← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 128

Sashe 81

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

..........Ammi ta rakasu da murmushin jin daɗi, dama ita burinta kenan taga sun haɗa kansu kuma Alhamdulillah ta lura babu wata matsala a zamannasu.... Yana gaba ina binsa abaya har muka karasa gurin motar, na zagaya na shige bayan shima ya shiga. kafin ya kai ga kunna motar wayarsa ta hau ruri cikin amo me daɗin sauti. dagawa yayi ya kara a kunne tare da yin sallama. Amsa masa akayi sannan yace, "Aunty ina kwana, ya ibadah?" Da sauri na kallesa jin ya ambaci sunan Aunty. daga can ɓangaren bayan Aunty amsa masa gaisuwar ta ƙara da faɗin, "Muhammad suhailat ce keson magana dakai, ta dameni inkira mata kai, wai ita idan takiraka baka samun wayarka." Cikin matukar mamaki yace, "suhailat kuma?" Gabanane yayanke ya fadi jin sunan Aunty suhailat daya ambata. Aunty tace, "ehh" bekara cewa komaiba duk da zuciyarsa cike take da mamakin meyakai suhailat gidan Aunty, tunda yasan ba zuwa takeba. nikuwa tsumu nayi ina saurarensu. Suhailat bayan Aunty ta mika mata wayar cikin azabarbi tace, "yayana! I missed you, dan Allah yaushe zaka dawo, wlh gaba-daya duk nabi nadamu, ganinka kawai nakesonyi" lumshe idonsa kawai yayi bece mata komaiba. suhailat taita masa magana amma kememe yaki cemata ko "kala" harda kukanta amma yayi biris abunsa karshema kashe wayar yayi dan kar Aunty ta karba ta masa faɗa akan kin kula suhailat ɗin da yayi. kallon Maryam yayi ta kasan ido, ta haɗe rai sosai an tsuke bakinnan. tabe bakinsa yayi ya tada motarsa suka wuce....yauma damuka tashi shiyazo ya ɗaukeni, Ni mamakinshi nake yanda yake barin kasuwa yadawo ya dakkoni sannan ya koma. Bayan ansha ruwa kafin sallar isha'i, su Maryam suna zaune a falon ammi dukansu suna hira. Ammi ta dubemu nida umaimah tace, "ɗiyata ku tashi kuje gurin Musa tailer, seki zabi ɗinkin da kikeso ya miki ya kuma gwadaki" a hankali nace "to ammi, da nisane gurin?" Aunty zuhurace tace, "da ɗan nisa kadan gaskiya" umaimah kuwa kallon su kawai take tana tabe baki, dan zuhuranma ba wani shiri suke da itaba. Ammi ta dubeta tace, "Autatah ki tashi kuje tare, bari nakira NOOR yakaiku idan babu abunda yake idan kuma yana wani uzurin sena kaiku da kaina." Da umaimah harzatace kanta na ciwo bazata raka maryamba, amma jin ance mustapha ne ze kaisu seta fasa. Ammi ta dakko waya takirasa ta sanar masa, yace mata su jirasa gashinan zuwa. ammi na sanar musu Umaimah ta tashi da sauri ta shige daki, turare ta bulbula har yayi yawa. Tana fitowa Aunty zuhura tace, "kai umaimah wannan turaren dakika saka yayi yawa har yana hawa kai fa" murguda baki tayi ta zauna batace komaiba. Ammi ce tace, "gaskiya autah yayi yawa" cikin sangarta tace, "ammi feshi biyu nayifa haka turaren yake" ammi zata kuma Magana wayarta tayi ƙara, dagawa tayi mustapha yace mata yana jiransu a mota. Bayan ta kashe wayar ta dubemu tace, "ku tashi kuje kunsan bayason jira" Zuhura na dariya tace, "ai da gimbiyarsa dole yajirasu" murmushi nayi kawai, na musu sallama muka tafi.

A gajiye nake tafiya yau nagaji sosai kuma azumin yaɗan kolani. ina gaba tana bina a bayana danna rigata fitowa daga falon. yana zaune acikin motar ya buɗe murfin ƙafarsa ɗaya na waje yana latsa wayarsa. zagayawa nayi na buɗe front seat na shiga da sallama ɗauke abakina. batare ɗaya dagoba ya amsamun acan ƙasan makoshi. Yana ganin umaimah tataho ya maido ƙafarsa ya rufe Kofar, kunna motar yayi, ya kuma kunna light din motar. kallon fuskar Maryam yayi yaga itama shi take kallo karaf suka haɗa ido. Hararata yayi nayi sauri na ɗauke idona daga kansa ina kebe fuska. umaimah ta buɗe bayan motar ta shiga sannan tace, "yaya NOOR ina wuni, dafatan kasha ruwa lafiya" "lafiya" yabata amsa atakaice yana tada motar. reverse yayi megadi ya buɗe mana get muka fice daga gidan. umaimah na masa hanya har muka karasa. A kofar wani shago mukayi parking, umaimah ta fito ta dubi Maryam daketa lumshe ido bacci fal cikinsu tace, "ki fito" mustapha na kallon Maryam yace, "ina zata?" Umaimah tace, "ciki zamu shiga ze aunatane ta kuma zaɓi ɗinkin datakeso" fuskarsa a tsuke yace, "bazata ta shiga cikin wannan mazanba" galala umaimah tayi tana kallonsa baƙin ciki fal ranta yanda mustapha yake nuna kishin Maryam akan komai. Maryam kam sama_sama take jinsu amma bata fahimtar mesuke cewa bacci yafara fuzgarta. umaimah batace masa komaiba ta juya ta nufi cikin shagon, bayan kamar 10 minutes suka fito tare da toilor ɗin. gaishe da mustapha yayi, Maryam kuma data wartsake dakyar ta gaisheshi. Ya dubeni yace, "Hajiya wanne irin ɗinki za'a miki?" Nace masa "style me kyau kawai" yace, "doguwar riga ko riga da skirt koda zani?" "Kamata doguwar riga" mustapha dake latsa wayarsa tamkar baya saurarensu ya fadi hakan. na kallesa kawai bance komaiba. Toilor'n yace, "angama ranka ya dade" umaimah ma ta faɗa masa irin ɗinkin takeso. Toilor'n yace to nafito ya gwadani, amma Mustapha ya hana. Toilor'n yace masa, to umaimah seta gwadani amma kememe bawan Allah nan yahana waishi baza'a gwada masa mata a titiba. Dariya kawai toilor'n yayi yacemun muje to zezo har gida ya karbi measurement ɗina. muna cikin tafiya a mota naji mutum ya janyoni jikinsa. lumshe idona nayi ina sauke ajiyar zuciya. daidai kunnena yakai bakinsa cikin wata sanyin murya yacemun "kin sakarmun nauyi fa" aiko kamar ya tunzurani nakara manne masa a jiki. umaimah dake baya ta hadiye wani yawu me daci a ranta tana faɗin. "Tsabar jaraba yana tukinma amma seya wani rungumeta, gashi se wani rada_rada yake mata, kamar sun manta da ni a motar" mtss taja siririn tsaki tana hararar bayan Maryam. Mustapha sarai yaji tsakin da umaimah tayi kawai sharewa yayi. kafin suje gida Maryam tayi bacci ajikinsa. yanayin parking umaimah ta buɗe kofa ta fice. Kallon Maryam yayi yaga baccinta take hankali kwance, se numfashi take saukewa a hankali. Kurawa fuskarta ido yayi a karo na biyu a rayuwarsa bekuma san dalilin kallonnata dayakeba. tabe bakinsa yayi bayan yagama ƙare mata kallon, a hankali yafara ƙoƙarin rabata da jikinsa. Maryam kuma ta ƙara kankameshi. Lumshe idonsa yayi ya ƙara rabata da jikinnasa. Maryam ta buɗe idonta a hankali tana jingina jikinta da kujera, buɗe murfin motar yayi ya fice abinsa, bekara koda kallon inda nakeba . da kyar nima na daure na fito, wani irin bacci nakeji. Kulle motarsa yayi yanufi masallaci dan har anyi isha'i anfara asham. Ban koma part din ammi ba, na koma namu......

Kwanci tashi asarar mai rai. Yau 23 ga watan Ramadan yau kuma muka gama exam dinmu ta NECO, dayake babu wani interval sosai. A 'yan kwanakinnan wata shakuwace ta shiga tsakanin Maryam da Mustapha, wanda su kansu basu gane hakanba. Mustapha matukar da umaimah a guri ze nunawa Maryam kulawa da tattali koda a gaban ammi ne kuwa. Hakan kuwa bakaramin kona ran umaimah yakeba. gashi kullum son mustapha karuwa yake a ranta tarasa yadda zatayi, zuciyarta nabata shawarar ta sanar masa kawai koze amshi tayinta, amma kawarta ta hanata tace ta bari a gama azumi tasan mezasuyi dole mustapha yasota. Maryam kam ta fara gwada abubuwan da taji zuhura na fadawa kawarta a waya, ta kuma dage da addu'a akan Allah ya waiwayo mata da hankalin mustapha gareta. Mustapha kuwa yanzun baya gane kansa dan kwata_kwata bayajin daɗin jikinsa, yakuma rasa meke damunsa. Gashi yanzu babu abunda yaji yanaso sama daya dinga jin Maryam ajikinsa yana shaƙar daddaɗan kamshinta, yanason kamshin jikinta sosai. kullum seya ayyana ya rungumeta ba'adadi amma seya kasa. saboda yana ganin Maryam zata rainashi gata yarinya ƙarama ai girmansa seya zube. Ya lura kuma yarinyar itama miskikar kantace.
Chapter 81 · 0% Book details