Sashe 65
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"shine wa Aunty Maryam" Aisha tatambayeta tana riketa ganin yadda duk ta burkice lokaci daya, mama baki sake take kallonta, danko sanda mijinta dan maman yarasu batayi irin wannan birkicewarba da gigicewa. "Dan Allah A'isha wanene shi wannan din danake ganinsa, koku bakwa ganinshine, kikalleshi zakiga kamarshi da miji na *MODIBBO*" "Danane" muryar daddy ta doki dodon kunnenta, dasauri ta kwace daga rikon da A'isha ta mata, taje gaban daddy cikin kuka tafara masa magana da fadin. "Danka, kuma?" To meyasa yake kama da mijina, hatta azurfar hannunsa irintace a hannun mijina harya mutu" "wai MARYAM, meke damunki ne, wanne mijinnaki kike magana akai, mufa bamugane mekike nufiba,gabadaya duk kinbi kin firgitamu" mama tatambayeta cikin dunbin al'ajabi, dan ita abun matar yafara bata tsoro harta fara tunanin ko matar tayi gamone. hannunta Aunty takama ganin duk falon sunkasa aiwatar da komai, hatta daddy kuwa daya tsaya kawai yana kallon matar. cikin lallami Aunty tafara mata magana. "Baiwar Allah, nasan ke musulmace kuma kinsan babu ta yadda za'ayi wanda yamutu yadawo, a kalamanki kuma naji kina fadin mijinnaki yarasu, kuma wannan danmune dashi mukazo garinnan, kinga babu tayanda za'ayi yazama mijin ki" "tabbas mijinannawa yarasu tun shekara fiye da talatin dasuka wuce, Amma kuma yau gashi naga wani me matukar kama dashi ai dole na shiga rudu" "baku da dane tare da mijinnaki?" Aunty tatambayeta cikin son tabbatar da abunda take zargi. kasa matar tayi dakanta idanunta na shatatatar da hawaye, tausayintane yacika su mama da iyalanta. cikin matsanancin kuka tace, "bani da ɗa ko ɗaya a duniyar nan" hawayene yaciko idanun Aunty, wani matsanancin tausayinta ne taji yashigeta lokaci ɗaya. shikanshi daddy seda kwallar tacika masa ido saboda yanda matar take kuka tamkar ranta zefita, ga dukkan alamu an sosa mata wani mikine a cikin ranta. Lokaci daya Mustapha daya kurawa matar ido kawai yana kallonta tun sanda tafara magana, yaji wani matsananci tausayinta gami da zazzafar kaunarta ta cika masa zuciya. rungume matar Aunty tayi tsam ajikinta, sedai batayi yunkurin rarrashintaba dan ta hanata kukan datakeyiba. tasan kukanne kadai ze rage mata radadin datakeji a cikin zuciyarta dan rashin haihuwa ba karamin abu tawaya bane ga dan adam. Maryam da aliyama hawayene kawai yake zuba a fuskarsa na tausayin matar, dan duk wani me imani idan yaga yadda matar take kuka seya zubar mata da hawaye. su mama kuwa mamakine yakamasu na matar, dan bata taɓa shiga irin wannan yanayinba akan rashin haihuwartata, saboda macece ita me tsananin tawakkali akan duk yadda rayuwa tazo mata,lokuta da damama mijinta yafita nuna damuwa akan rashin haihuwar tata. Daddy dayakejinsa tamkar mafarki yake, saboda duk wata alama dazata nuna masa matarnan mahaifiyar Mustapha ce ta bayyana agareshi. Saboda hujjojin dayake dasu kwarara guda biyu. Nafarko zancen azurfar dake hannun Mustapha datayi, na biyu kuma kukanta datakeyi yanzu yayi iri daya sak da wanda tayi lokacin data bashi Mustapha. sunayen Allah kawai yake kira danshima nutsuwarsa kokarin barinshi takeyi, haryanzu yakasa tabbatarwa da kansa ba mafarki yakeba, matar data bashi Mustapha itace tsaye agabansa. tattaro duk wata dauriyarsa yayi ya sarrafa harshensa dakyar yace, "kin taɓa haihuwa ne?" barin jikin Aunty tayi da sauri saboda yanda tambayar ta daki zuciyarta batare data dena kukan datakeba tace. "Ehhh!" tamkar mekoyan magana. mamakine yakama su mama domin su bata taɓa ce musu tataba haihuwaba, sun sandai tataba aure kafin ta auri baban Saddam. dauke kukan datakeyi tayi dif tamkar ba itaba, taci gaba da magana. "Nataba haihuwa na haifi yaro namiji amma yanzu bansaniba koyana raye koya mutu dan......" "Yazakiji idan nace miki wannan shine dannaki dakika taɓa haifa?" Daddy yakatseta da fadin haka cikin karfin zuciya yana nuna mata Mustapha. Ba ita kadaiba babu wanda kalaman daddy basu daki zuciyarsaba a falon, hatta Aunty kuwa da take da haske akan hakan. Maryam da aliya sunfi kowa shiga rudu, dama aliya itacan arude take banda zare idanu tana kallon mutane babu abunda takeyi. Maryam kuwa bata fahimtar komai, cikin duhu kawai kalaman daddy suke kara sanyata. Shikuwa gogan wato Mustapha wata muguwar faduwar gabace ta riskeshi shifa gani yakeyi abubuwan dasuke faruwa duka mafarki yakeyi ze iya farkawa wani lokacin. batasan sanda ta kama hannun daddy ba duka biyu tana maimaita kalmar. "daaanaaa...daaanaaa..." Tamkar wata mara fahimta. Abin gwanin ban tausayi. daddy danne wani abu daya darsu a zuciyarsa yayi yace, "ehh, dankine, duk da banji wani bayani akan kiba amma wasu hujjojina masu karfi sun tabbatar mun da kece matar dakika bani jariri, a wani dare akasar *Niger* a garin *Niamey*?" ilahirin jikintane yaɗauki kyarma gami da ɗauke war numfashinta na wasu sakanni a lokaci guda. Tabbas bazata taba manta wannan ranar data bayar da danta gudan jinintaba harta koma ga mahaliccinta. "Kidena mamaki, akan ikon Allah, domin buwayarsa ta wuce tunanin me tunani, shine me sauya al'amari a duk sanda yaso kuma a lokacin dayaso,kije ga danki da Ubangiji ya hadaku a lokacin da bakuyi tsammaniba dukanku." murmusawa daddy yayi yamaida kallo nsa ga Mustapha daya zama tamkar mutun mutumi yace. *"Son, come to your real mom"*
A matukar firgici ta juya ta kalli su mama, da mamaki yahanasu koda kwakkwaran motsi idanuwansu kawai suke bawa abinci suna ganin abun tamkar wasan kwaikwayo, banda haka daga mutane sun rakosu sekuma dansu yazama na wata. cikin sauri ta juya ta nufi inda Mustapha yake wanda ko motsawa beyiba daga zaunen dayake, zuciyarta na tsananin bugawa tasa hannunta dake rawa tafara balle botiran gaban rigar Mustapha, lumshe idansa yayi shima tasa zuciyar natsananta bugu tamkar zata faso kirjinsa ta fito, wanda har mahaifiyartasa tanajin bugun zuciyar tasa. singlet fara kar itace ta bayyana bayan ta gama balle botiran gaban rigar tasa, cikin zafinnama da karfin dabatasan tana dashiba ta yaga singlet din gida biyu, faffadan kirjinsa fari tass dashi me dauke da kwantaccen bakin gashi yabayyana. a kirjinsa daga ɓangaren dama ta kurawa ido, wani abune asaman nononsa baki. (rowa) abunka da farin mutum tafito tayi dodar. cikin fitar hayyaci saboda tsabar farinciki tarungume Mustapha ajikinta tana me fashewa da kukan murna. "babu shakka, kai danane nacikina, dukda nasan mafarki nakeyi,zan iya farkawa a kowanne lokaci amma hakan baze hanani nuna farincikinaba akan ganinka......." Zantuka tayi ta saki na farinciki cikin matsanancin kuka tamkar zata shide tana shafa sumar kansa. shikuwa Mustapha lokacin data rungumeshi wata doguwar ajiyar zuciya yasauke, yanajin wani shauki nabin dukkan jiki da ruhinsa, wata nutsuwa saya rasa a rayuwarsace yaji ta lullubeshi lokaci guda, ga tsananin kaunar matar data cika dukkan zuciyarsa. wasu sanyayan hawayene suka fara zuba akan kuncinsa..........✍️
*By*
*Zeey kumurya*
*4️⃣6️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
.............Yarasa a wacce duniya yake saboda, dadi,al'ajabi da mamaki. Tamkar ansauke masa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarsa haka yaji. farinciki mara misaltuwa ne yamamaye dukkan baƙin cikin dake cikin zuciyarsa. jikinsane yayi wani irin sanyi tubus hakan yasa yakasa tabuka komai, koda danyatsa daya yakasa motsawa. falon yayi tsit bakajin komai se sheshshekar kukan *ammi* wadda take kara manne Mustapha akirjinta, tanajin tamkar ta maidashi ciki saboda tsabar kauna. lumshe idonsa yayi yakara kwantar da kansa ajikinta yana shaƙar sassanyan kamshinta,wani dumi yaji yana shiga jikinsa, ajiyar zuciya yake sassaukewa akai_akai. Aliya da tsaiwa ta gagareta ta zube akan kujera cikin rawar murya ta dubi daddy dayaketa murmushi me nuni da yana cikin tsananin farin ciki tace. "Da..daddy.. tayaya tazama mom dinsa?..mommy fa?.." taku daddy yayi yazauna a kusa da ita har lokacin fuskarsa nadauke da murmushi, gefen kuncinta yashafa yace, "bazaki fuskanci komaiba, autar Aunty amma very soon nasan zakigane yanda abun yake nanbada jimawaba" yanda aliya ta kurawa daddy ido tana kallonshine yagane bata fuskantar meyake nufi. Aunty ma zama tayi a kusa da Maryam wadda ta kurawa su Mustapha ido, ko kiftawa batayi. share hawayen fuskarta Aunty tayi tare da kauda kanta daga kallon su Mustapha. Sosai tausayinsu yake ratsa zukatan kowa dake falon musamman ma ammi. A hankali mama tafara jan kafarta data mata nauyi tazo gaban daddy, cikin daukewar tunani tace masa. "Alhaji, dan Allah, kafitar damu daga cikin duhun dakuka samu, gabadaya kunsa zuciyoyinmu cikin tararrabi, tayaya danku dakukazo dashi zezama dan Maryama.?" "Labarine metsaho mama, dole semun zauna mun nutsu sanna zamu warware muku zare da abawa" "daddy yabata amsa cikin girmamawa. numfashi kawai ta fesar taja kafarta, ta karasa inda su Mustapha suke, tafarawa ammi magana cikin lallami danta fuskanci tahakane kawai zata iya barin wannan kukannata. "Haba, Maryam kukan na menene haka,kiyi hakuri kiyi shiru kibar kukan haka, kizo ki fitar damu daga cikin duhun dakika sanyamu" a hankali taraba jikinta dana Mustapha wanda ya wani manne mata, sekace karamin yaro. Kukan datakeyi ta dena se ajiyar zuciya take saukewa. Mustapha kuwa kasa yayi dakansa idanunsa a lumshe, beso tsohuwar ta katse masa samun nutsuwa da jindadin dayakeji dalilin jinsa a jikin mahaifiyarsaba sedai tsananin miskilancinsa baze bari kagane yanayin dayake cikiba. kama hannun ammi, mama tayi tazaunar da ita akan kujera ta fara share mata hawayen fuskarta cikin tsananin so da kaunarta. Tun ba yauba, ta fuskanci akwai wani abu dake damun zuciyar ammin, tana dannewane kawai, domin lokuta da dama tana taddata cikin zurfaffen tunani ko kuma cikin yanayi nadamuwa. kallon Mustapha kawai ammai takeyi takasa dauke idonta daga kansa, wani sanyi takeji yana ratsa zuciyarta. maida kallonta tayi ga mama tare da kama hannunta cikin sanyin murya tace, "mama dan Allah abunda yake faruwa gaske ne ba mafarki nake ba, wlh nakasa tabbatarwa da kaina." cikin tausayawa mama tace. "Gaske ne Maryama ba mafarki kikeba, azahiri komai dakika gani yake faruw...." Ai ammi bata bari mama takarashe zancen taba ta zube a kasa tana sujjada domin nuna godiyarta ga Ubangiji. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" daddy, aunty, mustapha, ammi suke furtawa a cikin zukatansu tamkar hadin baki cike da tsananin farin ciki. A'isha da kanwarta mesuna Halima tare da surukarsu wato zuhura, mazauni sukayiwa kansu dan sunga abun bana ƙarau bane, ga ƙafafuwansu duk sun sage saboda tsaiwa.............