Sashe 47
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
...........Gaba daya suka juya atare cikin tsananin mamakin jin muryar me maganar gami da abunda yafada, mutumin dasuka manta rabon dasuji yayi doguwar magana irin haka. "Faruq! ni mahaifiyarka kake jifa da wadannan muggan kalaman, nikake cewa nayiwa dana nacikina asiri kuma bani na haifesaba,kana cikin hayyacinka kuwa faruq!?" mommy tafadi haka cikin tsawa da matsanancin tashin hankali. murmushi faruq yayi, gami da yin taku yakaraso har gaban mommy yace, "ina cikin hayyacina mommy nake fada miki wadannan maganganun,kidena wani borin kunya,kina nuna kamar bakisan abunda kinfi kowa sanin saba,yau ranar tonan asirinki ce tazo keda wanda kuke shirya komai tare, kisani asirin dakikamun na shekara da shekaru ya karye hakama wanda kikayiwa daddy ya karye" kafin mommy tayi magana aunty tatari numfashin faruq tana duban daddy tace, "yaya kanajin me faruq yake cewa akan mahaifiyarsa amma kayi shiru kana kallonsa, menene gaskiyar al'amarin yaya?" Shiru daddy yayi bece komaiba amma fuskarsa tana nuni da tsantsar damuwa, da tashin hankali,kusan 50 second sannan ya numfasa yace, "tabbas atika ba'ita ta haifi mustapha b..." wata hantsilowa mustapha yayi daga kan gado jikinsa gabadaya yadauki wata irin kyarma hannunsa narawa yahau nuna mommy yana kallon daddy, magana yakeson yayi amma yakasa se bakinsa dake motsi alamar yanason yace wani abu. aunty, haidar,zannurain atare suka mike tsaye cikin tsananin dimuwa jin abunda daddy yace,aunty hartana yarda wayarta kasa batare data saniba, baya mustapha yayi luuu,ze fadi kasa,dasauri daddy yataro jikinsa,suka zauna abakin gado, dama jikinnashi babu kwari gakuwa wani bakin zance dayakeji wanda yake kokarin saka zuciyarsa ta buga, wanda yajishi tamkar saukar ruwan narkakkiyar dalma atsakiyar kansa. kallon mommy aunty takeyi amma itama takasa magana se girgiza kai kawai takeyi, aranta tana cewa, "wanne irin burine wannan da mommy takeson cikawa wanda har tayiwa danta na cikinta da kuma mijinta asiri,kuma take kokarin kashe mustapha" mommy kuwa jitayi gabadaya yawun bakinta ya kafe kaf, zuciyarta tahau harbawa dasauri cikin tsananin tashin hankali bata taba tunanin abun zezo mata ahakaba, "nashiga uku ni atika,yanzu kenan sulaiman ze iya tuno komai daya faru ada" mommy ta fadi haka atunaninta azuci tayi maganar, amma seta tsinkayi muryar daddy yana fadin, "tabbas tunanina yadawo akan abunda kika gusarmun da hankali akansa, kuma ranar wanka ba'aboyen cibi yau zansanar da mustapha abunda nake da burin sanar masa shekara da shekaru,amma kika rufe mun baki ruf namanta nakasa sanar masa." wani irin murmushi mommy tayi me ciwo cikin karfin hali tace, "to seme, sulaiman idan kafada masa, kadade baka sanar da mustapha gaskiyaba, to bari kaji insanar maka fadar abunda kake kokarin yi, daidai yake da tonawa mustapha asirin dani dakai muka rufa masa arayuwarsa" shima daddy murmushin yayi yace, "insha Allahu, fadata saidai tazamo masa alkhairi arayuwarsa" mommy tana kokarin sake magana sadiq dake falo tundazu yashigo dakin asukwane fuskarsa murtuk babu alamun fara'a yana bin kowa da kallo dai_dai, zaro ido aunty tayi cikin tsananin razani ganin rigar dataga mutumin jiya datagani yafita da ita ajikin sadiq,ga kuma kansa yane da hirami, hannunsa duka biyun da safunan hannu, alhalin ba lokacin sanyi bane. dafe kanta tayi tana furta Kalmar hazbunallau wa'inimal wakil afili. tana addu'a aranta,Allah yasa abunda take zargi karya tabbata kokuma fatan idonta beganin mata daidaiba,kai bamata tunanin haka sediq ze aikata abunda take tunani,kilan jiyanne idonta beganinmata daidaiba. "Sadiq meyadawo dakai yau kuma?" Mommy tatambayeshi cikin tsananin firgici tana kallonsa. be'iya bata amsaba se faruq daya nuna mata da hannunsa. zama aunty tayi dabas akasa tamarasa mezata kira wannan bakon al'amarin me cike da rudu da tashin hankali acikinsa. Mommy ma zama tayi a gefen gado gumi na tsatstsafoma mata ako'ina najikinta, domin bata taba tunanin abun zejuye mata hakaba, bata taba tunanin wannan ranar tonan asirin zata zomataba arayuwarta, tarasa wanne sakaci tayi dakomai nata ya lalace, amma duk da haka zuciyarta bata sadudaba, takudircewa ranta agama wannan rikicin dakanta zata koma gurin boka tsidau,yasake mata sabon aiki. Faruq ma zama yayi akasa agefen aunty, haidar da zannurain kuwa basa gane komai akan abunda yake faruwa,kwakwalensu gabadaya sun toshe tsabar tararrabi sunma kasa magana, yanzu dama ba mommynsuce ta haifi mustapha ba, "to wacece ta haifesa?" tambayar da suhailat data daskare a tsugunne itama takeyiwa kanta kenan, shiru dakin yadauka kowa da tunanin dayakeyi acikin ransa,babu wanda yadamu da yanda sukaga sadiq,dominsu basusan komaiba akan fyaden da akeyi agidanba,hatta da daddy kuwa, mommy ce kadai tasani seshi meyin da faruq.
aunty ce tanisa cikin tsananin damuwa ta katse shirun tana duban daddy tace, "yaya kafada mana abunda yake faruwa kunsamu acikin duhu kaida faruq da aunty atika,kasanarma menene kuke boyewa da kuma gaskiyar al'amari akan abunda mu bamu saniba,sannan kuma tayaya Muhammad yazama badan aunty atikaba, wacece mahaifiyarsa to?." numfasawa daddy yayi yakalli su haidar da sadiq yace su zauna labarine me tsaho, babu musu dukansu suka yiwa kansu mazauni cikin son jin yanda daddy ze warwaremusu yanda abun yake, daddy ma raba mustapha yayi da jikinsa ya zaunar dashi akan gadon bayan yasamasa filo abayansa,cikin tsananin tausayawa ganin yanda numfashinsa yake fita dakyar tsabar tashin hankali. gyara zama daddy yayi yafara magana kamar haka:
aunty ce tanisa cikin tsananin damuwa ta katse shirun tana duban daddy tace, "yaya kafada mana abunda yake faruwa kunsamu acikin duhu kaida faruq da aunty atika,kasanarma menene kuke boyewa da kuma gaskiyar al'amari akan abunda mu bamu saniba,sannan kuma tayaya Muhammad yazama badan aunty atikaba, wacece mahaifiyarsa to?." numfasawa daddy yayi yakalli su haidar da sadiq yace su zauna labarine me tsaho, babu musu dukansu suka yiwa kansu mazauni cikin son jin yanda daddy ze warwaremusu yanda abun yake, daddy ma raba mustapha yayi da jikinsa ya zaunar dashi akan gadon bayan yasamasa filo abayansa,cikin tsananin tausayawa ganin yanda numfashinsa yake fita dakyar tsabar tashin hankali. gyara zama daddy yayi yafara magana kamar haka: