Sashe 80
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Se kusan la'asar natashi daga bacci. Fuskata na wanke na kuskure bakina sannan na nufi part din ammi, dan anan muke aikin azumi na duka gidan. A baranda natarar da ammi da mama A'isha suna ferayar dankali. Mama kuma tana gefe tana wankin waken kosai. Bayan mun gaisa ammi ta dubeni tace, "ɗiyata har kin tashin kenan, dazu NOOR yashigo ai, yacemun harkun dawo amma kin kwanta, ya exam din.?" Kaina na ƙasa nace, "Alhamdulillah" "Masha Allah, Allah yabada sa'a" gabadaya muka amsa da "ameen" ciki na shige na nufi kitchen. Aunty zuhura ce, kadai a kitchen din tana girki. "Aunty zuhura sannu da aiki" nafada bayan na shiga kitchen din. "Yawwa Mamana, kindawo kenan" "nadawo Aunty zuhura tun kafin 1." "Sannunki ya jarrabawar?" "Lafiya kalau, Aunty zuhura. Bari nazo natayaki aikin" Aunty zuhura na murmushi tace, "dakinyi zamankima danna kusa karasawa miyace kawai tayi saura, kar a wahalar da babynmu" murmushi kawai nayi bance komaiba, nafara tayata aikin. Zuhura dama tana sane tayiwa Maryam wannan zancen, danta fuskanci har yanzu babu abunda yashiga tsakaninsu da mustapha, danta fuskanci yanada shegen miskilanci, amma zata taimakawa Maryam da dabaru ta yanda zataja hankalin mustapha zuwa gareta, Wannan miskilancinnasa duk se tayi maganinsa. fita tayi tacewa Maryam tana zuwa, bayan kamar minti goma ta dawo da waya kare a kunnenta tana faɗin. "Bangane tunda kukayi aure haryanzu babu wani abu daya tsakaninkuba." shiru tayi alamar tana sauraren wanda suke maganar na tsawon 50 seconds sannan tace. "Haba salma kekamar ba wayayyiyaba ace haryanzu kinkasa ɗaukar hankalin Tahir zuwa gareki yana mijinki kuma kuna gida ɗaya, haba salma karki bani kunya mana." Shiru ta karayi na wasu sakanni kafin tace, "wannan duk ba matsala bane, salma dan hadaku aure akayi, ai baza'ace shikenan bazakuyi soyayya kuyi rayuwar aure kamar kowaba, kuma koda baya sonki tunda ke kina sonshi sekiyi kokari kibi duk hanyoyin dazaki jawo hankalinsa zuwa gareki, kefa macece" Takarayin shiru sannan tacigaba da fadin. "Akwai hanyoyi da dama salma dazakibi kijawo hankalin mijinki zuwa gareki, batare daya gane danshi kikeba kokuma kina son shine, shifa namiji tamkar jaririne agurin matarsa duk ta yadda kikabi dashi haka ze tashi yana miki, yanzu idan kika zauna kuncigaba da rayuwa a haka kefa zaki cutu, danshi idan yana da bukatar mace aurensa ze kara, kuma yadinga bawa matarsa kulawa kekuma kina gefe ko oho, gwarama tun wuri kifarka daga nannauyar baccin dakike kibawa makiya kunya, kijawo hankalin mijinki zuwa gareki tun kafin dare ya miki kizo kina cizon yatsa" ta karayin shiru tana saurare sannan tace, "yawwa kawata yanzu naji batu, bari na baki wasu shawarwari danasan insha Allahu zasu taimaka miki. idan yana zaune a falo irin da daddarennan yana kallo, kekuma ki tsalo wankanki cikin kananun kaya, ki baza kamshi a kowanne lungu da sako na jikinki me daɗin gaske, wanda dole idan ya shaka seya dago ya kalleki, karkiji kunya ko tsoron komai, kifito falon abinki kina tafiya ta daukar hankali, kiyi kamar baki ganshiba kishige kitchen kamar zaki dauko abune, in kinfito zaki koma kice masa sannu, kiyi kamar se lokacin kika ganshi kikoma daki abinki, kiyi kamar kwana uku kinayin haka, seki dena fitowar. Nina faɗa miki da gayyama zena zaman falon danyaga fitowarki, duk randa baki fitoba kuwa ki leko ta window zaki gansa yana kallon kofar dakin ki hankalinsama gabadaya baya kan kallon, to yanaso kifito ya shaki kamshi yaga kuma abubuwan harka na juyawa. Sannan kuma kisan dabarun dazaki na yi jikinki na haɗuwa da nashi" Shiru ta ƙara yi, sannan tace. "Kai salma na rasa irinki, yanzu bakisan yanda zakiyi jikinku ya haɗu ba, to bari na baki misali ɗaya. Bayan kinyi abinda nace miki kamar na sati ɗaya ko biyu. wataran bayan kinfito falon, sekinzo kusa dashi, seki fadi da gangan ki zube a kasa, zaki ga yataso da saurinsa yana tambayarki meyafaru duk yabi ya rude, to yana tsoron kar ko kinji ciwo sosai yadena ganin gilmawarki. kekuma seki langwabe harda hawayenki ki rirrikeshi kina nuna masa kin firgitane tare da zuba masa shagwaba, duk miskilancinsa ranar zakisha mamaki nina faɗa miki, kamshin dakike zubawa kadai ya isa ya hautsina masa lissafi." Shiru ta kumayi daga can tayi dariya tace, "yawwa kawata kinfara hawa layi haka nakeso, ki dauke masa hankalin daga kan yanmata masu farautar mazajen wasu, dama gaki da kyanki da jiki na daukar hankali....."
Shawarwari da dabaru masu yawa zuhura ta lissafo sannan tayi sallama ta aje wayar. kallon Maryam tayi wadda tayi tsit tana sauraren zuhura da dukkan hankalinta tace. "Sannu mamana, na barki kinata aiki ke kadai ko, wlh wata kawatace ta kirani akan matsalar ta ita da mijinta" murmushin ƙarfin hali na kakaro nace, "bakomai Aunty zuhura ai babu ma wani aikin" murmushi kawai Aunty zuhura tayi. suna aikin tana satar kallon Maryam, yanda tayi tsumu alamun tana tunanin wani abu, tasan abubuwan data faɗane Maryam take tunani akai, dama kuma duk wayar datayi pretending ne kawai, dan Maryam din taji tayi, ai kuwa tayi nasara danta saka Maryam a zullumi da tunani...
Har aka sharuwa bansakashi a idonaba, jikina yau duk a sanyaye. Maganganun Aunty zuhura se yawo suke a kwanyata. "Tabbas duk abubuwan data faɗa hakane, karnaje natsaya kallon ruwa kwado yamun kafa, yazama dole nima nadage dan ganin na jawo hankalinsa gareni, tunda ina tsananin sonsa, ga kuma masu kawo masa farmaki daga waje, amma matsalar bansan ta ina zan faraba, ko shawarar Aunty zuhura zannema, takaramun haske da dabarun yanda zanjawo hankalinnasa.".... Haka dai naita tunane_tunane nikadai. Be shigo gidanba seda aka idar da da sallar asham, ina jinshi ya kunna kallo a falo amma nakasa fita falon, duk da zuciyata na azalzalata naje nafara aiwatar da abunda naji aunty zuhura nafadawa kawarta amma nakasa, hakura nayi na kwanta bacci saboda tashin dare..... Washegari bantashi daga barci da wuriba saboda yau se 11 mukeda exam, kafinma na tashi daga barci ya fita. seda na gyara gidan tsaf nayi wanka na shirya cikin Uniform dina sannan na nufi part din ammi domin na gaisheta. Suna zaune a falon ita da umaimah nayi sallama na shiga, ammi ta amsamun amma umaimah se bina datayi da kallon banza. muka gaisa da ammi cikin fara'a. duban umaimah nayi dan kar ammi ta zargi wani abu nace mata "Aunty umaimah ina kwana?" Umaimah da tunda Maryam ta shigo taji wani baƙin ciki ya turniketa, saboda ganin Maryam yanzu ya kara tuno mata da abunda yafaru jiya. maimakon ta amsawa Maryam gaisuwarta seta faki idon Aunty ta galla mata harara tare binta da wani wulakantaccen kallo, ran Maryam ya ɓaci taji babu daɗi sosai, amma ta daure ta dubi ammi tace. "Ammi zan wuce naga 10:20 tay..." Bangama rufe bakina sassanyan kamshinsa ya ziyarci hancina. Lumshe idona nayi cikin jin daɗi ina sauraren daddadar muryarsa yana sallama. Rabona dana ganshi tun jiya daya dakkoni daga school, da asubama daya tasheni sahur ban wani ganshiba ina buɗe kofa ya juya ya tafi.. muryarsa naji yana faɗin, "taso mu wuce" mikewa nayi cikin jin daɗi dannasan dani yake. Ammi tana murmushi tace, "har ina zanyiwa yiwa Ali driver magana yakaita, ashema kana tafe" kallon Umaimah data kura masa ido da mayen kallonta yayi, sannan ya maida kallonsa kan Maryam, yana wani kankanne ido irin kallon luv dinnan yace. "Nafison na kaita da kaina ammi, karnaje amun gudu da ita a mota a wahalarmun da ƴar matata." yana gama faɗin haka ya juya ya fice abunsa. Naji daɗin abinda yafada sosai ko ba komai ya wankemun bacin ran da umaimah ta samun, duk da nasan ba har zuciyarsa haka bane, dan umaiman yayi, kamar jiya daya ɗaukeni amma farincikin danaji baze misaltuba, dandai ammi tana gurinne dase na faɗa masa magana nima wanda zata kara kular da umaimah'n. Cikin jin kunya nayiwa ammi sallama nabi bayanshi. Aiko Umaimah ta shaka ba kadanba. Amma duk da haka ba gudu ba ja da baya a son mustapha yanzuma ta fara, wannan soyyayar dayake nunawa Maryam setayi duk yadda tayi ta dawo kanta seta jawo hankalinsa gareta kota yayane.......✍️
*Kuyi hakuri da wannan na koma school ne.*
*By*
*zeey kumurya*
*5️⃣7️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*