← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 128

Sashe 6

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya mukayi me dan nisa,sannan muka shigo wata unguwa,me matukar kyau da tsari.yanayin layikan unguwarma kadai abun burgewane.kowanne layi da get dinsa,gashi kowanne gida andankarashi wannan yana wane wannan, wannan yana wane wannan. Araina nake cewa dama da irin wannan unguwannin a garin kano,wani layi naga mun karya kwana munshiga get dinsa.wani makeken gida nagani a hannun damana,Wanda tunda nashigo unguwar banga me kyau da girmansa da tsaruwarsaba.sakar baki nayi ina kallonsa,ko wanene me wannan dankareren gidan oho,kai wannan sedai gidan wani babban dan siyasane.wannan gida haka sekace akasar turai.get din farko na gidan muka wuce,tafiya kadan na kara ganin wani get din agaba.Wanda anan drivan hajiya ya fara horn.rasss,gabana yayanke ya fadi,badai wannan gidan za'akaini aikatauba,shikenan lami ta saidani,gidan 'yan yankankai akakawoni.tunanina ya tsayane daidai lokacin daka wangalemana kofar get din gidan,me matukar girma.harabar gidan kanta katuwace ta isa a gina kamar gidanmu uku acikinta,wannan ma hasashenane kawai amma banga karshentaba.parking space muka nufa,Wanda aka lullubeshi da wata runfa,motocine dayawa a gurin.nidai sakar baki nayi ina kallon ikon Allah.ga wasu mutane datunda muka shigo gidan nake ganinsu,masu korayen kaya,suna shawagi kamar dai security ne.kama hannuna matar tayi tana murmushi. "Maryam mun iso gidanfa,seki fito mu nufi ciki.wani gwauron numfashi na sauke,ina dubanta.bude murfin motar tayi bayan ta sakarmin hannuna,bin bayanta nayi nima na fice Daga motar.ina rungume da 'yan kayana.

Bansan tayaya zan misalta kyawu da tsaruwar gidanba,tare kuma da girmansa.part,part ne da yawa agidan,tsakanin kowanne da dan'uwansa akwai tafiya.mun wuce na1,na 2.na uku naga ta nufa,Wanda yafi duka wadanda muka wuce kyau da tsaruwa.

Matattakala muka fara takawa,wadda take abakin part din,hawa hudu muka iso bakin kofar part din,wani Abu naga hajiya ta danna Wanda bansan komeneneba.mintuna kadan wata mata da bazata wuce shekara talatinba tazo ta bude mana kofar.aljannar duniya na fada lokacin Dana ganni acikin wani hadadden falo,Wanda ko'a mafarki bantaba tunanin shigarsaba a rayuwata.lallai kudi yana gurin masu kudi.ga wani kamshi da sanyin a.c daya ziyarceni a lokaci guda.ban boye kauyancinaba na fara bin ko'ina na falon da kallo.sannu da zuwa matar tayiwa hajiya.jagorarmu ta farayi da'alama ita zata kaimu wajen matar gidan.wata kofa muka kara shiga,nanma wani falonne Wanda yafi na farko haduwa.gaba daya na manta da abunda ya kawoni gidan,na manta da wata fargaba.abinci kawai nake bawa idanuwana.

Matattakalar bene,naga matar ta nufa damu.nidai kawai binsu nakeyi abaya zugwi_zugwi.se tuntube nake tayi.hannuna hajiya ta kama ganin yanda nakeyi.ita a tunaninta tsoro ne ya kamani. "Kikwantar da hankalinki kinji 'yata,babu abunda zefaru dake,tunda naganki naga kin shiga raina,dabadan hajiya ta tsanantaba dani zan rikeki a wajena.saboda kin burgeni gaki da nutsuwa.babu abunda zefaru dake agidannan,kisaki jikinki kinji.gyada mata kai kawai nayi,amma zuciyata na bugawa.wani matsanancin tsorone naji ya lullubeni.addu'a nafara karantowa acikin zuciyata ta Neman taimakon Allah,da tsarinsa.

Kafin mu shiga kofar falon seda muka jira aka bude mana,wowww na furta acikin zuciyata saboda girma da tsaruwar falon,babu wani tarkace acikinsa,amma falon ya matukar haduwa fiye da wadanda muka wuce na baya.kalle kallena nakeyi bansan mun iso gaban mutanen gidanba,seda hajiya ta taboni sannan na dawo hankalina,zubewa hajiya tayi akasan carpet, din dake malale a falon.nima tsugunnawa nayi kaina a kasa,araina nace lallai gaba da gabanta.Hajiyace ta fara magana cikin girmamawa,"Hajiya barka da hutawa,dafatan kina cikin koshin lafiya,dafatan na sameku lafiya.wata murya me cike da aji da izza naji tace"lafiya kalau lami,kin cika alkawari dafatan yarinyar ta cika duka sharadan Dana lissafo miki."eh hajiya gaba daya ta cika,babu matsalar komai.maida dubanta matar gidan tayi kaina tacemun "yan mata yaya sunanki.se alokacin na dago na dubeta kai masha Allah,ta dace da gidannan gaskiya,kyakkyawace sekace India,tayi ado cikin wani rantsatstsen less,koda bansaniba amma babu shakka kunnanta da hannuwanta da wuyanta daham,saboda yanda suke daukar ido. "maryam" na furta a hankali, saboda tsareni da tayi da ido tana kallona.kawar da kaina nayi gefe,kyawawan samari guda hudu idanuwana sukayi tozali dasu,tamkar babu su a falon kowannensu yanata latsa wayarsa.kamarsu daya gaba dayansu dayane kawai ya banbanta dasu.sunkuyar da kaina nayi saboda wani mugun kallo da daya Daga cikinsu ya wurgomun. Muryar hajiyar gidan naji tana cewa"shikenan lami,zaki iya wucewa zan miki transfer zuwa anjima,sauran abubuwan kuma zamu tattauna awaya. "To hajjaju makkatu,nagode Allah ya kara girma da daukaka da arziki Mara yankewa,na barki lafiya. Da ameen kawai ta amsa mata.mikewa hajiya,danaji itama ankirata da lami tayi,tayi mata sallama.dafa kaina tayi "to maryam Nina wuce,semun sake haduwa. Kawai senaji kwalla tacikomun idanuwana,senaji banaso tatafi ta barni domin bansan taya zanfara rayuwa awannan gidanba.gyada mata kai kawai nayi,har lokacin kaina yana kasa.ina wasa da yatsun hannuna.

Bayan tafice daga falon hajiyar gidan,ta umarci wadda ta mana jagora datakaini dakin dazan zauna.tashi nayi nabi bayanta.Acikin falon ta nunamun dakin dazan zauna.abude yake hakan yasa tura kofar dakin nayi kawai na shige.katon dakine me dauke da saitin kayan gado masu tsananin kyau da daukar ido.tsayawa nayi ina karewa dakin kallo,ko ina tsaf dashi tamkar da mutum aciki."Yanzu ni zan kwana a wannan dakin nikadai,a wannan dakin zanci gaba da rayuwata,dakin da ko rabinsa a kyau bantaba tunanin shigarsaba,Jan kafata nayi na karasa bakin gadon,na zauna.katifar dake kan gadonma ita kanta ta dabance.ajiye kayana nayi.ina cigaba da karewa dakin kallo tare da sake_sake iri iri araina,da sabuwar rayuwar dazan fara.

Kiran sallar magriba ne ya tasheni daga karanta wasikar jakin danakeyi.wata kofa Dana gani acikin dakin na nufa wadda nake kyautata zaton ta bayice.ina budewa kuwa naga toilet ne.shima toilet seda nayi kauyanci araina nace sekace daki shima.wasu abubuwan dabantaba ganinsuba nagani,banyi karambanin taba komaiba,famfo kawai na kunna nayi alwala nafito.na idar da sallah,kenan ina addu'oina matar data kawoni dakin ta shigo da sallamarta.amsa mata nayi se alokacin nasamu damar gaisheta amsamun tayi fuskarta dauke da murmushi. Tace"Kizo inji hajiya tanason ganinki. " Mikewa nayi nayi bayanta muka fice daga dakin.kamar dazu yanzumma ita da yarantane,sedai yanzu naga wata mace,tana kwance akan cinyar hajiyan ita kuma tana shafa kanta,tana mata magana.agabansu naje na durkusa kaina a kasa nace "hajiya gani. Dasauri naga budurwar dake kwance akan cinyarta ta mike zaune.........✍️

*By*
*zeey kumurya*
*ABUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

*Bismillahirrahmanirrahim*

0️⃣6️⃣

............Nunani ta farayi da hannunta tana jifana da wani mugun kallo"mommy wannance me aikin. shafa kumatunta hajiyan tayi "eh,itace daughter."Ammafa mommy senaga kamar bazata iya aikinba,kalletafa sanyinta yayi yawa.jifa yanda take tafiya kamar bata da laka. " hmmm,daughter kenan rabu da 'yayan talakawannan idan sunason kudi zagewa sukeyi,suyi aiki.tabe baki tayi bata kara cewa komaiba,amma se kallona takeyi.nidai ina durkushe ina dubansu. Maido da dubanta hajiya tayi gareni ta faramun magana. "Maryam kikacemun sunanki ko? "eh hajiya. "ohk, Aikin dazakiyi agidannan iya part dinnanne,kawai.anjima za'azo a miki bayanin aikin daza kidingayi.ina fata bazan samu matsala dakeba,kinga wadannan,ta nunamun duka matasan dake dakin.ahankali na dago ina dubansu.taci gaba da magana.dukansu 'yayanane,idan sukaje aiki suka dawo anan suke zama,saboda haka kome suka saki kiyi,banason bacin ransu kokadan dan haka kibisu sau da kafa. "Insha Allah hajiya zankiyaye. nafada cikin sanyin murya ta."zaki iya komawa,dakinki.harna mike sekuma naga dacewar naje nagaida 'yayannata. Gabansu naje na durkusa nace. "ina wuninku."Daga Wanda yadago ya wurgamun kallon banza,seme bina da harara,da kallon tsana.guda dayane Wanda kamarsa ta bambamta danasu.ya ajiye wayar hannunsa,fuskarsa dauke da fara'a ya amsamun gaisuwata.harda 'yan tambayoyi yamun.tare damun fatan nasara arayuwata.naji dadi sosai yanda be kyamaceniba kamar sauran 'yan uwansa.mikewa nayi jikina a matukar sanyaye na fara tafiya.karaf idona ya hadu Dana wannan budurwar.wani kallon tsana naga tana jifana dashi se wani yamutsa fuska takeyi tamkar taga kashi. "Jibeta yanda take tafiya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki.muryar budurwar na tsinkayo tana fadar haka.kwashewa da dariya naji sunyi,"to kekuwa suhailat bataci ta koshiba ai dole kiganta haka.da sauri na karasa dakin danasauka,dan bazance nawaba.idona ya cicciko da kwalla.saboda na fuskanci mutanennan basusan darajar dan Adam.yanzu haka zanyi rayuwa acikinsu.tsanata da kyamata kawai nake hangowa a atattare dasu,nabar kyarar gwaggo Ashe nanma zan tadda wata.hawayene yafara zubowa Daga idanuwana,na tausayin rayuwata.

Turo kofar dakin akayi,da sauri na dago ina kallo bakin kofar.wata 'yar tsohuwace domin ko tantama banayi tayi jika dani.sallama tayi na'amsa mata,ina goge hawayen fuskata.tsugunnawa nayi cikin girmamawa na gaisheta.murmushi tamun,tana amsamun gaisuwata.kamo hannuna tayi muka zauna a bakin gado."yarinya yaya sunanki. "Sunana maryam. "Allah sarki,maryama ta baban gida,.ni kuma sunana talatu nice babba a masu aikin gidannan,nice wadda hajiya ta turo in miki bayanin aikin dazakiyi amma kafin sannan,idan bazaki damuba inason jin labarinki,wato tarihin rayuwarki. Dasauri na dago ina mata kallon mamaki. "mamaki kikeyi ko 'yannan,na shigo na tarar dake kina kuka,Daga gani dole akayi miki a aikinnan,inason jin labarin kine domin insan ta inda zan iya taimakonki.
shiru nayi ina juya maganganunta araina,banason tuno abubuwan da suka faru a baya arayuwata,amma kuma a kallo daya danayiwa matar ta shiga raina,kuma bazan iya mata musuba,kodan kasancewarta babbace. " Baaba,labarina yanada yawa amma zan takaita inbakishi. "Yawwa yarinya,dafatan bantakuramikiba,inason sanin wani abune Daga gareki,domin nima inason sanar dake wani Abu game da gidannan.numfashi naja tare da gyara zama na farabawa baaba talatu tabarina.

***************

"Sunana maryam,na tashi na ganni a hannun kakata,wadda ake kira inna.a unguwar darmanawa dake nan kano.innata itace ta haifi mahaifiyata.ita kuma mahaifiyata ta rasune a wajen haihuwata hakan yasa bansantaba.innata kawai nasani.mahaifina kuma tunda cikina,inna tacemun aka nemeshi aka rasa.dama badan kasarnan bane dan Niger ne.bashi da kowa yazo kasarnan neman kudi.anan cikin garin kano yake sana'arsa.innata tacemun,itadai batasan sanda suka fara soyayya da mahaifiyata ba,kawaidai da mahaifinta yace ta fito da miji tace shitakeso,duk da tarin masoyan datake dasu,domin mahaifiyata kyakkyawace.kyawun asalin Fulani.
Chapter 6 · 0% Book details