← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 128

Sashe 18

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turus zannurain ya tsaya bayan yafito daga toilet din,ganin babu maryam adakin, ga shara ta fara kuma bata karasaba. Cikin dacin rai ya fita domin ganin iskancin daya hanata karasa masa gyaran dakin,ga toilet dinma bata wankeshiba. A falon kasa yaci karo da yaya sadiq,daya shigo part din,zagaye shi yayi yana kokarin fita sadiq ya rukosa. Tsayawa yayi batare daya juyoba, "kama dena wani sauri,kana tafiya fuuu kamar zaka tashi sama,nasan mekake shirinyi,toni nace ta koma,ka gyara dakin da kanka,kokuma Wanda suka saba gyara maka su gyarama,aidama ita banda gyaran dakinku aka dauketa aiki a gidannan,danhaka daga yau karka kara sata gyaran daki,nafada maka,kuma karka kuskura kace zaka mata wani abun!" Yakarasa zancen dadan daga murya, zannurain bashi dadamar musawa sadiq abunda yace,domin duk fitsararsu basayiwa yayyensu,dan daddy bebasu wannan tarbiyyarba,ga kuma oga kwata_kwata mustapha yanajin labarin kayiwa nagaba dakai rashin kunya seya sabarmaka. Juyawa yayi,yakoma sama yana kunkuni aransa amma bece komaiba........

Seda gabana yafadi danashiga falo,ganin suhailat kwance akan cinyar mommy ita kuma mommy tana waya,ni indai ba tsautsayiba bana kaunar abunda zehadani da suhailat. Sallama nayi batako kalkeniba balle ta amsamun,mommy cema kawai tadagamun hannu tana bina da kallon dabana ganemasa, narasa meyasa indai muna guri daya duk dagowar dazanyi senaga mommy tana bina da wani irin kallo,araina nakance ko dabi'arta kenan kalllon mutane oho,danni kallonnata yafara isata. Dakina nashige.

Mommy bayan tagama wayar datakeyi ta shafa kan suhailat Wanda ko dankwali babu,tana fadin, "yadai daughter naga kamar ranki abace,meke damarmunkene.?" Cikin tabara tace, "mum, yayanefa daga naje part dinsa dazu yayitamun fada yanamun tsawa,karshema koroni yayi wai duk akan kamal yazo gidannan,kuma nafada masa abokin karatunane" murmushi mommy tayi tace, "aidama nasani,toki kwantar da hankalinki kidena damuwa bari nakirasa awaya nabashi hakuri" "yawwa mommy ta thanks" pick mommy tamata agoshi. ta dakko wayarta ta yi diarling number shi, har 2 missed call tamasa amma bedagaba. "Kinga daughter, beyi picking call dinba,amma mubari zuwa later idanma bekiraniba senaje har part dinnasa,natausheshi" "tom shikenan mum,bari naje na kwanta bacci nakeji" suhailat ta fadi haka tana tashi daga jikin mommy. "Ohk daughter sekin tashi"......

Bayan sallar sala'ar ina toilet ina wanke kayan dana cire naji,ana knocking kofar dakina,tsane hannuna nayi na dauraye na fito na bude. Daya daga cikin masu aikin gidan ce, gaisawa mukayi tacemun infito falo hajiya tana nemana. Amsa mata nayi nakoma na dakko hijabina nasaka,ina mamakin mommy,yanda idan tana nemana bazata iya zuwa takiraniba da kanta, dukda muna part daya,sedai ta turo wasu dasukecan da nisa,aganina ai wannan wahalace. Da sallama abakina na karasa falon,ina bin bakin masu kamala dake falon da kallo. Wata dattijuwace,sekuma wata yar budurwa dako zata girmemun kadanne. Tsugunnawa nayi na gaishe da dattijuwar cikin ladabi, ta amsamun fuskarta dauke da fara'a,ita kuwa matashiyar se kallona takeyi. Sannu namata,amsawa tayi ta kara da fadin, "aunty,kinga nasaki baki se kallonta nakeyi,naganta kyakkyawa masha Allah,mommy ina kika samu wannan me aikin kyakkyawa da ita,gata kuma......"kai aliya badai danbanzan surutuba,daga ganin yarmutane zaki fara cikata da surutu." Wadda sukazo taren ta fadi haka,da alama kuma mahaifiyartace saboda tsananin kamar dasukeyi. Nidai murmushi kawai nayi,mommy ma murmushin tayi tana kallona. "Maryam baki mukayi,kije kihado musu abinci" cewar mommy tana mikewa. Cikin ladabi na amsa mata ina tashi. "Bari inzo intayaki" cewar budurwar itama tana mikewa,Murmushi nakara mata akaro na biyu. Tare muka Shiga kitchen din, muka hado kayan muka jera akan dinning, mamakinta ya cikani,daga ganinta itama daga gidan kudi ta fito,amma jibi yanda takemun babu kyama kokuma nuna banbanci,ashe dai masu kudin akwai masu kirki. dakina na koma,bayan mun kammala. "Gaskiya aunty me aikin gidan daddy menasara,ta burgeni zanso ta zama frnd dita,bari nagama cin abincin nan naje musha hira." cewar aliya tana kokarin kai abinci baki. Harararta aunty tayi tace, "zadai kije cikata da shegen surutunnan naki, Mara kan gado,to itadai kinga yanda take, daga ganinta bameson hayaniya bace,karkije ki takura mata."

Tura baki gaba,Aliya tayi tafara cin abinta. (Hajiya saudart kanwar alh menarasace,uwarsu daya ubansu daya,dama su uku iyayensu suka haifa,daga alh menasara,se baban suhailat sekuma auta hajiya saudart,wadda suke kiranta da aunty. ) ita kanta aunty,maryam ta burgeta, gani daya data mata tagane yarinyar tana da nutsuwa, da hankali. ina cikin shanya kayana najitashigo dakin da sallama,dama abude nabar kofar. Har bakin toilet din takaraso rike haba tayi tace, "sannunki da aiki, dakanki kike wankin,bada masu wanki agidanba kidinga basu mana" "ai wankin babu yawa,kayan dana cirenefa" "lallai agaisheki,nikuwa kinganninan na tsani wanki da wanke wanke arayuwata." Murmurshi na mata kawai,ina mopping toilet din bayan nagama shanyar. Aliya bata damu da shirun da maryam tamataba, tace. "Nikuma. Maryam aunty suhailat tananan tunda mukazo banji duriyartaba" "tananandai dazuma kafin kuzo tana falo,ammadai yanzu bansaniba kota fita" nabata amsa ina fitowa daga toilet din. Zama mukayi abakin gado,tabe baki aliya tayi tace, "hmmm,kilanma tana jinmu taki fitowa,shiyasafa dakyar na biyo aunty gidannan, saboda kwata_kwata bama shiri da ita, kingadai babanta da auntynmu uwarsu daya ubansu daya,amma seta dinga daddaga mun kai,gata da masifa,amma ina zuwa naganki senaji dadi dannasamu abokiyar hira." Dariya nayi danyadda take magana ta matukar bani dariya,"wow kinga yadda kika kara kyau kuwa,dakikayi dariyar nan,ga dimples dinki sunkara lotsawa,dama nice ke." Murmushi kawai namata, nace. "Kemafa kyakkyawace amma.kindage seyabon kyauna kikeyi" "hmm,mekyau inda babu kyawawa irinkuba." nanma murmusawa kawai nayi.Hira tashiga yimun tana bani labarai, harta fadamun daga kaduna suke,tanata bani labarin kawayenta dana school, lokaci daya naji tashiga raina, baburuwanta gaskiya, tamkar wadda muka Dade da sanin juna, nalura daga ganinta bazatayi wulakanciba,bata duba matsayina agidanba,tasaki jikinta dani tanatamun hira,nima naji dadin haka,kobakomai zata debemun kewa kafin suntafi.......

*___________________*
*MUSTAPHA*
*___________________*

Har sallar azhar yanata faman aiki, sallah ce tasheshi dama kuma ya kammala, abunda yakeyi. Yunwace yaji tana nukurkusarsa,dinning ya nufa inda maryam tajere masa abinci, yahada tea yasha sannan yatsakuri sauran kayan break din,dahar time din dazafinsu basuyi sanyiba,saboda flaks din dasuke ciki masu rikon zafine sosai, yaci. Sedayaje sallah yadawo sannan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, Wanda suka matukar yimasa kyau. Direbansa yakira,yazo ya daukesa zuwa kamfanin dayake aiki,domin yanason yaduba wasu ayyukane. Time din da mommy takirashima yanacan,shiyasa beyi picking call dintaba, sedaga baya yaga missed call dinta,text ya turamata,akan yaje office ne,yana sauri shiyasa beshigo yamata sallamaba sedai idan yadawo. Dama ka'idane kullum idan yadawo daga sallar asuba,baya komawa part dinsa seya fara zuwa yagaida mommy,yaga kuma yatatashi,sannan yakoma part dinsa. Yanaganin text din da suhailat ta masa kala_kala naban hakuri,karantawa kawai yayi amma bemata reply ba. Shifa Sam bayajin son suhailat aransa,bayan na yan'uwantaka, saboda shi sam bakalar macen dayakeso bace suhailat. Suhailat tanada rawar kai,da hayaniya. Shikuma yafison mace silent Mara hayaniya. Kawai yana tausayin suhailat ne yanda take tsananin sonsa, shiya shima yake nunamata yana sonta, kuma sannan iyayensuma suna farin ciki da soyayyartasu. A'da Sometimes yana tunanin anya kuwa yanada lafiya,kamar kowanne namiji, saboda bayajin wani feeling kokadan ajikinsa, amma kuma segashi yanzu harciwo feeling yake samasa,tundaga ranar da accident yahadasu da yarinyar dabesan ina zegantaba, gashi asanadiyyarta komai nasa yana kokarin canzawa,danma yadage da shan magunguna yanzu, dabesan halin dazeshigaba. Watsar da tunanin komai yayi daga ransa yacigaba da abunda yakawosa. Se kusan magriba yabaro office din,sanda ya shigo gida ana kiraye_kirayen sallar magriba, beko shiga cikin gidanba,ya nufi masallaci.

Part din mommy yanufa bayan an idar da sallah,shida sauran yan'uwansa dasuka hadu a masallaci. Babu kowa a falon duk suna daki, aunty ce tafito daga dakin dake jikin na mommy,Wanda ana take sauka idan tazo gidan. Da mamaki mustapha yake kallonta,danbesan tazoba. Shikuma su sadiq sunsan tazo harsun gaisama. Fadada fara'a aunty tayi tace, "sannunka boy seyanzu kadawo kenan agogo sarkin aiki,tunda nazo nake cikiyarka aunty atika tacemun katafi office, kai weekend dinma bazaka hutaba" shagawabe fuska yayi yace, "wai auntynah haryanzu boy dinnan baze fita daga bakinkiba, nifa bansan sunan" karasawa aunty tayi kusa dashi ta kamo hannunsa tana fadin, "sorry my son,nariga nasabane,zomuje kazauna kahuta dannasan ka kwaso gajiya" su haidar kuwa dasuke kallonsu se guntse dariya sukeyi, indai aunty tazo gidan seta tsokanesa tace masa boy, saboda dayana yaro haka akecemasa,daya girmane yayi cancel din sunan. Zama sukayi akan kujera,yana gaisheta. Aunty macece,me kirki da saukin hali,gashi tana jansu ajiki,musammanma mustapha, haka kawai takejin wani Abu agame dashi me kamar tausayi,Wanda batasan dalilin hakanba. Mommy ce tadawo falon itama. Daga baya kuma suhailat tashigo, se satar kallon mustapha takeyi, shikuma daga gaisuwar daya amsa mata,bekara mata maganaba, cigaba da hirarsu sukayi da aunty.

Adakina mukayi sallah,da muka idarma hira Aliya tacigaba damun, araina mamakinta kawai nakeyi yanda bata gajiya da magana,gaskiya Allah yahore mata baiwar surutu. Aunty ce dakanta tashigo dakin da sallama, amsa mata mukayi ta Dora da fadin, "sannu Aliya,kinzo kincikata da surutu, narasa irinki aliya kogajiya da magana bakyayi" murmushi nayi nace, "babu komai aunty hirafa mukeyi" "kai aunty, nifa bani da surutu,kawaidai banaso inga nazauna shirune" "naji nidai,kitaso kigaisa da yan'uwanki kowa ya hallara afalo." Zunbur aliya ta mike tayi bakin kofa, nikuma ina zaune ko motsawa banyiba. Juyowa aliya tayi tana kallona, "kitaso muje mana tare maryam" "A'a aliya kije kawai zanfito anjima" takuramun aliya tayi,dole na mike muka fita tare. dashi nafarayin tozali,hakan yahaddasamun wata faduwar gaba,bantaba ganinshi yana murmushi ba seyau naga yanayiwa aunty,dimples dinsa duka kumatu biyu sun lotsa abun sha'awa,akodayaushe idan na kallesa karamun kyau yakeyi,yanzumma hakance ta kasance. "Oyoyo yaya.....muryar aliya ta katsemun tunani, sekuma naji itama tayi shiru,kallonta nayi naga ta wani nutsu harta da tafiyartama ta canza. Dariya naga su yaya sadiq sunsaka mata,ashesu sunsan dawar garin, ganin mustapha ne yasata nutsuwa ba jiri,ta wani koma salihar gaske,dantasan halinsa farinsani. Shikuwa ya wani tsare gida, yana latsa waya. Akasa muka zauna,kusa da aunty muka gaishesu.
Chapter 18 · 0% Book details