Sashe 15
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda na nufi part dinnasa zuciyata take luguden bugu, tundaga falon kasa sihirtaccen kamshinsa ya ziyarci hancina lumshe idanuwanayi saboda dadinsa.sama nahau,shima dai kamshinnasane yamun sannu da zuwa.kan dinning na ajiye kwandon. Kofar dake kusa dakinshi na bude cikin sa'a kuwa nanne kitchen. Tsayawa nayi ina kallon kitchen din,Wanda ko wata amaryar albarka.sekace mace komai kwai a kitchen din. Ba karya ya hadu shima.Plates din na dakko seda nadaurayesu sannan na dawo falo.rasss,gabana yayanke ya fadi ganinshi zaune akan dinning yana latsa wayarsa. Karasawa nayi cikin matukar tsoronsa na ajiye plates din,gaishesa nayi amma ko kallona beyiba.tambayarsa nayi mezan saka masa nanma shiru kamar besan ina gurinba.tsayawa nayi ina kare masa kallo.kananun kayane ajikinsa,rigar farace Tass, se bakin wando.kayan sun masa kyau sosai,se yanzu naga tsananin kamarsa da mommy.gajiya nayi da tsaiwa nafara serving dinshi,ina kunkuni kasa_kasa. Komai zuba masa nake acikin plate ina tura masa gabansa. Na dakko farfesu zan zuba masa,nadan saci kallonsa. Idanuwansa tsam akaina yana jifana da wani irin kallo.nandanan jikina yafara rawa. Allah yagani tsoron idanuwansa nakeyi,saboda suna saukarmun da wani yanayi ajikina.ban Ankara kawai gani nayi spoon din yafadi daga hannuna,ferfesunne ya zube akan table din.cikin matukar tsoro na dago ina kallon gefen dayake. Gaba daya roman farfesun ya tsatstsallu a gaban farar rigarsa........✍️
*yauma ba editing,am sorry*🙏🙏
*By*
*zeey kumurya*
*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*
*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚
~*Free novel*~
*Bismillahirrahmanirrahim*
1️⃣3️⃣
...............Kallonta kawai ya tsaya yanayi cike da takaici da bakin ciki,bayan ta shigo ta samesa bata masa sallamaba, sannan tana ta masa surutun banza,yanzu kuma yana sauri zeje office tazo ta bata masa Riga,dolene ya hukunta yarinyarnan yau. Nikuwa jikina rawa yakamayi saboda matsanancin tsoro da razana,wlh bansan ya'akayi ludayin ya subce daga hannunaba.batare dana bari na kallesaba,na tsugunna akasa akan gwiwata idona tab da kwalla na fara magna. "Dan Allah Dan annabi,kayi hakuri wlh bansanib".... "Shut up!" Yadakamun wata uwar tsawa,wadda najita har tsakiyar kaina,hawayen dake makale a idonane yafara zuba,akan fuskata jikina yacigaba da rawa tamkar mazari. Kallonta kawai yakeyi,gata yarinya karama amma se shegen rashin jin tsiya,ga dan banzan tsoro. Inajin yanda idanuwamsa suke yawo ajikina,amma nakasa dago kaina na kallesa. Mikewa yayi bekaracemun komaiba,ajiyar zuciya na sauke,ina bin bayansa da kallo. Tashi nayi, nafara goge inda na zubar da romon,amma fa bandena kukaba. Yayi kusan 5 minutes sannan ya fito sanye da wasu kayan ajikinsa,hannunsa dauke da rigar dana bata masa.dafe kansa yayi aransa yace. "Ko a ina mommy ta samo wannan yarinyar, ita kam Sam kuka baya mata wahala,yanzu meyamata datake ta kuka,yana zaman zamansa zatasa masa ciwon kai. Ina rakubu tamkar almajira naji ya cillomun rigartasa a jikina, yayi hanyar fita batare dayace mun komaiba. Fahimtar danayi fita zeyi kuma ko break din beyiba, senaji ba dadi saboda nice sanadiyyar hakan. Cikin marairaicewa nace masa. "Dan Allah karka fita bakaci abincinnanba,idan ka tafi haka bazanji dadiba wlh." ni kaina seda na furta hakan naji wani iri. Kamar daga sama yaji muryarta tana rokonsa,tsayawa yayi cak, zuciyarsa na masa kuna shifa bayason mutum me yawan takura, dolene yasanar da mommy karta kara aiko masa yarinyarnan. Juyowa yayi karaf muka hada ido,da sauri nayi kasa da nawa idon saboda wata uwar harara daya wurgomun. Ahankali ya fara takowa zuwa dinning din,da hannu ya nunamun kofa alamun na fice masa. Sum_sum nafara tafiya rungume da rigarsa,duk da befadamunba amma nagane nufinsa na wanke masa. A falon kasa na tsaya ina maida numfashi,tare da daidaita nutsuwata. Saboda ina fita a haka kallo daya mutum zemun yagano zallar firgici da tsoro a tattare dani. Ninke rigarsa nayi wadda sassanyan kamshinta ya mamaye ni,a hijab dina na boyeta na nufi hanyar fita daga part dinnasa........
Kamar amafarki na hangi baaba talatu da'alamun fita zatayi saboda naga ta nufi get din tsakiya.wani sanyi naji araina, tafiya na farayi cikin sauri_sauri saboda na cimmata. "Baaba talatu" nakira sunanta bayan na matso kusa da ita. Juyowa tayi itama cikin mamaki tace, "maryam!" "Na'am baaba talatu ina kwana, kamo hannuna tayi batare data amsamun gaisuwataba,fara'a fal fuskarta. Tace, "maryam dake nake kwana nake tashi araina,kullum,inaso naganki amma badama." "Baaba to meyasa yanzu kikadena zuwa part din hajiya,nima inason ganinki amma bansan inda zansamekiba. "Hmmm,maryam,kenan ai se hajiya ta kiramu muke da damar shiga part dinta,amma ke kina da ikon dazaki iya fitowa kije ko'ina agidannan, kinga wancan dan karamin part din idan kika wuce na hajiya,to nanne part dinmu na yan'aiki idan kikazo zaki ganni." "Kai amma naji dadin ganinki baaba,insha Allah idannagama aikina zanzo anjima,nifa nayi tunanin ma bakya gidannan." Murmushi baaba talatu tayi tace, "banda abunki maryam,ina zani ai nanne gurin Neman abincina,yanzudai sauri nakeyi zanje dubiya, wata yar garinmuce datayi aure anan jiya tayi bari,shine zanje na dubota banason a shiga masallaci bandawoba. "Toh,shikenan baaba,sekin dawo,ki mata sannu,Allah yakiyaye." "Ameen maryam sena dawo" part dinmu nanufa zuciyata cike da murnar ganin baaba talatu dama akwai tambayoyin danakeson nayi mata.
Mommy bata falo,may be tana dakin ta. abunda yake kara dauremun kai da gidannan tunda nazo banga bako ko daya yazoba,kodayake bandade da zuwaba kila shiyasaka. Dakina nashiga na'ajiye masa rigarsa acikin cover da nufin idannaga aikin dazanyi sena wanke masa. Kitchen na shiga, kuku na tarar yana kokarin Dora lunch tun yanzu,dariya nayi masa nace, "kai emeka tun yanzu zaka Dora girki?" Cikin hausarsa yacemun madam karamace tasakashi aiki kafin ta fita. Jinjina kaina nayi,dannagane aunty suhailat yake nufi. Tsayawa nayi ina karewa kitchen din kallo narasama wanne kalan drinks zan hada, na iya drinks kala_kala,tunda shine sana'ar innata. amma bansaniba koze musu dadi. Yanke shawara nayi bari kawai na mata zobo,da kunun aya da lemon kwakwa. tunda na kware wajen yinsu,dan da azumi munayi a gidan umma nida saleemat. Cikin freezer na duba,naga akwai duk abunda zan bukata. Sedai banga aya da zobo ba a kitchen din,amma naga kwakwa da dabino da madara da sugar, dasu flavour. Tambayar emeka nayi amma yakasa gane me nake nufi, dole se dakin hajiya na shiga na tambayeta. Tacemun inje kitchen injirata zata saka akawomun,godiya na mata na koma kitchen na fara gogo kwakwar da zanyi lemo da ita. Mintuna kadan wata mata ta kawomun aya da zobon dayawa, wanke ayar nayi na jikata...... ( typing da wahala danayi muku yanda tayi lemon,da kunun ayar.)
Ina cikin aikina naji fitinannen kamshinsa ya mamayemun hancina, nandanan naji zuciyata ta hau luguden bugu Wanda narasa na menene aduk lokacin damukayi kusanci dashi senaji hakan a tattare dani,lekawa nayi ta window ina kallonsa,yana sanye cikin manyan kaya yanzu sabanin sanda na baroshi kananane,kayan sun matukar yimasa kyau,amma ba hula akansa, dakin mahaifiyarsa ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke na dawo na cigaba da aikina,araina ina tunanin tome yahanasa zuwa gurin aiki,kodai haryaje ya dawone? Babu amsa,wata zuciyar ta fadamun hakan. Se kusan karfe 2,nagama aikin drinks din saboda nayishi da yawa ko wanima zesha. A fridge nasakasu duka. Bayan na zubawa emeka nasa, ai kuwa nasha santi a gurinsa. Nidai dariya kawai natayi masa.
Daki na koma saboda inatajiran wadanda aunty suhailat tace,zamuyi aiki tare amma shiru_shiru basu zoba,ashe ni bansaniba a part dinsu sukayi aikin,dama kayan snacks ne,sukayi mata. Wanka nayi tare da dauro alwala nayi sallah. kwanciya nayi da nufin nadan huta. banmasan sanda bacci ya daukeniba.....
Tunda ta fice daga falon ya bita da kallo ta gefen ido,besan sanda murmushi ya subce masaba saboda yanda takeyin komai nata a tsorace,kuma da yarinta. Kadan ya taba breakfast din ya mike ya koma dakinsa,fasa zuwa office dinma yayi gaba daya saboda lokaci ya kure,gashi yau Friday, 12 yake baro office saboda masallacin juma'a. Aiki yayi a laptop dinsa,sannan ya mike yayi wanka yayi shirin zuwa masallaci. Seya fara zuwa ya gaida mommy sannan zewuce masallacin. Lokacin dayashiga part din mommy,yana kallonta ta gefen ido tana lekensa ta window, wani murmushi yayi Wanda shikadai yasan ma'anarsa,ya shige dakin mahaifiyarsa.......
Suhailat se da 2 ta wuce,ta dawo gida. A matukar gajiye ta dawo dama ita langwaice batason aikin wahala,zaman lectures ma wahala ne agurinta. wanka tayi ta shirya cikin wani hadadden Dubai less.dinkin Riga da skirt ne,yamata dass a jikinta. Ta kafa daurinta tayi kyau sosai,tamkar ka saceta. Suhailat irin matannanne dakana ganinsu zakaga tsantsar kyawunsu. Taci turaruka kala_kala setashin kamshi takeyi. Waya sukayi da kamal yasanar mata yana kan hanya. Abinci taci kadan kafin yakaraso. Amma zuciyartarfa cike take da tsoron yayanta. A kan zuwan kamal Tasan dai idan tace masa abokin karatuntane,ze yarda. Dakin mommy ta nufa tasanar mata kamal yanakan hanya. Mommy macece me son ra'ayin yayanta dabin abunda sukeso. Hakan yasa batayi yunkurin hana kamal zuwaba, koda yakema hakan bakomai bane agurinsu,dan abokin yarka yakawo mata ziyara gida.kuma tayarda da abunda suhailat tace mata akan,kamal abokin karatuntane.....
Kamal shikadai yazo gidan su suhailat,kuma wannan shine zuwansa na farko gidan. Bin gidan yakeyi da kallo yana jinjina yanda aka kashewa gidan kudi, tabbas dolene, yabi shawarar abokinsa, yasan yanda yayi ya auri suhailat kodan yaci kudin babanta. Sema yanzu dayazo gidannasu,yakara jin kwadayin aurannata. Murmushi yayi yana kissima abubuwa da yawa aransa,kafin yafara Neman auran suhailat dolene yafara kawar da *almustapha sulaiman menasara* daga doron duniya,domin idan har yana raye suhailat baza tataba auransaba. Yadade da sanin tarihin soyayyar mustapha azuciyar suhailat, wani murmushin yakara saki,akaro na biyu........
Tarba sosai kamal yasamu daga gurin suhailat,babban falon bakin daddy suhailat ta kaishi bayan ta taryoshi da kanta.