← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 128

Sashe 57

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

toilet aunty ta nufa ta watso ruwa ajikinta domin taji dadi, dan yanda takejin kanta a wannan lokacin baze misaltuba, jinta take a wata duniyar databan tsabar damuwa. Tana fitowa daga toilet din taga maryam na mutsu_mutsu alamar tatashi. Da sauri aunty ta karasa gareta ta tallafota jikinta tana kiran sunan sunanta. Memakon maryam tabata amsa se kuka data saka cikin wata wahalallaiyar murya tafara fadin, "dan Allah kumaidani gida gurin gwaggo ta, gwara na zauna agurinta akan zaman gidannan da'ake son cutar da rayuwata d...... Rufe mata baki aunty tayi, ganin haryanzu bata gama dawowa cikin nutsuwartaba, daidai lokacin daddy ya murda handle din kofar dakin bakinsa dauke da sallama, yazone domin yaduba jikin maryam din, kuma yanata knocking aunty bata jiba, kalaman maryam gabadaya akunnensa tayisu, runtse idonsa yayi cikin tsananin takaicin wai yau gidansa ake neman tsarin zama acikinsa, gaskiya atika ta gama dashi. Muryar maryam da yanda tayi maganar cikin kuka yatuno masa da muryar matar dabaze taba mantawa da itaba arayuwarsa, tamkar itace ta dawo take masa magana a yanzu. cikin sanyin jiki yakarasa cikin dakin inda sautin kukan maryam ne kawai yake tashi, aunty kuma na aikin rarrashinta. "saudart jikinnatane haryanzu" aunty dabatasan da shigowarsaba ta juyo tana kallonsa idanunta cike da kwalla tace, "inajin fa yaya haryanzu bata dawo hayyacintaba,yanzu ta farka sekuma ta fara surutai" daddy bece komaiba ya mike yanufi karamin fridge din dake dakin ya dakko ruwa a roba medan sanyi, ya tsiyaya a cup sannan yatofa addu'a yamikawa aunty yace tabawa maryam din tasha. Tallafota aunty tayi takafa mata cup din a baki, aiko Tass maryam ta shanye ruwan. "Akaro miki ruwan?" Aunty ta tambayeta. Girgiza kai tayi alamar a'a tana sauke ajiyar zuciya, taimaka mata aunty tayi ta koma ta kwanta saboda jikinta sam babu kwari. "ya Jikinnaki, yanzu inane kuma yake miki ciwo?" Aunty ta jero mata wannan tambayar. kanta dake mugun sara mata ta nunawa aunty da hannunta idanunta a lumshe, se kuma hannunta inda ta yanke da madubi. "sannu Allah yakara sauki, hannunnaki kuma bari nakira doctor yazo yaduba mikishi" gyada mata kai kawai ta iyayi. tanaso tatambayeta yajikin mustapha amma maganama wahala take mata. "Maryama, sannu kinji,Allah yakara sauki" muryar daddy ta doki kunnena, bude idona nayi da sauri najuya inda najiyo sautin muryartasa. Daga masa kai nayi shima alamun da sauki. fita daddy yayi ya zauna a falo, ya rafka tagumi yanata tunane_tunane. Aunty ce ta mike ta hadowa maryam tea mekauri, taimaka mata tayi,cikin ikon Allah kuma tasha sosai. Se'alokacin naji wata nutsuwa tafara lullubeni har gumi yana tsatstsafomun ajikina. aunty ce tataimakamun takaini toilet domin nayi wanka ko zankara jin dadin jikina. Jikina Sam babu kwari haka nadaure na watsa ruwan. ga zuciyata dakemun wani irin bugu tamkar wani abu yana shirin faruwa dani. Falo aunty tadawo gurin daddy bayan maryam tashiga wanka, zama tayi agefensa tana kallonsa yanda ya rafka uban tagumi da hannu bibbiyu. danne duk wata damuwarta tayi domin ta taushi dan'uwanta danta fuskanci yana cikin tsananin damuwa. Cikin tausasa lafazi tafara masa magana. "Yaya dan Allah kayi hakuri akan abunda yafaru mudauki komai amatsayin kaddara wadda tariga fata. kuma rubutacciya haka Allah ya kadarto mana babu yanda zamuyi." wani gwauron numfashi daddy yasauke sannan yadubi aunty Cikin raunin murya yace, "saudat zuciyata cike take da tsananin bakin cikin abunda atika tayi,yanzu ace a gidana akeyin wannan danyen aikin, amma bansaniba yanzu idan duniya taji kotasan halin da'ake ciki wanne kallo za'amun, dayawan mutanema cewa zasuyi ninakeyi dan wata bukatar kaina" "kayi hakuri dai yaya, mugodewa Allah dayasa maganar bata yaduba ita kuma aunty atika kabarta ita da Allah,shikadai yasan meze mata" "hmmm, nacanza tunani saudart zankai karar atika da sadiq ga hukuma da kaina, domin a yanke musu hukunci daidai da abunda suka aikata" da sauri aunty tadago ta dubi daddy cikin mamakinsa, shida dazu_dazu yagama cewa yabarsu da halinsu amma kuma yanzu yacanza ra'ayi. kara gyara zama aunty tayi ta fuskanceshi sosai, sannan tace. "Haba yaya yakuma zakace haka, hannunka baya taba rubewa kayanke kayar, sadiq naga nadama tsantsa a idonsa, nasan yanzu yanacan yarasa ina zesaka kansa. Kuma yanzu idan kayi kararsu katonawa mustapha asirinsa dake rufe, duniya zatasan kowaye shi. kaga mukuma bazamuso hakaba, dan Allah yaya kamar yadda kace da farko kabarsu da halinsu yanzunma kajanye batun mikasu ga hukumar." "Saudat abunda atika tayifa bakadanbane ta cutar da bayin Allah dabasujiba basu ganiba, kina ganin idan muka barsu bamuso kanmu dayaba" "yaya babu batun sankai, ayanzu koda kayi karar anti atika tanada kudin dazata iya kwatar kanta, tunda kasan shari'ar yanzu bata Allah baceba, karar anti atika da sadiq daidai yake da muntonawa kanmu asiri" shiru daddy yayi bekara cewa komaiba. Ganin haka aunty tashiga rokonsa gami da bashi baki, dan ita bazataso ayi karar su mommy, batason kowa yasan mustapha badan daddy bane. badon daddy yasoba yahakura yakuma tabbatarwa da aunty ta shirya idan anyi sallar la'asar zasu tafi Niger domin nemo dangin mustapha, kuma da maryam daza'atafi. Aunty taso fahimtar dashi hakan bamafita bane, domin idanma sunje Niger din gurinwa zasu nufa ta ina zasu fara Neman wani dangin mustapha, kuma kodama sunsan inda zasu nufa yau yayi wuri su tafin, tunda mustaphan ba ishashshiyar lafiya gareshiba. Amma daddy yace mata hakan kawai shine mafita dan mustapha yatada hankalinsa sosai. Badon tasoba ta amince. batayi kuma tunanin komaiba da daddy yace, zasu tafine tare da maryam, danko befadaba bazatabar maryam dinba dankar mommy ta cutar da ita.

Daddy bayan sungama magana da aunty direct masallacin dake manne ajikin gidansa yanufa domin ya kaddamar da abunda ya kudurcewa ransa tun a lokacin dayayi arba da maryam, yadade da kudirin aransa amma yau yayi alkawarin kafin subar kasarnan seya idda nufinsa. Kamar yadda yazata kuwa liman na zaune a masallacin shida wasu tsirarun mutane. Gaisawa sukayi da kowa cikin mutunci da sakin fuska tamkar babu abunda yake damunsa,duk da karfin haline kawai yakeyi. Gefe suka koma shida malam liman yamasa bayanin bukatarsa, yakuma tabbatarmasa da a yanzu yakeson ayi. Sauran mutanen dake masallacin malam liman yahado kansu atake agurin aka daura auren da daddy yabukata akan sadaki naira dubu hamsin wanda daddynne yabada. Malam liman ne yayi waliccin amarya daddy kuma na ango.(To Allah yasanya albarka a auran, yabada zaman lafiya me dorewa, tunda daddy bebari naji daurin auren konasu wayeba😜)....

Ina fitowa daga toilet natarar aunty ta kwasomun kayan dazansa daga dakina. Amma ita bata dakin. murmushi nayi nadauki kayan nafara sawa, zuciyata cike da kaunar aunty, yanda take nunamun kulawa ko yar cikinta sehaka. Tunanin yaya sadiq ne yafadomun acikin raina, haka kawai naji gabana yayanke yafadi dana tunasan. nasan yanzu yanata nemana a waya besameniba, amma idan aunty tashigo zance ta aramun wayarta na kirasa. kayan kawai nasaka nafito falo domin naje nagaishe da mommy, aunty nagani tafito daga kitchen hannunta dauke da plate da cokali. "Sannu aunty" "yawwa maryam, yajikinnaki?" "Dasauki aunty" "Allah yakara sauki, kizo kici indomie dinnan kenadafawa sekisha magani, zamuyi wata tafiyane yanzu, nakira doctorn ma yacemun gashinan zuwa" da mamaki nake kallon aunty cikin sanyin murya nace mata. "Aunty tafiya kuma, ina zamu?" "nima dai bansaniba maryam haka dai yaya yacemun, sekiyi sauri kici abincin munayin sallah zamu tafi" cewar aunty tana ajiye mun plate din akasa. "To aunty bari naje nagaida mommy, yau antofawa yaya addu'ar kuwa?" kallona aunty tayi sannan tace, "kici abincinki kawai anti atika batanan, shikuma mustapha jikinsa yayi sauki sosai, alhamdulillah" ajiyar zuciya nasauke aboye tajin dadin aunty tace, jikin heartbeat dina yayi sauki. Zama nayi akan carpet na bude
plate din da aunty takawomun nafara cusa indomien badon inajin dadintaba, saboda yanda zuciyata take bugawa inajin tamkar wani bakon al'amari nashirin faruwa dani ayau...........✍️

*kuyi hakuri da typing error, yauma babu editing*

*By*
*zeey kumurya*
*ABUNDA KASHUKA....*
_*(shizaka girba)*_

*4️⃣0️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

..........Abangaren su faruq kuwa, gabadaya part dinsu suka nufa zuciyoyinsu babu dadi, kowa dakinsa yashige ya kullo kofa domin samun kadaita. sadiq da nadama gami da kunya suka masa katutu yakasa zaune yakasa tsaye zarya kawai yakeyi a dakinsa abubuwa biyu ne suke damunsa a wannan lokacin. Na farko wata zazzafar kaunar maryam ce ta mamaye masa zuciya. na biyu kuma boka tsidau yatabbatar masa da cewa matukar aiki ya lalace to ciwon da mustapha yakeyi ze dawo kansa ne. a yau kam yayi nadamar kasancewar mommy mahaifiyarsa, ta cusa masa abunda baze taba amfanesaba arayuwarsa. Fiye da shekaru goma ta cusa masa kiyayyar mustapha me tsanani acikin ransa, ta nuna masa mustapha babban makiyinsune, alhalin bahaka abun yakeba. wani zazzafan huci ya fuzgar, hannunsa yakai ya ware hiramun dake kansa gami da cire safar hannunsa, dinkin da'aka masa yabayyana na ciwon da maryam taji masa. fadawa kan gado yayi sharab, zuciyarsa na masa kuna jiyakeyi tamkar ya kashe kansa dan bakin ciki, ga wata kewar maryam data cika masa zuciya. Da farko da yaudara yafara son maryam, amma zuwa yanzu son yarikide masa yakoma nagaske wanda yake barazanar tarwatsa masa zuciyarsa. kansa yafara bubbugawa akan gadon a fili yafara magana. "Mommy, why,..! why, dakika zabarmun wannan rayuwar, meyasa nabiye miki nakai kaina ga halaka,yanzu da wanne ido zankalli maryam wadda tabani dukkan yarda da amanarta, ta dauki a amatsayin bango na rayuwarta, koyaya zataji idan taji labarin ninake kokarin rabata da mutuncinta. Tabbas ubangiji baze barniba akan cutar da bayinsa wanda basujiba basu ganiba danayi. kansa yarike dayake kokarin tarwatsewa saboda damuwa, wannan ranar besan dame zekirataba arayuwarsa..........
Chapter 57 · 0% Book details