Sashe 100
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Mustapha yana shiga part ɗinsu ɗakin Maryam ya nufa direct, tunda beganta a part din ammi ba yasan tana ɗakin. ɗakin dulum babu haske ko kaɗan, yana mamakin yanda take bacci a haka bata barin hasken ko kaɗan. Torch light din wayarsa ya kunna ya haska kan gadon. tana ƙudundune kamar koyaushe kamar wadda take kwanciya a tsorace ta dunkule guri ɗaya. A hankali ya ƙarasa kan gadon ya haye yana ƙara haskata. Blanket din data rufa ya janyeshi daga jikinta a hankali juyi tayi ta matso daf dashi hannunta ɗaya ta ɗora akan cinyarsa tana sauke numfashi taci gaba da baccinta hankali kwance, fuskarta ya haska sosai kifkifta ido ta fara yi saboda haske mata idon da yayi. Ajiyar zuciya ya sauke, ya ɗauke idonsa daga kallon fuskarta. Blanket din ya janye gaba-daya daga jikinta, ya gyara mata kwanciya, yana yin komai cikin dauriya ne, amma tuni ya fara neman nutsuwarsa ya rasa saboda rigar jikinta shara_shara take, kuma duk ta dage sama santala_santalan cinyoyinta duk suna waje. ga kamshin jikinta dake ƙoƙarin hargitsa masa lissafi. kwanciya yayi a gefenta ya janyota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa, blanket yajanyo ya lullube musu rabin jikinsu. Maryam se ƙara manne masa jiki take, kanta ya ɗora akan hannunsa guda ɗaya, ɗayan kuma ya fara yawo dashi a jikinta yana shafa lallausar fatarta me sulbi yana sakin numfashi a hankali a hankali cikin jin daɗi, Maryam kuwa jitayi tamkar susa yake mata baccinma se ya ƙara mata daɗi. seda ya shafeta san ransa amma a hankali yadda bazata tashiba sannan ya kyaleta badon yasoba, se dan karya wuce gona da iri ya kai matakin dabaze iya hakura da itaba. rungumeta yayi tsam ajikinsa kamar ze maidata ciki, addu'a ya tofa musu bajimawa bacci ya ɗaukeshi.....
*MOMMY*
Yau da wani a zababben ciwon kai tatashi ko idonta dakyar take iya buɗewa, shine dalilin dayasa ba fita dan fara shirin tafiyarta Landon ba, a daren jiya bata samu ishashshen bacciba saboda tunane_tunane data dingayi. Haka ta wuni kwance akan gado tana juyi saboda kannata kamar ze tsage gida biyu haka take jinsa. Se bayan la'asar ta samu ya ɗan sassauta mata harta kira likitanta ta zo ta dubata. Magunguna ta rubuta mata, ta kuma ce mata ta rage yawan damuwa domin a halin yanzu jininta ya hau sosai. Megadinta ta bawa takardar da Dr. Ta rubuta mata magungunan ya siyo mata a wani pharmacy, shine da tasha ta samu bacci ya ɗauketa.....
_*BAYAN KWANA UKU*_
Tattali sosai mustapha yake nunawa Maryam, kodayaushe yana gida manne da ita yana bata kulawa, sallah ce kawai take fitar dashi. maryam kuwa se taɓararta take zuba masa son ranta kusancinsu na ƴan kwanakinnan ba ƙaramar shakuwa ya haifar a tsakaninsu ba, wanda su kansu basu gane hakanba. Kullum tare suke kwana manne da juna, amma Mustapha be ƙara yiwa Maryam komaiba saboda yadda take a tsorace da shi, kullum idan zasu kwanta a ɗari_ɗari take, duk abunda take yana sane da ita, kyaleta kawai yayi tagama abunta. Maryam tama manta da magungunan da zuhura ta bata, bata amfani dasu. lalle kawai take tafasawa tana tsarki dashi safe da dare, se ruwan ɗumi da datake tsarki dashi parmanantly. Taji sauƙin jikinta sosai, yanzu batajin komai na ciwo a jikinta ta koma normal kamar da. Yau talata gobene kuma mustapha ze tafi Kano dubo Sadik jiya monday suka dawo, maryam batamasan da tafiyar tasaba har yau dan be faɗa mata ba. Yau mustapha ya fita kasuwa tun safe, Maryam setaji gabadaya yau bata jin daɗi a cikin zuciyarta, gashi kuma se dare suke dawowa. Bayan sallar la'asar ina zaune a falo na ina karatun Al_Kur'ani megirma. kamar a mafarki naji kamshin turarensa ya cika falon, dago da kaina nayi da sauri na kalli bakin kofa, shine ya shigo bakinsa ɗauke sallama. cikin tsananin farin cikin ganinsa na amsa masa, sannu da zuwa na masa ya amsa ya wuce ɗakinsa. rufe Alkur'anin nayi na ajiyeshi a gefen darduma sannan na mike na nufi kitchen na dakko robar ruwa guda ɗaya tare da ƙaramin cup na nufi ɗakinnashi, yana zaune a bakin gado ya cire takalmin kafarshi, yana cire rigar jikinshi na shiga ɗakin. "Slm alkm" na faɗa cikin sanyin ina satar kallonshi. batare daya kalleniba ya amsa. Ajiye ruwan nayi na gabansa na koma gefensa na zauna, kallon ruwan yayi ya kalleni. ɗan zamowa nayi daga kan gadon danake na buɗe robar na tsiyaya masa ruwan na miƙa masa. karba yayi tare da furta "thanks" a hankali. tass ya shanye ruwan, ya tambayeshi a karo masa ya girgizamun kai alamar a'a. bance komaiba na ɗauki ruwan da cup din na fito falo bin bayanta yayi da kallo harta fice, ajiyar zuciya ya sauke ya ƙarasa cire kayan jikinsa ya faɗa toilet. ban koma dakinnashiba bayan na ajiye ruwan zama nayi a falo ina tunanin rayuwa. Se wajen ƙarfe 6 ya fito daga ɗakin cikin shirinsa na ƙananun kaya, kallonsa nake ta ƙasan ido yamun kyau sosai, kowanne kaya yasa amsar jikinsa suke kamar danshi aka yosu dama can, gashin kannannasa yasha taza ya kwanta abun sha'awa, dama shi bama'abocin saka hula bane koda yasa manyan kaya. kasarowa cikin falon yayi ya zauna a kusa dani, lumshe idona nayi saboda daddaɗan kamshinsa daya cikamun hanci. A hankali batare dana buɗe idonaba nace, "in kawo maka abinci?" "Later" ya faɗa yana ɗaukar remote ya kunna TV ya fara kallon Labaran yamma. yanayi yana kallon fuskar maryam data ɗauke masa kai tana kwabe fuska, yasan ko meyasa take hakan murmushi yayi kawai ya shafi gefen fuskarta yace, "yadai? ƴan mata" shagwabe fuska nayi sosai nace, "ina alawata?" ɗan buɗe bakinsa yayi kaɗan yana fito da kyawawan idanunsa waye alamun shock dinnan yace, "oh, sorry namanta ne" kallonsa nayi na ɗauke kai ina turo baki gaba, tun jiya alawar da Aunty zuhura ta bani ta kare, yau tun safe dana tashi naketa bashi sallahun ya siyomun na maimaita masa sau da yawa saboda karya manta,amma seda ya manta. murmushi mustapha yayi ganin yanda tayi da fuska. Janyota yayi jikinsa ya kwantar da kanta akan kafadarshi tare dasa hannunshi ya zagaye bayanta, Ajiyar zuciya na sauke na ƙara lafewa ajikinnasa. A haka muka kasance harya gama kallon. Tashi yayi yacemun zashi gurin ammi daganan ze wuce masallaci, Allah ya kiyaye na masa tare da fatan dawowa lafiya.
Tunda ya fito daga part ɗinsu ta hangoshi ta fito ne itama zata fita, ajiyar zuciya ta sauke cikin jin daɗin ganinsa, rabon data ganshi tun jiya da safe, tsayawa tayi cak tana kallonsa. Wani tunani ne ya darsu a cikin zuciyarta akan shawarar da fareeda ta bata, duk tana jin tsananin tsoro amma haka ta ƙarfafa zuciyarta akan ta jarraba kawai kozatayi nasara, tunda tabi duk hanyar da zatabi dan ganin yasan da ita amma duk a banza, ita kuma a yanda takejin sonsa acikin zuciyarta da burin datake dashi na auren mijin kece sa'a bazata iya hakura dashiba, dole tayi duk yadda zatayi wajen ganin ta samu gurbi acikin zuciyarsa, ga kuma dama ta samu bazata bari ta kufce mataba. tana ganin ya ƙara kusantota ta tafi da gudu tana faɗin "yaya NOOR oyoyo" tare faɗawa kirjinsa.😳........✍️
*By*
*Zeey kumurya*
*ABINDA KASHUKA....!*
_*BY*_
_*ZEEY KUMURYA*_
*6️⃣9️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*