← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 128

Sashe 89

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A falo natarar dashi a zaune akan kujera yana kallo kamar kullum, da sallama na shiga, banji ya amsamun ba amma dai na masa sannu da hutawa na shige ɗakina. ajiye wayar aliya nayi akan gado na rage kayan jikina na shige toilet..... Binta kawai Mustapha yayi da kallo harta shige dakin. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi, dama zaman jiran dawowarta yake. Hankalinsa gabadaya baya kan kallon dayakeyi, idan da za'a titsiyeshi bezece ga abunda ake acikin TV'n ba. zuciyarsa gaba-daya tana gurin Maryam yarasa meyasa tunaninta ya yawaita acikin zuciyarsa a kwanakinnan. wani numfashi me ƙarfi yaja ya fesar yana runtse idonsa, wani irin sanyi yakeji ajikinsa, dumin jikinta kawai yakesonji a halin yanzu yasan shikadaine ze masa maganin abunda yakeji, amma kuma idan matsalar take besan ta yaya hakan zata faruba, tun yayi sallar isha'i yadawo gidan tunanin ta yanda zasu kwana tare yau kawai yakeyi amma haryanzu ya kasa samun hanyar, miskilancinsa kuma baze barshi ya tunkareta da bukatarsaba. Ɗan ƙaramin tsaki yaja, ya buɗe idonsa dasuke wani lumshewa ya mike batare daya kashe kayan kallonba ya nufi bedroom ɗinsa, toilet ya shige domin yin wanka zuciyarsa babu daɗi......tunda na fito daga wanka ake kiran wayar Aliya banbi ta kantaba na ƙarasa gaban mudubi na fara shafe jikina da lotion, harna gama shafe_shafe na ba'adena kiran wayar aliya ba. Rigar bacci kawai na zira na ɗauki hijabina kato har ƙasa shima na zira. wayar na ɗauka har lokacin kira ake ba kakkautawa. Sweet dita danake sha kullum na ɗauko na jefa a bakina sannan na fita falo da wayar a hannuna, banganshi a falo. Hakan yasa nayi sauri nanufi kofa domin na kaiwa Aliya wayarta, dan bazan iya da wannan addabar kiranba. Mustapha yana hango Maryam ta cikin window'n dakinshi, tunda ya fito daga wanka ya kasa komai, zarya kawai yakeyi a dakinshi yana sake_sake. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ta fice daga falon, yasan part din ammi zataje, kuma yasan kome zatayi Aunty bazata barta ta kwanaba seta korota. Jallabiya ya ɗauka ya zira ya fesa turare kaɗan, ya fito ya nufi kitchen domin ya haɗa coffee ya sha, dan jiyake kamar hancin cikinsa ze tsinke. Babu kowa a falon ammi se suhailat dake barci haryanzu, dakin dasu Aunty suke na shiga sallama. Fitowar Aunty kenan saga wanka taga Maryam kamar daga sama. Da mamaki tace, "Maryam yanaga kin dawo" ina mikawa Aliya dake kwance tana kallona da alamun mamaki nace, "wlh aunty tun ina wanka ake kiran wayar Aliya, harna gama shiryawa ba'adena kiranba shiyasa nace bari nakawo mata" numfashi Aunty ta sauke tace, "hmmmm" kawai. ƙara kiran wayar akayi, Aliya ta ɗaga da sauri ta tashi ta raba ta gefena ta fice tana satar kallon Aunty. tabe baki kawai Aunty tayi tacigaba da shirin kwanciyarta, seda safe nayiwa Aunty na fito. Aliya ganin Maryam ta fito ta katse wayar datake tana dubanta tace, "matar yaya, irin wannan zuba kamshi haka kamar anyi barin turare ajikinki ko duk na zuwa office din oga ne" murmushi nayi bance komaiba na fice, dan idan na tanka mata shakiyancinta zata cigaba damun. Bansan daliliba ina fitowa naji wata irin faduwar gaba ta riskeni, bugun zuciyata kuma ya sauya ta fara bugawa da sauri da sauri. dafe kirjina nayi ina kiran sunan Allah araina. jikina a sanyaye na koma part dinmu, still yanzuma banganshi a falon ba, ɗakina nayi ƙoƙarin wucewa, fitowarsa daga kitchen hannunsa ɗauke da cup yasani tsayawa. Kallonsa nake ina ƙoƙarin daidaita nutsuwata har ya zauna akan kujera yana kurbar Black tea din a hankali. damuwa na hango ƙarara akan fuskarsa kuma yanayinsa kamar bashida lafiya ma. A hankali na fara taku still idona na kansa, kusa dashi naje na zauna cikin tausayawa nace. "Yaya baka da lafiya ne?" Lumshe idonsa yayi yanajin kamar ya yanyota ya rungumeta ajikinsa, daga mata kai kawai yayi alamar eh. kamar zanyi kuka nace, "Ayya sannu meke damunka?" " _Kece!_ ya faɗa acikin zuciyarsa amma a zahiri seya nuna mata kansa kawai da hannu batare daya buɗe idonsaba. Sannu na masa tare da fatan samun sauƙi na wuce dakina ganin kamar bayason magana. buɗe gajiyayyun idanunsa yayi yana fesar da wani zazzzafan numfashi daga bakinsa, kamar ya bita yace karta tafi amma baze iyaba yana kallo ta shige dakinta. Ajiye cup din hannunsa yayi ya mike yana taune lips ɗinsa, hannunsa dafe da mararsa ya shige bedroom ɗinsa. Kan gado yana faɗa cikin rashin kuzari zuciyarsa babu daɗi sosai mararsa ke murda masa kamar yayi hauka haka yakejin kansa, be taɓa jin kansa a irin wannan yanayinba se sau ɗaya a rayuwarsa, lokacin da accident ya haɗashi da wata yarinya yaje gidan su abokinsa. gumi ne yake tsatstsafo masa a jiki ta ko'ina.... Tunda na koma daki sena kasa sukuni, zuciyata ta kasa nutsuwa, yanayin dana ganshi nasan yana jin jiki bakadanba musamman yanda idanunshi sukayi ja, nasanma da kyar ma idan yasha magani. Tuna lokacin da nayi ciwon ciki nayi da azumi, haka ya dinga zarya a dakina yana duba jikina, nima Yakamata ace naje na bashi kulawa,dan yana buƙatar kulawar tawa a halin yanzu a matsayina na matarsa. Kamar antsikareni na mike, inda nake ajiye magungunana naje na buɗe na dakko Panadol na fice daga ɗakin, seda na ɗauki robar ruwa mara sanyi sannan na nufi dakinnashi zuciyata na ƙara tsananta bugu.....✍️

_*Thank you so much my FAN'S for your wishes and du'a. Allah yabar kauna da zumunci me ɗorewa.❤️🥰*_

*By*
*Zeey kumurya*
*ABINDA KASHUKA.....*

_*BY*_
_*ZEEY KUMURYA*_

*6️⃣2️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

........... Har na ƙaraso bakin kofar dakinnasa sena tuna ban dauko cup ba, juyawa nayi na koma kitchen na dakko na dawo. A hankali kamar mara gaskiya na murda handle din dakin tare da turawa. kwance na hangoshi yayi ruf da ciki idanunshi a lumshe, hannunsa ɗaya dafe da kansa. Tausayinsane ya ƙara lullubeni, a hankali nake takawa har na ƙarasa gaban gadon idanuna akansa. Tunda ta shigo dakin yaji alamun anshigo, amma ya kasa buɗe idonsa yaga ko waye, seda ta ƙaraso ya gane itace ta hanyar sassanyan kamshinta daya ziyarci hancinsa. Farin ciki mara misaltuwa ne ya lullube zuciyarsa gami da mamakin abunda yakawota dakinsa adaidai wannan lokacin, dan be taɓa zatoba, ko motsawa beyiba duk da yanda zuciyarsa take azalzalarsa akan ya buɗe ido koda kallontane yayi koyaji sauƙi aransa. Ajiyar zuciya na sauke ina tunanin ta ina zanfara, dan atunanina bacci yake. A jiye ruwan da cup din gami da maganin nayi akan bedside, a hankali na hau kan gado na zauna daf dashi zuciyata na ƙara tsananta bugu, tafin hannuna na dora akan forehead dinsa, bayan na zame hannunsa a hankali daga kannasa, zafi naji akannasa ga jijiyoyin kansa duk sun fito rada_rada se gumine dake ɗan tsatstsafowa kadan_kadan a goshinsa, daga gani kan bakaramin ciwo yake masaba. Ƙasan hijabina nasa na fara goge masa gumin. Ajiyar zuciya ya sauke sassanya yana ƙara lumshe ido lokacin dayaji tattausan tafin hannunta akan goshinsa. seda na goge masa gumin tass sannan a hankali na fara kiran sunansa domin na tasheshi na bashi maganin yasha, dan banga alamun yasha maganinba. "Yaya..yaya!" Buɗe idansa yayi a hankali ya saukesu akan kyakkyawar fuskarta. cikin tausayawa nace, "sannu ya jikinnaka?" Daga mata kai kawai yayi still idanunsa na kan fuskarta. "Allah ya ƙara sauƙi" na faɗa a hankali ina tashi na sauka daga kan gadon. Robar ruwan na ɗauka na tsiyaya a cup na ballo maganin guda biyu, kan gadon na dawo na taimaka masa ya tashi zaune, filo nasa masa ya jingina bayansa, sannan na dakko maganin na bashi, karba yayi ya sha ya kora da ruwan, sannan ya mikomun sauran maganin yana sauke ajiyar zuciya, Ni Ko se jera masa sannu nake cikin tausayawa. Zamewa yayi ya koma ya kwanta tare da lumshe idanunsa. kamar kar na tafi na barshi haka nakeji, zuciyata ta cika da tausayinsa yanda yake taune lips dinsa nasan ba ƙaramin jin jiki yakeba. jiki a sanyaye na tashi na fice bayan na kashe masa light din dakin, ina masa addu'ar samun sauƙi a cikin raina. Yana jinta harta fice amma yakasa tabuka komai, murnarsa duk ta koma ciki na zuwanta, ya rasa meyasa daya ganta yakasa aiwatar da komai akanta, duk da yanda yake cikin tsananin bukatarta a yanzu. hangota yakeyi a idanuwansa yanda takeyin komai cikin nutsuwa da sanyinta lokacin datake bashi magani, yaga tsananin tausayasinsa a cikin idanunta. ciza lips ɗinsa yayi cikin takaici. besamu bacci ya daukeshiba se can dare........
Chapter 89 · 0% Book details