← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 128

Sashe 55

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

makashi da wani maganin daban dayake kara ta'azzara ciwonnaka harta ruwan tofin daya baka seda nasauyashi. Kullum cikin dare zanzo inwatsa wani magani koni ko sadiq acikin wannan yarkaramar tukunyar kasar da maryam ta dauka wadda ni dakaina nasanya maka ita acikin filonka,kuma acikintane sihirin dana maka yake wanda nahada harda gashin kanka. Addu'ar da maryam take maka shiyake sanyaya tukunyar daga mugun zafin datake dashi tana zafafa maka jikinka, nikuma dazarar tsakiyar dare tayi zanzo inkara barbada magani acikinta wanda zata koma ainihin zafinta. bansan ya'akayi tukunyarnan taje hannun maryamba, tabbas maryam tazamemun ciwon idanu, ta rushemun ginin dana debi shekaru masu yawa ina ginasu acikin yan mintuna. kasani mustapha maryam ta batamun duk wani shirina akanka amma banhakuraba danni mutumce bame raguwar zuciyaba zankoma incigaba indora daga inda natsaya senaga bayanka dakai da maryam da sulaiman d....." "karya kikeyi mushirika da yardar Allah karshenki yazo kuma zakiga sakayya tun anan gidan duniya kikiyayi ranar da *zaki girbi abunda kikashuka* na sharri da hannunki" cewar aunty cikin kuka data katse mommy da wannan maganar. Gabadaya dakin kuka sukeyi banda daddy daya daure yakeyin na zuci,amma idanunsa sunyi jajur saboda tsananin bacin rai da bakin ciki da damuwa gami da dumbun takaicin halin mommy. da kuma mustapha dayaji jikinsa yayi masa wani irin sanyi duk ya shika, tsanar mommy gabadaya ta gama baibaye zuciyarsa ta maye gurbin tarin kaunar dayake mata. bayason mugunta kuma bayason mugun mutum, yanxo mommy akan dukiya tayi sanadiyyar rasa rayukan mutane da yawa, ko tunanin itama wataran zataje inda sukaje din batayi, lallai wanda yayi nisa bayajin kira,yaji yatsani kansa da duniyarma gabadaya,yanayin dayakejin kansa baze misaltuba. Cikin kuka haidar yadubi mommy dake tsaye har lokacin yace, "mommy amma baki kyautamanaba mu yayanki mukika cuta kika bata mana suna, wlh nayi danasanin kasancewarki mahaifiya a gareni, kin cutar damu gashi baki bamu tarbiyyaba w....." Kuka yaci karfinsa meban tausayi wanda yasashi kasa karasa abunda yakeson cewa. Suhailat ma kuka takeyi tamkar ana zare mata numfashi dataji mommynta mafi soyuwa agareta ita tayi sanadiyyar barin mahaifanta duniya. Daddy ne yadubi sadiq Cikin kunar zuciya yafara magana. "Amma sadiq kabani mamaki kaida nake ganin ko mutuwa nayi zaka gajeni segashi dakai aka hada baki gurin yin wannan mummunan danyan aikin, yanzu mezakacewa da ubangijinka idan ka mutu akan cutar da bayinsa da basujiba basu ganiba dakayi" cikin shashsheka sadiq yadago yana duban daddy yace, "daddy kagafarceni wlh sharrin shedanne da kuma sharrin zuciya, gami da hudubar mommy. Tabbas yau naji wata nadama ta lulllubeni gamida kunyar ubangijina akan abunda nadade ina aikatawa tsawon wasu shekaru". maida dubansa yayi akan mommy yacigaba da magana. Kin cutar dani mommy kindorani akan zunubin da ubangiji baze taba yafemunba, mafi girman zunubi kuma agurin Allah ga kuma hakkin wadanda nazalunta,wanda ahalin yanzu basa doran duniya bare nanemi yafiyars..." kukane yaci karfinsa. faruq ne yashare hawayen dake malala akan fuskarsa yadubi daddy yace, "babu shakka zuwan maryam alkhairi ne agidannnan domin kuwa ta sanadinta duk wani shirin mommy ya lalace wanda harnima nadawo cikin hayyacina daga mugun asirin da mommy tamun. Duk abunda mommy da sadiq suke kullawa ina sani amma harshena baze iya sarrafuwaba balle harna fadawa wani. A duk lokacin da sadiq yakaiwa wata yarinya hari a gidannan ina hankalce dashi sedai bani da ikon hanashi kokuma natona masa asiri. Wannan ruwan addu'ar da maryam takeyiwa mustapha kullum idan yayi guntu shinake zuwa nasha batare da kowa yasaniba, da haka harna farajin nima nafara dawowa daidai. A Daren jiyane da zannurain yayi bacci nadauka ruwan nasha a lokacinne kuma naji dukkan nutsuwata ta dawo, kaina yamun wasai tamkar ansaukemun wani abu me mugun nauyi acikinsa. Dama tunda naji sadiq yace yayi tafiya nasan batafiya yayiba domin haka yakeyi duk sanda zeyi mummunan aikinshi seyace tafiya zeyi. barin part dinnan nayi gabadaya nakoma part din mommy na buya a inda babu me ganina, kuma inada yakinin dama da yardar Allah sadiq baze samu nasara akan maryam ba, harya shiga dakin yafito banbar part dinba, ina tsaye a inda nabuya naga yafito da gudu dafe da goshinsa nima binbayansa nayi dasauri harya buya ajikin fulawoyi sukayi waya da mommy duk ina biye dashi besaniba ya tashi da niyyar guduwa shine narikeshi kokuwa muka shiga yi dashi hardai nayi nasara akansa saboda yafara galabaita ga jinin dake zuba ajikinsa. Kamasa nayi nakaishi can bayan gida na daureshi dankarya gudu, seda azubane nadaukeshi nakaishi asibiti aka masa treatment a hannunsa da goshinsa shinema kuka ganmu munshigo tare dashi. dama nataho da niyyar nazo na fayyace muku komai sekuma natarar da yaya mustapha yatashi haryana'iya magana da kansa" Shiru dakin yayi bayan faruq yagama magana, babu abunda kakeji se tashin kukan suhailat dana sadiq,aunty kam girgiza kai kawai takeyi tana mamakin rashin imani irinna mommy sekace ba musulmaba,akan duniyar dakowa zebarta. Mustapha kuwa jikinsa yayi tubus tamkar andafa dankali ko danyatsansa daya ya kasa motsawa soyayyar mahaifiyarsa gami da muradin ganinta susuka cika masa zuciya,yanajin tamakar yabude idonsa yaganshi agabanta. kudiri yadaukarwa kansa ayau ba gobeba zefara nemanta a duk inda take acikin duniyarnan matukar tana numfashi . Zannurain datun dazu shine bece komaiba ya katse shirun nasu yana duban mommy da fadin. "Mommy dan Allah kihakura haka, duk abunda kikayi abaya be ishekiba sekinyi yunkurin karayin wani mugun abun, memakon kikoma ga Allah kinemi yafiyarsa da wadanda kika zalinta amma sema kara wani kudirin kikeyi babu alamar nadama atattare dake, bayan kuma Allah yanuna miki ishara a lokaci daya ya karya dukkan wani shiri naki da kikayi shekaru masu yawa kina kullawa." Wata dariya Mommy takece da ita irinta marasa imani sannan tace, "yaro man kaza, ai rago shiyake ja baya a fada. Karfa kamanta akan wannan cikar burinnawa yar'uwata guda daya tal tarasa rayuwarta kuma nice sanadi, sannan kuma kawata hindatu data rakani gurin boka, naga irin mutuwar wulakancin datayi a sanadiyyar bin bokaye, duk besa nasadudaba se dan wannan abun. To kusani ba gudu baja da baya yanzu aka fara wasan,idan kaga banga bayan mustaphaba da sulaiman to katabbatar bana numfashi a doron duniya.............✍️
Chapter 55 · 0% Book details