Sashe 69
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tafa hannuwa mama takeyi tana sallallami tace, "yanzu Alhaji macece ta aikata wannan abubuwan itama akan dukiyar, kai duniya ina zaki damune?.. wannan wanne irin masiface da bala'i, kadaukarwa kanka hakkin mutane saboda wani banzan burinka na duniya" "Gaskiya matarnan tacika shu'uma, kuma makira, Allah wadaran halinta" cewar nafisa. Maryam da aliya kuwa suman zaune sukayi dajin abunda mommy ta aikata, yanzu sungano dalilin dayasa mommy bata gida. Rungume Aunty ammi tayi ajikinta tana hawaye tace, "nagode sosai da yanda kika kula da ɗana, kika tsaya tsayin daka wajen ganin rayuwarsa ta inganta, Allah yasaka da alkhairi." kara rungume ta, Aunty tayi itama ajikinta tace. "Babu komai ai yiwa kaine, kuma Ni haryanzu Muhammad, kallon ɗana nake masa, babu abunda yacanza." sakin Aunty ammi tayi tana murmushi tace, "bazan gaji da miki godiyaba, Allah yaraya miki zuri'a ya kare gabanki da bayanki" "ameen" kallon Maryam ammi tayi, tundaga kallon farko data mata, taji kaunar yarinyar tashiga ranta. yarinyar ta burgeta ga nutsuwa a tattare da ita. yanzu kuma dataji abunda tayiwa ɗanta setaji kaunar tata ta karu aranta. "Zonan diyata yar albarka" ammi tacewa Maryam. A hankali ta mike cikin matukar sanyin jiki, ta nufi gurin ammi. rungumeta ammin tayi ajikinta, tana saka mata albarka, lokaci daya Maryam taji kaunar matar ta shiga ranta. Duban Zuhura mama tayi tace. "Zuhura, kije kidakko Abul mana magriba ta gabato." "Toh, mama" zuhura ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta mike tashiga wani daki ta dakko ɗanta, mesuna Nasir amma ana masa lakabi da Abul. Jaririne dan befi wata uku ba. Sosai su mama suka jimanta halin mommy, dana yayyin baban Mustapha, ga kuma mamakin yanda Allah, yasakawa dukiyar Mustapha albarka. Ammi ma tayi mamaki sosai, dataji wai dukiyar Mustapha ce, tazama haka, gashi Allah yasa mata albarka, mutane da dama sun amfana da ita. duban daddy tayi tace. "Yanzu ina matar taka, inason ganinta itama namata godiya, ko bakomai ta rikemun yarona, bazan gazaba zanta mata addu'ar shiriya, Allah yasa tatuba takoma ga Allah" kasa kawai daddy yayi da kansa yana jinjina kyawun hali irinna ammi, duk abunda akace mommy tayiwa yaronta amma bata zagetaba, kota aibatataba se fatan shiriyama data mata. kallon Mustapha wanda yayi shiru tamkar baya falon daddy yayi yakira sunansa. "Son!" A hankali ya juyo lumsheshshun idanunsa ya kalli daddy, tare da motsa labbansa ya amsa masa. "Ina son sanar dakai wani abune, duk da nasan namaka karfa_karfa a cikin rayuwarka, amma inafatan zaka yafeni kakuma fahimci manufata" kallon daddy kawai Mustapha yakeyi amma be fuskanci meyake nufiba. fahimtar hakan daddy yayi. a gogon hannunsa ya kalla a karo na biyu. dagowa yayi yadubi kowa sannan yace. "Lokaci na kurewa, gashi a yau nakeson mukoma Kano, amma akwai abu guda daya danakeson sanar daku. A ranar da Mustapha ya warke daga ciwon dayayi, naje masallaci bayan an idar da Sallah nasamu liman mukayi magana akan wata bukatata,liman ya amincemun. batare da wani bata lokaciba nasa aka daura auren *MUSTAPHA da MARYAM* ni nayi waliccin mustapha,liman yayi na Maryam, tsirarun mutanen dasuka rage a masallaci suka zamto shaida"...........✍️
*By*
*zeey kumurya*
*4️⃣9️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
..........A razane Maryam ta dago ta kalli daddy zuciyarta na tsananta bugu tamkar zata faso kirjinta ta fito. gabadaya yawun bakinta kafewa yayi,kallon daddy take a matukar razane, kana ganinta kasan a matukar rude take dajin al'amarin. shiko mustapha lumshe idonsa yayi cikin yanayin da baze misaltuba. cikin tsananin farin ciki ammi tace. "Kaii, Masha Allah Alhaji, Allah yasanya albarka Allah yasa hadinnan yazame mana alkhairi, kai Masha Allah, amma naji dadi sosai Ubangiji ya tabbatar da alkhairi yabasu zaman lafiya da zuri'a dayyiba" "Ameen" Aunty ma kallon daddy kawai takeyi cike da dunbin mamakinsa bata taɓa tunanin abunda ze fadaba, kenan. amma kuma taji dadin wannan hadin da yayi sosai, dama kalar matar data dace da Mustapha'n kenan ba kalar su suhalat ba. tasan Maryam bazata taɓa bawa daddy kunyaba da yardar Allah. Aliya kam se murmushi take saki, najin dadi dakuma na shakiyanci ganin yanda Maryam duk tabi ta firgice. gashi kuma sun bala'in dacewa seyanzuma take ganin haka. sotake su hada ido da Maryam,amma ta sunkuyar dakanta. Maryam Sarkin kuka, se hawaye takeyi tarasa na farinciki ne, kona me?... gashi dai zuciyarta ta jima da kamuwa da kaunarsa, amma kuma hada aurensu da dady yayi yazo mata a wani irin yanayi na fargaba da tsoro. Daddy kam, nazarin Maryam kawai yakeyi yasan ya mata katsalandan acikin rayuwarta, shikansa yasan be kyauta mataba. besaniba kotana da wanda takeso. Amma shi yanada dalilin dayasa ya aura mata Mustapha'n, kuma yana fatan aurennasu yazamo musu alkhairi gabadayansu. cikin sanyin murya me nuni da rarrashin wanda akewa maganar daddy yafara mata magana. "Maryam! Bansan da kalmomin dazanyi amfani dasu gurin baki hakuriba akan wannan auren dana miki batare da yardarkiba, a matsayina na wanda bakomai bane a gurinki, amma duk da haka lokaci bekure mikiba, idan har kinga zaki cutu, kokuma kina ganin natauye miki wani hakki na rayuwar ki, karkiji komai ko wani nauyi ko kunya, tunda rayuwarkice. kifadamun idan bakyason aurennan, kamar yadda nasa aka daura yanzu senasa a warwaresa." Ajiyar zuciya nasauke, kaina na kasa bandagoba. kukan dake kokarin kufcemun na danne nace. "Babu komai daddy, aikaima ka isa dani, insha Allahu zanmaka biyayya gwargwadon iyawata bazan baka kunyaba" daga haka nayi shiru a raina ina fadin, "tayaya zan yarda a warware wannan auren da....." "Masha Allah, haka nakeson ji Allah yamiki albarka, yabaki yaya masu biyayya kamar yanda kikamun" daddy yakatsemun tunani da fadin haka. Addu'a sosai daddy yaita kwararawa mustapha da Maryam. kowa nagurin sesawa auren albarka yakeyi. nikuwa nayi shiru ina saurarensu jinakeyi tamkar mafarki nake zan farka wani lokaci. sonake na kalli fuskar gogannawa naga a wanne yanayi yake ciki amma nakasa. Ammi ko se kara rungumeni take ajikinta. Mustapha kuwa ko kwakkwaran motsi beyiba, miskilancinsa kuwa baze bari kagane yanayin dayake cikiba game da maganar aurannashi.....