← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 128

Sashe 40

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su aunty suna bakin gurin atsaitsaye cikin karayar zuci, su haidarma se kuka suke, ga yaya ba lafiya ga mommy ma ta fadi,abun gwanin ban tausayi. Fiye da awa daya likitoci suna kan mustapha, har wani babban likitane yazo daban mesuna Dr, jibril. Karshema su aunty gani sukayi anfito dashi akan gadon tura marasa lafiya an nufi wani dakin daban dashi. Cikin tashin hankali su aunty sukabi bayansu dukansu, amma kafin su karasa har sun shige dashi dakin sun rufo. Hankalinsufa ya kara tashi, suka kara gigicewa. Se bayan magriba likitocin suka fito suna share gumi, dakyar suka samu numfashin mustapha yadawo ahakanma seda suka samasa oxygen, su Kansu likitocin ciwon mustapha ya tsoratar dasu yakeyi, gashi sunkasa gano takameman meke damunshi, sun masa gwajin jini, sundau hoton zuciyarsa, har gwajin kwakwalwa sun masa amma babu abunda suke gani na sakamakon wani ciwo nadamunsa. Abunda yake kara tsoratar dasu zafin da jikinsa yakeyi. Gabadaya su aunty sukayi kansu da tambayarsu ya jikinnasa, Dr, jibril ne yace musu subari suje suyi sallah su dawo, sesu musu bayani. Suma su sadiq din aunty cewa tayi suje suyi sallar, itama tatada tata agurin dama da alwalarta ta sallar la'asar. Suhailat kuwa tana zaune fuskarnan tayi jajur saboda kuka, wai ita batayin sallar. koda su yaya sadiq suka idar da sallah suka fito daga masallacin dake asibitin daddy yakirasa yasanarmasa yakaraso yana airport yazo ya daukesa. Shida zannurain suka tafi dakkonsa haidar da faruq kuma suka koma ciki. Aunty da suhailat na dakin mommy daketa bacci azaune, sunyi jigum_jigum. ahaka su haidar suka shigo suka samesu. Ahankali mommy ta bude idonta tana karewa dakin kallo, zumbur kuma ta mike zaune tana kokarin sakkowa,dasauri aunty da suhailat sukayi kanta suka riketa. Rungumeta suhailat tayi ajikinta tana fashewa da kuka. "Saudart, ina my son, yamutu ko, dan Allah karkicemun ya mutu" mommy ta fadi haka tana haki. Aunty bata,bata amsaba seda tajinginata da filon dake kan gadon sannan tace, "be mutuba aunty atika,amma suncanza masa daki kuma sunki barinmu shiga,amma babban likitan yace zasuje suyi sallah seyazo ya mana bayanin abunda kedamunsa" lumshe ido kawai mommy tayi batace komaiba. Mikewa aunty tayi domin sanarwada Dr,mommy ta farfado. a tare sukadawo dakin dawata nurse mace, sannu tayiwa mommy tare da tambayarta jikinta, dakai kawai mommy ta amsa mata. Duddubata takarayi ta fice. Su haidarma sannu sukayiwa mommy suka sanarmata isowar daddy. Agigice daddy yakaraso cikin asibitin, su sadiq na biye dashi abaya. dakin da sadiq yanuna masa mustapha yana ciki yanufa direct da nufin shiga,amma Dr jibril yatsaidashi. Tsayawa daddy yayi yana kallon Dr. Hannu Dr, yamikawa daddy sukayi musabaha yakara da fadin. "Ranka yadade, barka da wannan lokacin dafatan ka sauka lafiya" "lafiya kalau" daddy ya bashi amsa akagauce.danya matsu yaji meke damun dannasa. Fahimtar hakan da Dr, yayi seyace. "Idan babu damuwa,mu shiga nan dakin namuku bayanin gabadaya dan bayanin bazeyiyu atsayeba" yakarashe zancen da nuna dakin da mommy take ciki. dakin suka nufa gabadayansu. Mommy tana ganin daddy, takara rikecewa,itadai abarta taje taga danta. Karasawa kusa da ita daddy yayi cikin rarrashi yace, "kikara hakuri, atika insha Allahu zaki gansa anjima." Cikin kuka mommy tace, "daddy danbaka halinda my son yake cibane, bafaya numfashi...." lallaba mommy daddy yahauyi, dukda shima dauriya kawai yakeyi, amma zuciyarsa kwadayin ganin dansa kawai takeyi. bayan mommy tayi shiru, suka maida hankalinsu duka akan Dr dominjin mezece. Gyara murya Dr,yayi yafara magana yana duban daddy. "Ranka yadade, azahirin gaskiya munkasa gano takamaimen ciwon dake damun yaronka, munyi iya gwaje_gwajenmu akan duk abunda muke zargin ze iya haifar masa da wannan ciwon, amma result din dai baya bamu da wani ciwo ajikinsa. " haba doctor duk halin da dana yake ciki, amma kace kunkasa gano ciwon dake damunsa gaskiya Dr, nalura kamar bakusan aikinkuba, nidai Ku sallamemu kawai mucanza wani asibitin, kokuma mu fita dashi waje." Cewar mommy cikin zafin zuciya. Duban mommy Dr, yayi yace. "Hajiya bahaka bane, tun safe likitocinnan suke kansafa, ganin sun kasa gano mekedamunsa suka kirani. Ni'inama tsaka da aiki suka kirani, dabama zanzoba seda suka sanarmun yaronkune dakuma halin dayake ciki, haka na katse komai danakeyi nataho. ina zuwa ko zama banyiba nadukufa akan dubasa,amma haryanzu danake muku bayaninnan bamu gano meke damunsaba. amma ina ganin ta bakin naki zamubi, afitar dashi wajen kawai,su zasufimu gano mekedamunsa. Numfasawa aunty tayi tace, "bantari numfashinkaba doctor amma ni ayanda naga jikin mustapha dakuma bayananku kamar ba ciwon asibitine kedamunsaba, ina ganin kawai mukoma gida ayi masa na hausa." "Wanne irin na hausa kuma, mekike nufin yana damun yarona, nidai babu maganin hausan daza'ayiwa dana, kawai a fitarmun dashi waje aduba lafiyarsa." Mommy tafadi haka cikin hayayyakowa. Gyada kai doctor yayi yana kallon aunty yace, "tabbas abunda kika fada hajiya gaskiyane. Don muna samun irin wannan case din, na irin wadannan ciwukan da'ake rasa kansu dadama. Amma daga ankoma gida anyi nahausa sekaga andace idan Allah yaso. Ni likitane danasan aikina,amma idan zakuyi amfani da shawarata, ku koma dashi gida Ku nemar masa maganin hausa, idanma fitar dashidin zakuyi to kukaishi kasa me tsarki. (saudiya) domin gaskiya bana tantama ciwon dake damun mustapha bana asibiti bane, kodan wani irin zafi da jikinsa yakeyi........✍️

*AYI HAKURI DA TYPING ERROW BA EDITING NE*

*By*
*zeey kumurya*
*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

*Bismillahirrahmanirrahim*

*3️⃣1️⃣*

...........Nidai gaskiya doctor dana bazan masa maganin hausaba,kawai Ku sallamemu yanzu mucanza asibiti kafin safiya muyi shirin fita dashi waje,tunda Ku kunkasa gano abunda kedamunsa." Mommy ta fadi haka tana batarai. Kallonta aunty tayi yanda take hakikancewa tana magana tamkar ba ita tagama lagwai_lagwai dazuba. Daddy da tunda aka fara maganar bece komaiba seyanzu ya numfasa yana duban doctor yace, "amma doctor mekake tunanin yana damunshi,kokuma yake kawo irin wannan ciwon haka." "Agaskiya alh,a yanzu dai bazance gashiba amma su masu maganin idan kukaje gurinsu zasu sanar muku da yardar Allah,yanzudai Ku barshi anan zuwa safiya mukara ganin abunda Allah zeyi akansa, semusan abunyi." "Toh shikenan doctor mungode yanzu zamu iya zuwa muganshi" "ehh,zaku iya zuwa ba matsala,amma se'akiyaye,danma naga kundamune shiyasa nabarku kuje kuganshi,amma aka'ida babu meshiga gurinsa,ayanzu. "ohk,insha Allah zamu kiyaye Dr." musabaha daddy sukayi da doctor yamusu sallama ya fice. Babu bata lokaci suma su daddy suka mike dukansu suka nufi dakin da mustapha yake. Yanayin dasuka ganshi bakaramin kara firgita daddy yayiba,gashinandai akwance shiba rayuwaba shiba mutuwaba, tambayoyi daddy yafara yiwa mommy akan ko abu yasamesa jiya kafin ya kwanta,kokuma yace mata wani guri najikinsa na masa ciwo, mommy tace babu komai lafiya kalau suka rabu. jikin daddy gabadaya yayi sanyi da ciwon mustapha, harya fara tunanin ko ciwon ajali ne yakama mustaphan dan haka yake shima arasa meke damun mutum. Addu'a kawai daddy yashiga yimasa acikin ransa akan Allah yabashi lafiya....

Yinin yau gabadaya cikin rashin nutsuwa nakarasashi, nayi tunanin duk hanyar dazanbi dazan iya zuwa naga yaya mustapha a yau amma bansamuba. Gashi banason na kira yaya sadiq akan inason zuwa, yayi tunanin wani abu daban,zama nayi naita tunane_tunane har akayi sallar magriba. Dakyar na iya tashi nayi sallah, sannan na dafa indomie guda daya,na watsawa cikina dan kar yunwa tamun illa. Ganin duhun dare yayi se tsoro yakamani ni kadai a part din. kamar daga sama naji tunanin abunda yafaru dani ranarnan yadawo cikin kwanyata, tiryen tiryen kamar yanzu abun yake faruwa. wani matsanancin tsorone yakamani, cikin sauri na mike na dauki wayata nafice daga part din gabadaya bayan na janyo duka kofofin part din na rufe. Part din su baba talatu nanufa,ina tafe ina tunanin abunda yafarun a kokarina nasan tuno wanene yazo da niyyar ketamun haddi, duka dai yayan gidan nasan muryoyinsu harma da megidan, kuma Wanda yazomun dindai yayi magana, "tokodai yaya faruq ne?" natambayi kaina, domin shine tunda nazo gidannan, jin muryarsa danayi befi a kirgaba. zato zunubi hakan yasani yin istigfari tare dayin addu'ar koma waye Allah yakareni daga mugun nufinsa. koda naje part din su baba talatu naji sunata zancen ciwon mustaphan, dayake drivern dayakai su mommy asibiti akwai matarsa acikin ma'aikatan gidan agurinsa ta jiyo musu. Nidai dakin baaba talatu nashige na kwanta bayan mungaisa dasu. zuciyata sam babu dadi, namarasa meyake damuna ahalin yanzu. Karatun kur'ani me girma na kunna awayata inaji ko zuciyata zata samu sukuni.......

Acan asibiti kuwa tuburewa mommy tayi ita se'ancanzawa mustapha asibiti tunda nandin sunkasa aiwatar da komai. Hakuri daddy da aunty suka shiga bata tare da nuna mata, itafa lafiya ba likitoci ke bada itaba, Allah ne yake badawa a lokacin dayaso. Dakyar mommy ta hakura akan su kwana a asibitin zuwa safiya se'asan abunyi kamar yadda doctor yafada. Bayan sallar isha'i daddy yacewa dasu sadiq sukoma gida hakannan dasafe sazo, mommy kam dama anan zata kwana, suhailat ma daddy yace tabiyo su yaya sadiq amma tace, Sam itama a asibitin zata kwana, haka daddy yace abarta ta kwanan. Aunty kuwa harta mike zata tafi, daddy yace ta zauna itama ta Kwana,tace masa ai anyi yawa amma yace ta kwanandai danyaga tafi mommy hayyaci. shima zuwa anjima ze koma gida idan sungama tattaunawa da doctor. Adakin baba talatu nayi sallar isha'i, abinci ta zubo ta kawomun nace mata nakoshi naci abinci kafin na fito. Takuramun tayi naci kadan danma naji dadin zuciyata danaji karatun. Harna kwanta yaya sadiq yakirani, yacemun ina ina, nacemasa ina part din su baaba talatu, yacemun meyasa bazan kwana a part dinmuba, nace masa tsoro nakeji nikadai. Wai ni raguwace banda haka mene abun tsoro nadawo nan na kwanta, nace masa wlh bazan iyaba. Badan yasoba ayanda na fuskanta ya hakura ya barni na kwanan anan. sanarmun yayi yadawo gida zedebarwa su mommy kayane yakaimusu seya dawo, kamar nace masa zan bisa sekuma naji becemunba nima senayi shiru, amma yasha tambaya aguna akan yajikin yaya mustapha. nikadai adaki su baaba talatu suna falo suna hira, se juye_juye nakeyi akan katifa amma nakasa bacci. Mikewa nayi dama da alwalata nashiga jero nafilfili akan Allah yabawa *heartbeat* lafiya..........
Chapter 40 · 0% Book details