne dan Adam,hakance ta kasance ga maryam. Yau gashi har alh, menasara yayi sati biyu da dawowa. Rayuwata natafiya acikin gidansa, cikin rashin jin dadi, saboda kyara da kyamar danake fuskanta ga suhailat yafi nada. Dadina daya yanzu kawai ina zuwa makaranta ko zama bana samu sosai, danyanzu nafara zuwa islamiyya ta safe 9_11, asabar da lahadi. Yaya sadiq ne yakaini, anan bayan layinmu take babu nisa da kafatama nake zuwa. Kulawa da kaunar da yaya sadiq yake nunamun bazata misaltuba, harna rasa dame zansaka masa arayuwa. Yayimun abunda bazantaba mantawa dashiba akullum cikin yimasa addu'a nakeyi Allah yabiya masa bukatunsa na duniya da lahira. Bani da matsala da megidan kokadan, danshima tamkar aunty yake, gashi da barkwanci da ban dariya, tamkar bame kudiba. Duk da ba kullum nake ganinsaba amma na fuskanci hakan daga gareshi, danseyayi kwana 3 kafin yazo part din mommy,sedai kullum su sunacan. A kowanni sakanni dayake wucewa tunanin mustapha na karuwa a zuciyar maryam, yanzu kam abunna bani tsoro matuka,gashi duk ranar daban ganshiba hankalina atashe yake, nayitabin duk wata hanya kenan danasan zangansa konaji dadi araina. Gashi banasamun ganinnasa kullum senayi kwana 3 ko 4 bamu haduba, sedai idan Allah yataimakeni mommy ta aikeni wani lokacin. Alhamdulillah ina maida hankalina sosai akan karatu danyanzu muna gabda fara jarrabawa. Wani satin zamu fara da yardar Allah. Abangaren sadiq kuwa, yagama tabbatarwa da kansa da zuciyarsa son maryam yashigesa,amma yakasa tunkararta yasanar mata seyayi niyyar fada mata sekuma yakasa, saboda besan yazata dauki al'amarinba, kuma yana ganin kamar tayi kankanta amata zancen soyayya yanzu. Aunty tayiwa daddy zancen yin auransu suhailat da mustapha, amma koda yatuntubi mommy da maganar, setace Sam bata lamuntaba se yarta takarasa karatu tunda saura shekara daya da watanni sugama. Hakuri daddy yabawa aunty akan tabari suhailat din takarasa karatunnata, badon aunty tasoba ta hakura tabisu addu'a kawai. Su mustapha kuwa kai yayi caji sunata shirye_shiryen bikin lukman, ga aikin office gashi kuma komai na bikin dashi akeyi, dukda yaso turjewa akan hidimar bikin amma abokansa sukace be'isaba yana aminin ango dole ayi komai tare dashi.
Chapter 27 · 0% Book details