← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 128

Sashe 43

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har yau bansamu naga mustapha ba duk kuwa da matukar gwadayin ganinsa danake sonyi, yaudai nakasa hakuri seda nacewa yaya sadiq inason ganinsa dan tunda yafara ciwo banganshiba, shine yace dasafe nazo shine agurinsa sena shiga naganshi. da misalin karfe goma na safe bayan nagama aikina nanufi part dinnasa, babu kowa kuwa kamar yadda yaya sadiq yace seshi dayake kula dashi, seda najirashi a falo yagama kimtsashi sannan yafito yace nashiga naganshi. da mamaki na kalli yaya sadiq nace, "yaya nikadai zanshiga bandakai" "haba maryam,kemafa yar gidace kishiga kawai babu matsala zanyi wayane tun dazu ake kirana da ina ciki" gyada masa kai nayi. Ahankali na mike nafara tafiya zuciyata na luguden bugun datasaba aduk lokacin danayi kusanshi dashi. ahankali na murda handle din kofar dakin nashiga da sallama, dukda nasan babu me amsamun. Faduwar gaba da karuwar bugun zuciyatane suka dirarmu alokaci daya sanda nayi arba dashi kwance idanunsa a lumshe. jankafata nayi data faramun nauyi nakarasa gaban gadon ina mai kura masa ido. Jallabiyace ajikinsa wadda babu alamar datti a tattare da ita. "Ya Allah muntuba,Allah ka iya mana" nafada acikin zuciyata ina kara girmama ikon Allah, mutum me kwazo da kasaita,shine acikin wannan yanayin kwance komai sedai a masa,lallai muji tsoron Allah domin duniya abar banzace. Lumshe idona nayi ina tuno yanda yake abaya da lafayarsa amma yanzu gashi a kwance ko hannunsa baze iya dagawaba. ahankali nabude idona nasauke akan kyakkyawar fuskarsa da ita kadaice bata kumburaba ajikinsa. Hawaye ya shiga kwaranyomun a fuskata na tsananin tausayinsa, ga wani gumi dayaketa tsatstsafo masa na azabar ciwo, kawai jinayi nakai hannuna kan goshinsa ina ina share masa gumin kansa batare dana shirya yin hakanba, dukda wani zafi da huci danakeji a tafin hannunnawa amma nakasa cirewa daga goshinsa, sema kara kamasa kandanayi da danyatsuna biyu kamar yadda akeyi idan za'a kamawa me ciwon kai, kai. nafara karanto abunda ake karantawa nakamun kai acikin zuciyata, jikinane kawai yabani yanda kannannasa yake zuba uban gumi yana masa ciwo, seda na kammala karanta duk abunda ake karantawa sannan nasakar masa kannasa. Rankwafowa nayi daidai fuskarsa har ina jiyo hucin numfashinsa a fuskata,lumshe idona nayi,bugun zuciyata kuma ya karu, hannuna na rawa nakaishi daidai bakinsa naraba kananun lips dinsa nasama dana kasa, nafara karanto ayoyin rokiyya a fili yana shigarsa tacikin kunnensa kuma ina tofawa acikin bakinsa, dan idannatsaya debo ruwa nace zantofa aciki zanbatawa kaina lokacine, kuma yaya sadiq yana falo yana jirana. naji abakin aunty ciwon dake damunsa ana tunanin jinnune, duk da tsananin tsoron danakeji akan abunda nake aikatawa,amma haka na daure zuciyata, nacigaba da karanto masa domin wannan shine kadai taimakon dazan iya masa,kuma nasan bazan kara samun wata damar dazan masa irin wannanba.........✍️

*kuyi manage da wannan*

*By*
*zeey kumurya*
*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

*Bismillahirrahmanirrahim*

3️⃣3️⃣

..........cikin ikon Allah harna gama karanta masa yaya sadiq bezo kiranaba kuma babu wanda yashigo,abunda ya bani mamaki kenan. Ammafa naji ajikina, dan naji jikina yayi mun wani iri kuma se rawa yakeyi, gabadaya na hada gumi ga wani mahaukacin bugu da zuciyata takemun. ahankali nakai hannuna dake karkarwa na taba goshinsa,senaji zafin jikinnasa ya ragu, se ajiyoyin zuciya naji yana saukewa akai_akai cikin baccinnasa, dauke hannuna nayi daga kannasa nima ina sauke ajiyar zuciyar. badon nasoba bakuma danna gaji da kallonsa naja jiki nafito zuwa falo, abun mamaki babu yaya sadiq babu dalilinsa, zama nayi akan kujera ina maida numfashi hannuna dafe dakaina dayake mugun saramun,wani irin shauki da kaunar yaya mustapha ne, yake kara ninkuwa araina gami da tsananin tausayinsa,daga gani base anfadaba kasan yana jin jiki,dakuma azabar ciwo, dama dazan iya dana maido da ciwonnasa jikina, wasu guntayen hawayene suka silalomun wanda bansan dalilinsuba,tabbas idan Allah yabaka lafiya yagama maka komai najin dadin rayuwa. nakai ten minutes azaune ina jiran yaya sadiq amma naji shiru bedawoba, mikewa nayi zanje naduba falon kasa koyacan, a kan steps mukacikaro da mommy,datake hawowa benen cikin sauri har bangazata tayi, bayanayi dasauri harna kusa faduwa dama jikina babu kwari sekuma narike karfen benen. "Maryam!" naji mommy takira sunana da alamun mamaki. Gabanane yayanke yafadi danbansan me mommy zatamunba intaga nikadaice agurin danta. "Na'am" na'amsa mata cikin rawar murya. "Mekike anan" cikin dauriyar abunda nakeji ajikina nace mata, "mommy nazo duba yayane, shine yaya sadiq yace injirashi zeje yadawo, kuma haryanzu bedawoba" mommy batakaramun magana sebina datayi da kallo, kasa nayi da kaina cikin faduwar gaba. "Yanzu sadiq son din yabarmun shikadai shikuma yakama gabansa" mommy ta fadi haka cike da bacin rai" batajira mezanceba ta raba tagefena tahaye saman. wata nannauyar ajiyar zuciya nasauke ina bin bayanta da kallo, "yanzu da'ace ina dakin mommy tazo tasameni mezance inayiwa danta,nagodewa Allah daseda nafito ita kuma tazo. Karasa sauka nayi nafice daga part din,banga yaya sadiq ba harna karasa part dinmu. Dakina nashige na kwanta akan gado,kaina na juyamun,addu'a nashiga karantowa acikin zuciyata har baccin wahala yadaukeni.

Cikin baccina naji ana kiran sunana tare da tabani, ahankali na bude idona dasuka sauya kala saboda bacci, nace. "Uhm" muryar aunty naji tana fadin, "maryam, kitashi kiyi sallah baccin ya isa haka, har 2 tawuce fa" mikewa nayi zaune cike da mamakin dadewar danayi ina baccin ina yar mika nace, "aunty har 2 fa tawuce kikace banmasan nadade hakaba" "aitun dazu nashigo naga kina tashan bacci,nima baccinnayi banjima da tashiba" "bari naje nayi sallah aunty" nafadi haka ina sauka daga kangadon har yanzu idona begama budewaba kamarma inkoma baccin haka nakeji" bakina na wanke na dauro alwala nafito nayi sallah, har lokacin aunty tana kishingide akan gadona tana danna waya. bayan na idar aunty tadubeni tana murmushi tace, "kinjini da mutuniyar taki, wai yaushe zandawo kokuma ita tabiyoni" murmushin nayi nima nace, "gaskiya dai aunty dakin taho da ita, yanzu se ita kadai agidan ko?" "Maryam makaranta shiyasa bantaho da itaba,amma jibi Friday zance yayanta yakawota seta koma ran sunday, kuma bata gidama tana gidan kanwar abbansu dayake bamu da nisa" "yawwa aunty, harnaji dadi dakikce zatazo Allah yakaimu jibin" "ameen" gyara zama nayi natambayi aunty abunda yake damuna arai dafadin"aunty yame jikin kuwa" "jiki da sauki maryam, daga gurinshi nakema nabiyo tanan,yau jikinnashi yayi kyau sosai" gyada kai nayi nace, "Allah ubangiji yakaro sauki,amma aunty meyasa ba'abashi rubutu kokuma adinga masa tofi aruwa ana shafa masa ajiki" "nima dafarko nayi wannan tunanin maryam,amma ganin malam yabashi na shafawa ajikin yasa banmaida hankali akan adinga masa hakaba, kuma shima yabada tofin ana diga masa abaki" "hakane aunty, amma ni aganina addu'a bata yawa, malaminmu na islamiyya ya turamun ayayoyin da ake karantawa na rokiyya a wayata wanda SUDAIS ne yake karantawa,kullum kafin nayi bacci sena kunna naji harna haddacema yanzu, meze hana adinga kunnamasa shima yanaji, nikuma zantofa aruwa se'abashi yasha kokuma ashafa masa ajiki." Cikin gamsuwa da bayanan maryam aunty tace,gaskiya maryam kinkawo abu me kyau,aidamu bamuyi tunanin koda karatunne adinga kunnamasaba, wannan shawarartaki tayi sosai maryam, mungode Allah yasaka da alkhairi, anjima bayan la'asar idan zani semuje tare a fara masa." "Bakomai aunty fatanmu kawai,Allah yabashi lafiya" hira mukacigaba dayi da aunty, zuciyata fess da farinciki zandinga ganin *heartbeat* kullum, kuma da izinin Allah seya samu rangawame aciwon dake damunsa dan ayar Allah bakarya bace,kuma alkur'ani warakace ga dukkan kowanne ciwo.

Kamar yadda aunty tace, dayamma mukaje na kunnamasa karatun adakinsa ita kuma takawomun ruwa a cup na tofa aka shafe masa jikinsa dashi. mommy da aunty tafada mata abunda za'adinga yiwa mustapha batace komaiba, daddy kam yayi farinciki sosai yayta sawa maryam albarka. Tundaga ranar kullum senaje namasa safe da dare,wataranma aunty tana falo nikadai take bari adakin inyi ta kallonsa. Kuma alhamdulillah jikinnasa yanasamun sassauci, dan wannan kumburin jikinnan nasa duka babu yanzu, saidaifa wani abun mamaki, duk sanda nazo nakunna masa karatun kuma akashafa masa ruwan tofin ajikinsa sejikinsa yayi sanyi kamar nakowa, amma washegari, ina kara zuwa za'a masa se'aji zafin jikinnasa yadawo zafi zau se ankuma masa yake tafiya. Su aliya sunzu sunyi kwana biyu ita da yan'uwan abbansu da yayanta,umma da saleemat ma sunzu harda gwaggo, duk sunzo dubiya, muna waya da saleemat ne nakefada mata ciwon yaya mustaphan, shine tafadawa umma, umman tace kodan kirkin sadiq zasuzo suduba yayansa,shine tayiwa gwaggo magana sukazo tare. Gwaggo anzo gidan alh.menasara hankali ya kwanta, mommy kam bata wani kulasuba daga gaisuwa shikenan, danma aunty tananan itakam ta karbesu hannu bibbiyu faran_faran.
Chapter 43 · 0% Book details