← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 128

Sashe 115

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryam ce ta fito daga ɗakinta, ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin ganinta, kallonta yake ta ƙasan ido tayi masa kyau sosai, tana sanye cikin wani riga da wando ƴan Pakistan Red colour, ta ƙara kyau da cika, hasken fatarta ya ƙara fitowa. bata kalleshi ba, itama kamar Yadda shima ya ɗauke kai kamar bai san da fitowartaba, kitchen ta nufa duk da bata da abunyi a kitchen din, ta fito ne dan taganshi kawai taji daɗi, ita kanta ta gaji da fushin datake dashi shi kuma yaƙi lallashinta, takai 10 minutes a kitchen din sannan ta fito, wayam taga falon bayanan, zama nayi akan kujera na sauya tasha na fara kallo, sai da aka kira sallar isha'i naga ya fito ɗaga ɗakinsa, ƙara ɓata rai nayi sosai na turo bakina gaba, murmushi yayi kawai ya kalleta ya fice zuwa masallaci, ganin ya fita na tashi na koma ɗaki nima danyin Sallah. Bayan ya dawo Aunty ta ƙara kiransa, ɗagawa yayi Aunty tace "nasata ta kunna wayarta ka mata magana, dan ita tanata maka magana tun kafin yau amma baka gani, yana nuna kamar kayi blocked ɗinta" yayi ɗanjim kafin yace "bani da Number ta" Aunty tace "Bari na tura maka" shiru yayi bayan sun gama waya Aunty yana tunanin me suhailat zatace masa, danshi ya riga da yayi deleting ɗinta gabadaya a cikin rayuwarsa, amma zai saurareta yanzu saboda Aunty. miƙewa yayi ya nufi gurin ƴar rigimarsa. ina zaune akan darduma idanuna a lumshe, so nake kawai najini a jikinshi dan baƙaramin missing ɗinsa nayi ba, yariga ya sabarmun koyaushe idan yana gida muna manne da juna. da sallama ya shigo ɗakin, buɗe idona nayi da sauri na juyo na kalli k'ofa tare da amsa masa sallamar, ba yabo ba fallasa yace "ki fito kici abinci" tashi nayi nabi bayanshi, a tare mukaci abincin kamar kullum, kuma a baki ya bani amma fuskarsa a haɗe sosai, ɗakinsa ya koma bayan mungama, bin bayansa nayi bayan na kawashe kayan da mukaci abincin na d'auraye, yana kwance akan gado yana latsa wayarsa bayan ya rage kayan jikinsa, tunda ta shigo ya k'ura mata ido, sosai shima yayi kewarta yayi kewar ɗumin jikinta dake saukar masa da nutsuwa, a ƙasan gadon na zauna ina turo baki gaba bance komaiba, murmushi yayi kawai aransa yana mamakinta, gaba-daya yanzu ta sauya abu kaɗan sai ta hau fushi, gashi indai be lallashetaba bazata kulashi ba, idan ya shareta kuka taita kuka tana damuwa. Tashi zaune yayi yana kallonta ganin yanda ta keɓe fuska zatayi kuka yace "zo" tare da ware mata hannunsa, da sauri na tashi dama abunda nakeso kenan na faɗa jikinshi ina sakin ajiyar zuciya, rungumeta yayi tsam a jikinsa shima yana sakin ajiyar zuciyar, a hankali yace "am sorry tawan, mun shirya ko?" girgiza kai nayi alamun a'a, yace "why?" A shagwabe nace "ba kaine kak'i kulani ba tun dazu" yayi murmushi yace "yanzu aina kula ki ko? kuma ai duk kece rigimar ki tayi yawa yanzu" na turo bakina gaba bance komai ba, na dora hannuna akan kirjinshi ina wasa da kwantaccen gashin kirjinsa, kissing lips ɗinta data turo gaba yayi yace "i missed you so much" nace "nima haka" gashin kanta ya shiga shafawa yana shishshina wuyanta, lumshe idona nayi cikin sanyin murya nace "yaya" yace "uhm" nace "zansha sweet da choculate" yace "babu" gashin kirjinsa naja tare da mintsinar breast ɗinsa, runtse idonsa yayi dan yaji zafi amma bece komai ba, bubbuga kirjinsa na shiga yi ina ƙananun kukan da babu hawaye, ɗagota yayi daga kirjinsa cikin lallami yace "mene ne?" nace "Sweet" ajiyar zuciya ya sauke yace "da safe zamuje ki zaba wadda kike so da kanki kinji" nayi murmushi cikin jin daɗin zan fita nace "dagaske yaya" ya gyadamun kai yace "promise" nace "thank you" ya lakacemun hanci yace "murna kike zaki fita ko?" nayi dariya nace "eh mana" yace "ina wayarki?" nace "tana ɗaki" yace "when last da kuyi waya da Aunty?" nace "3 days ago" yace "to albishirin ki" nace "goro" yace "a'a Ni banason goro" nace "me kake so?" yace "two things, saboda albishir ɗin dazan miki biyu ne" nace "me kake so toh?" yayi kasa da murya yace "kiss" na ɗan waro ido nace "da me kuma?" yace "something special for your own choice" na ɗanyi jimm nace "na yarda faɗamun albishir ɗin, na matsu inji" Yace "result ɗinku na NECO ya fito, gobe idan mun fita zamu biya capay mu duba" cikin farincikin nace "Alhamdulillah, naji daɗi sosai yaya, mafarkina ya kusa tabbata" yace "wanne mafarkin?" nace "na karatu" yace "kinason karatu ne?" nace "sosai ma yaya, burin innatama kenan taga nayi na karatu" yace "me kikeson karanta?" Nace "inason na zamu likitar mata" ya shafi kuncina yace "gud girl, insha Allah Zaki cika burinki very soon, amma sai kin haifamun kids" ya ƙarashe zancen yana shafa shafaffen cikinta, na shagwabe fuska nace "sai na tsufe kenan" yayi murmushi yace "A'a, a shekara nawa ne, kin haifamun, ni ko 3 kika haifa sun isa seki tafi karatunki" nace "idan ina karatunma ai zan iya hai....." sai kuma nayi shiru, yace "wahala zakisha, ga karatu ga rainon ciki ko baby, ki bari ki haifamun ko 2 ne, nayi miki alkawarin karatu har sai kince kingaji" na kwantar da kaina a ƙirjinshi, nace "Allah yakaimu lokacin" cikin jin daɗi yace "Amin" abunda yake ƙara burgeshi da ita kenan, kome yace mata tayi bata musa masa, koda bataso kuwa. nace "saura ɗayan albishir ɗin" yace "sai kin fara bani gorona" na dago da kaina nace to rufe idonka na maka, ya ɗan murmusa tare da lumshe idonsa, kallon small pink lips d'insa tayi na watsu sakanni, a hankali ta ɗora nata lips ɗin akan nasa ta fara tsotsa, hannunsa yasa abayanta ya ƙara mannata da jikinsa cikin jin daɗin yanda take tsotsar lips dinnasa kamar ta samu sweet, a hankali da dabara ya zira harshensa cikin bakinta ya fara bata wani hot kiss.... ya daɗe yana kissing ɗinta, da kyar ta samu ya barta, shima dan anata kiran wayarsa ne, kwantar da kanta yayi a kirjinshi yana shafa gashinta tare da sauke numfashi, luf nayi ajikinshi nima ina maida numfashi, a hankali ya ɗauko wayarsa, Aunty ce ta kirashi dataga be ɗagaba ta turo masa message na tura masa number'n suhailat ta whatsApp, baibi bayan kiran ba sai reply ya mata. cikin muryarshi datayi ƙasa sosai yace "Ummu" nace "uhm" yace "bacci" nace "um, um" yace "tashi inabaki ɗayan albishir ɗin" na tashi zaune yace "jibi Monday insha Allah Aunty tace zata zo ta ganki" na rungumeshi nace "Allah yakaimu, dama nayi missing ɗinta ita da Aliyata" yace "meyasa bakije kin gansu ba" nace "ai bazaka barni ba, kuma inaso inje sau ɗaya na taɓa zuwa fa" yace "ki bari zansa mana sai muje, bayan ta tazo" nace "toh" yace "to abani ragowar goro na" nace "kanason in maka waƙa?" yayi murmushi me sauti yace "banajin waka, amma indai ke zaki mun inaso, dannasan zatayi daɗi a wannan daddaɗar muryar taki" nayi murmushi na gyara zamana akan cinyarshi na fara rera masa wakar kamar haka:

_labarii a zuciya kaine, soyayya ce taka tayi tasiri ɗan gataa._

_Ehh....burinaa, ko dare ranaa, roƙo Allah nai gamo da Alkhairii, cikin rainaa, tunaninaa, lissafi nake nai gamo mainurii, kaine nawa wanda naggani rannan, kana taffiya sawaye akan tsarii, kaine dai, muradindai, na kamu, da sanka da nadamu ɗan gataaah._

_Ehh...abin sonaa, kazamo nawaa, shi ranar farin ciki ba'a boyewaa, misali kaika kasance na nunawaa, koma meza'ayi kai bani canzawaa, ka'entani nadena rud'ewaa, babbar magana k'aunarka tai yalwaa, dakai zanii, taho janii, kalami naso daure kayi minni ɗan gata..... ɗan gataaah.......ɗan gataaah_.

lips ɗinta kawai ya ƙurawa ido, yanda take motsasu abin sha'awa, ga muryarta datayi daɗi gurin karya wak'ar gwanin daɗi, kamar karta dena haka yaji. Ya sauke ajiyar zuciya yace "Wow tayi daɗi sosai wakar a bakinki, amma kuma naji kinyi shiru kici gaba mana" nace "aina gama, shikenan ita" yace "to ki ƙaramun wata" nace "ita kaɗai fa na iya, kabari sai na ƙara koyar wata zan maka" yace "a ina kike ji?" nace "a wayar Aunty zuhura na tura" yace "ok, muje muyi wanka, bacci nakeji" da mamaki na kalleshi nace "tun yanzu" yace "uhm" yana saukeni daga jikinsa, tare mukayi wankan kamar kullum, duk da har yanzu bandena jin kunyarsa ba, kamar yadda na kasa sabawa dashi a tarayyar auratayya, ko kayan bacci be bari sunsaba suka kwanta rungume da juna, bayan wasu mintuna yaji saukar numfashinta alamun tayi bacci, ajiyar zuciya ya sauke ya lallaɓa ya zareta daga jikinsa, turo baki tayi ta ɓata fuska sosai, tashi zaune yayi ya maye mata gurbinsa da filo, gyara mata kwanciya yayi ya lullubeta da blanket iya wuya, sauka yayi daga kan gadon ya kunna light ya ɗakko wayarsa, gefen gadon ya dawo ya zauna yana kallon Maryam ganin bata motsa ba, ya maida hankalinshi kan wayarsa, data ya kunna ya shiga whatsApp, Number'n suhailat da Aunty ta turo masa, yayi add to contact sannan ya shiga yayi unblock ɗinta ya mata "slm" suhailat dama tana online ɗin tana ganin ya mata magana ta shiga yi masa reply da sauri, daganan kuma ta shiga zuba masa maganganu, duk dai akan tayi missing ɗinsa ne, tanason ganinsa, sai turo masa emogi na kuka take wai ya dena sonta, shi dai kawai gani yake ba reply, a hankali ta buɗe idonta dan baccin yadena mata daɗi gabadaya, yanzu bata iya bacci kwata_kwata idan ba ajikinsa, ita kanta abun yana bata mamaki, ko sallar dare zai yi sai ta tashi itama, tashi zaune nayi a hankali ina kallon bayanshi da mamakin abunda ya tayar dashi, shida yace yanajin bacci, matsowa nayi kusa dashi cikin Muryar bacci nace "yaya" juyowa yayi da mamakin jinta a kusa da shi, yace "uhm, ina baccin?" na turo baki nace "ba ka tashi ka barni ba" na karashe zancen ina kwantar da kaina a kafaɗarsa, daidai nan wayarsa tayi ɗan vibrate alamar shigowar sako, kallon wayar nayi ba da niyyar komai ba, idona ya sauka akan sunan wanda suke chat naga ansa *baby suhailat*..........✍️

*By*
*Zeey kumurya*
*7️⃣7️⃣*
Chapter 115 · 0% Book details