Sashe 66
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
farincikin da dady da Mustapha da ammi suka nuna akan haɗuwar Mustapha da mahaifiyarsa a wannan lokacin baze misaltuba, duk miskilancin Mustapha kasa jurewa yayi yaje ya rungume mahaifiyarsa cikin tsananin shaukinta da kaunarta mara misaltuwa a cikin ransa, tabbas ya yarda mahaifiya daban take, dan yanayin dayake jin kansa akan bayyanarta baze misaltuba. ita kuwa ammi se shafa kansa takeyi tana sumbatarsa, takasa dauke ido daga kallonsa ko kunyar surukartata yau bataji. babu abunda yaraba Mustapha da mahaifinsa hatta tafiyarsu kuwa, har miskilanci data fahimci Mustapha'n dashi duk na mahaifinsa ne, yanayin yanda yake kallon abu dakuma lumshe ido shine kawai irinnata, amma komai na mahaifinsa ne. mama ganin kamar sun manta dasu agurin ta junansu kawai sukeyi tace sudai, ammi tazo ta fitar dasu daga cikin duhun dasuke. badan ammi tasoba taraba jikinta dana danta, abin kaunarta tace kowa yaje yayi Sallah don har anyi la'asar sannan ta basu labarin. Bayan kowa ya idar da sallar suka kara hallara a falon dukansu kowa yazaku yaji yanda abun yakasance, dan abun yarikitar dasu bakadanba musamman Maryam da aliya dasukasan mommy ce ta haifi Mustapha. Gyara zama ammi tayi tafara bada labarinta kamar haka...
"Sunana MARYAM IBRAHIM, mu yan ƙasar NIGER ne, anhaifeni a garin NIAMEY. Anan natashi anan na girma anan nayi makarantata anan nayi aure. mahaifina ba wani mekudi bane saidai yanada rufun asiri daidai gwargwado. mahaifiyarmuce kaɗai matarsa kuma mu biyu ta haifa, nice babba se kanina MUHAMMAD. muntaso cikin son junanmu, iyayenmu sunbamu tarbiyya wadda kowa yake yabanmu. inada shekara goma sha biyu kanina kuma tara, Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa. Tun daga wannan lokacin rayuwa ta fara sauya mana,muka fara rayuwar maraici. Muhammad yakasance yaro me kwazo da zuciya. Tun baifi shekara goma sha biyuba, yake ƙoƙarin neman nakansa. Akwai wata makociyarmu matar tana da kirki sosai, kuma tsohuwace ta manyanta. mijinta itama yarasu yabarta da yaya maza guda biyar, tasake aure ta haifi yaro ɗaya shima mijinnata yarasu, se yan'uwan baban yaronnata suka daukeshi. Saboda masu kuɗi ne sosai, mahaifin yaron yamutu yabar masa dukiya me tarin yawa. Duk kafin a haifeni akayi haka, tsohuwar dakanta take bani labari. saboda Allah yahada jinina da ita. nibanmasan tana da wani ɗa ba, bayan biyar ɗin data haifa da mijinta na farko, dan da mijinta na biyun yarasu seta dawo gurin ƴaƴanta suka cigaba da zama tare. Tumunin takabar da'aka bata na gadon mijinta shitake juyawa take saide_saide. matar tana sona sosai kasancewar bata ƴa mace, haka zata saimun kayan kwalliya na mata da abubuwan buƙata. Seda dannata ya girma yazama saurayi sannan yadawo gurin ta, a lokacinma duka yayannata biyar ɗin sunyi aure. Sanda yadawo gurinta inada shekara 16. Kyakkyawane shi, dominshi ruwa biyu ne, mamansa buzuwace kamar mu, mahaifinsa kuma bafulatanine. Haka kawai Allah yadoramun tsoronsa dan gaskiya yana da kwarjini, gashi miskili, kuma baya sakarmun fuska, amma fa akwai shi da kyauta. Abun hannunsa betsone masa idoba. amma suna shiri sosai da kanina Muhammad saɓanin Ni, hakama mahaifiyarmu kullum seya shiga yagaisheta yamata abun arziki. sana'ar saida gwala-gwalai yakeyi yana zuwa Dubai da Saudiya yana sarowa, Allah kuma yabuda masa sosai. sauran yan'uwansa sesuka hade kansu suke nuna basa kaunarsa, afili karara suke nunu masa kiyayya. Amma shi babu ruwan shi haka yake girmamasu kuma komai suka ce yamusu yana musu, yasai musu gidaje yabasu jari, kuma idan suka zo da bukata haka zemusu. mahaifiyarsu da kanta take masa faɗa, akan yadena yawan basu kudi tunda suma barasawa sukayiba. Aduk lokacin da tamasa zancen haka, sedai yayi murmushi yace mata "idan be musuba wazewa bashifa da wasu yan'uwa sesu, tunda mahaifinsa shikadai yahaifa shima. ai bashida kamarsu.
Watarana dabazan taɓa mantawa da itaba a rayuwata. Ranar juma'a da safe. Nashiga gidansu domin duba mahaifiyarsa a lokacin bata da lafiya tana zazzaɓi, ina shiga gidan naci karo dashi a harabar gidan yana tsaye. seda gabana yafadi dana gansa bansan kuma meyasa ba, kuma seyamun kyau sosai tamkar wani Balarabe, satar kallonsa naitayi harnazo giftawa tagabansa seda na lumshe idona saboda kamshinsa dana shaka me dadin gaske. kaina na kasa nagaisheshi. me mamakon ya amsamun seyace mene ne kallonsa. dasauri na dago nasaci kallonsa senaga yahade rai, tsorone yakamani nafara bashi hakuri, ganin duk na firgice seyayi murmushi kawai ya wuce abinsa, nima jikina ba kwari nakarasa ciki. Ranar agidan na wuni inata aikece aikece, shikuma yazo yazauna yasamun ido yana kallona, duk motsin danayi idansa na kaina. duk se naji na takura. In takaicemuku zancedai a daren ranar yacemun yana sona. nayi matukar mamakinsa danni banyardabama,tun daga ranar nafara wasan buya dashi duk hanyar danasan zata hadamu seda na kauce mata, har gidansuma nadena zuwa. har gida mamansu tazo ta sameni tace kotamun wani lefinne nadauke mata kafa, nace mata wlh babu komai. babu yadda na iya haka naci gaba da zuwa gidansu dankar mahaifiyar sa tayi tunanin wani abu.
Aiko watarana yaritsani yace sena fada masa, shi dodo ne danake gudunsa, nace masa a'a. yace to idannakara gudunsa seya fadawa mahaifiyarsa yana sona. dasauri nace masa a'a karya fada mata nadena insha Allah. Tun daga ranar kullum semunyi tadi, dannima gaskiya inason sa. Dan duk inda ake neman namijin da mace zatayi alfahari dashi MODIBBOnah yakai. tun inajin kunyarsa harna rage. munsaba dashi sosai mun kuma shaku iya shakuwa. Tun munayin soyayyar a boye harta fito fili kowa yasani. mahaifiyarsa tafi kowa murna dajin labarin soyayyar mu, saɓanin mahaifiyarmu dabatayi murnaba, bansan kuma meyasa ba dan alokacin bata fadamunba. munkai kusan shekara muna soyayya dashi sannan akayi zancen aurenmu, aka saka ranar aurentamu. ba'awani saka lokaci me tsahoba na bikin. Tun daga lokacin yan'uwansa suka dora mana karon tsana nida mahaifiyata da kanina, wai kwadayine zesa na auresa badon Allah ba. nikuma ina matukar sonsa shiyasa tsanar dasuke mana ko'ajikina mahaifiyarmucema take damuwa. Rana bata karya, segashi lokacin da'aka saka na bikinmu yazo. Ansha shagali sosai anyi taro lafiya angama lafiya, muka tare a gidanmu dake cikin unguwartamu dai, amma da ɗan tafiya daga gidanmu. munyi rayuwarmu ta farinciki da jindadi da kwanciyar hankali, soyayyar damukasha da megidana *ALHASSAN MODIBBO* bazata faduba, yasoni ya tattalani kamar kwai, nima kuma ina matukar sonsa. yabani farinciki arayuwata duk abunda nakeso shiyakemun. Nandanan na murje nakara fari nayi haske, ana ganina anga ina cikin kwanciyar hankali Alhamdulillah. Nanfa tsanar da yan'uwansa sukemun ta karo, waina mallake musu dan'uwa se'abunda nace yayi shiyake. Shifa sesuka fara masa zagon kasa, suna masa wayo suna cin dukiyarsa a boye batare da saninsa ba. Aurenmu befi da wata biyar ba, Allah yayiwa mahaifiyarsa rasuwa, alokacin ina dauke da karamin ciki. Munji mutuwarnan sosai, mutuwar tadakeni nayi kuka tamkar raina ze fita, daga karshema shiya komo yana rarrashina. A hankali mutuwar tabi jikinmu muka hakura muka koma yimata addu'a. Tundaga lokacin yan'uwansa suka fara nuna masa wayonsu a fili, suka dinga binsa suna yabasu kadarorinsa. Shima dake yaganesu seya k',i basu. Mubamu saniba ashe sunacan suna haɗa masa gadar zare. watarana muna zaune a falo da daddare, ranar yadawo daga Dubai yayi sarin gwalagwalai masu yawa, ko inda ake narka masa su a maidasu dankunnaye da sarka bekaiba, ya a jiyesu a gida, yace dasafe zekai dan lokacin yagaji. a lokacin cikina yakai wata 7. Muna zaune naga yakuramun ido yana kallona, tafin hannuna nasa narufe masa idon nace. "Wannan kallonfa" hannuna yacire daga fuskarsa yana bina da wani kallo dayasa jikina duk yayi sanyi yace. "Nasone!" murmusawa nayi cikin jindadi duk da faduwar gaban danakeji amma haka nadaure nace. "Mijina, ina sonka sosai,ina addu'ar Allah yabarmu tare harkarshen rayuwarmu..." kalamai masu dad'i da sanyaya zuciya mukaita fadawa junanmu a wannan daren, a ranar MODIBBO yanunamun soyayyar dabetaba nunamun irintaba, soyayya me tsayawa arai dasanya nishadi a duk sanda aka tunata" shiru ammi tayi tana sauke numfashi, lokaci daya yanayinta yasauya idanunta yakawo ruwa. wani yawu medaci tahadiye sannan ta cigaba da magana. "Amma duk da haka jikina a sanyaye yake kamar wata mara lafiya, shima kuma haka na lura danashi'karfin hali kawai yakeyi. kaina na bisa cinyarsa bacci yasaceni, a falon ya kwantar dani ya tada sallar nafila kamar yadda yakeyi kowanne dare. Bansan mekefaruwaba se farkawa kawai nayi naji suna magana da wasu mutane a falon. bude idona nayi da sauri kokarin mikewa zaune nayi najini rungume ajikinsa. Abunda naji yana fadane ya matukar dagamun hankali. "Kome zakumin kumun,amma karku taɓamun lafiyar matata da abunda ke cikinta" ai bansan sanda na kwace daga rikon dayamunba, ina kallon mutane. Fuskokinsu duk a rufe da wani bakin kyalle. cikin tsorata nace musu. "Suwaye ku,? mekukazoyi gidanmu? mekuke bukata?" Wani me ƙatuwar muryane a cikinsu naji yace. "Ran mijin ki mukazo dauka" cikin zafin rai nace masa, "ƙarya kakeyi, baka isa ka kashe shiba matukar kwanansa bekareba. Ai rannasa ba'a hannunka yake......" kafin na karasa maganata naji daya a cikinsu yadagi yacillar gefe, cikin zafin naka da karfin zuciya namike zankoma gun mijina, suka karayin gefe dani. Intakaice muke zance, ina kallo a gabana, mutanennan marasa imani da tausayi masu zuciyar kafirai suka yankamun mijina, duk da uwar magiyar daya musu akan su kyaleshi karsu maida masa da ɗa/ya Maraya tun kafin suzo duniya, su fadi ko nawa sukeso,kome sukeso zebasu,amma sukace su sam basa bukatar komai. ransa kawai suke da bukata. Inaji ina gani suka masa yankan rago" kuka me karya zuciyar me saurarensa ammi tafashe dashi tamkar a lokacin abun yafaru.......✍️
*BY*
*zeey kumurya*
*4️⃣7️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
...........Babu wanda bezubar da hawayeba a falon se dady da Mustapha. shikam Mustapha zuciyarsace take tafarfasa tsabar bakin ciki da tausayin mahaifansa, jiyayi dama shima kukan zesamu yazo masa, koyaji sauƙin radadin dake damunsa a zuci. Farararen idanunnan nasa sun kada sunyi jajur, jijiyoyin kansa gaba daya sun mike sunyi rudu_rudu. kasa kawai yayi dakansa yana fesar da zazzzafan huci daga cikin bakinsa. daddy ma dauriyace kawai domin karya kara karyarmusu da zuciya, lallaminsu yafarayi duka da fadin. "Kuka bashine maganiba, duk da nasan tausayine yasaku kukan, amma yakamata kuyi hakuri kuyi shiru, kar kukan yajanyo muku wata matsalar, musammanma ke dakike kukan tun dazu" yakarashe zancen yana kallon ammi. shiru suka masa babu wanda yace masa kala, dakyar dai dady yashawo kan ammi tayi shiru tacigaba da bada labarin cikin raunin murya.