Sashe 74
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da sallama suka shiga, saleemat dake kitchen ta amsa musu, tsayawa sukayi a tsakar gida bayan kamar 2 minutes saleemat ta fito. Da fara'a dauke akan fuskarta tace, "sannunku da zuwa" duk da bata wayesuba. "Ku shigo tana ciki" Aunty tace, " barshi nanma yayi muna sauri ne" "to bari namata magana" saleemat ta fadi haka tana nufar dakin umma, sanar mata tayi tayi baƙi kuma sunce suna saurine. Biyo bayan saleemat umma tayi, da fara'a itama tayiwa su aunty sannu da zuwa, tare da kaisu falo. Bayan sun zauna sun gaisa umma tace. "Saidai banganekuba" murmushi Aunty tayi tace, "dama bakisanmu, nazo nanne makotanku naga gidan a kulle, shine nace bari nazo natambaya ko kwatancenne banganeba" umma tace, "gidanwa kuke nema" "gidan wata gwaggo wadda take rikon yarinya Maryam" umma na mamakin abunda yakawo wadannan kyawawan mutane, masu tattare da kamala gidan gwaggo, duk da sunsha hijabansu amma kallo ɗaya zakasamu kasan a daga gidan hutu suke, tace. "Eh, nanne kuwa bakuyi batan kaiba, saidai yanzu haka tana asibiti batada lafiya" "subhanallahi meyasameta" Aunty tatambaya cikin razani. atakaice umma ta musu bayani. Cikin jimantawa Aunty tace, "Allah Sarki, Allah yabata lafiya, yakiyaye gaba, sukuma wadanda sukayi Allah yatoni asirinsu" "Ameen" umma da aliya suka amsa a tare. "Tana wanne asibitin yanzu" Aunty ta tambaya. "Aminu Kano" daidai lokacin saleemat ta shigo dakin hannunta dauke da ruwa, godiya su Aunty suka mata, sannan suka kara gaisawa. Aunty ce tayiwa umma bayanin abunda ke tafe dasu atakaice. kafin umma tayi magana, saleemat cike da mamaki tace. "Maryam ditace take da aure yanzu?" "Ehh ita, kinsan iko na Ubangiji babu yadda baya canza al'amari, mu mutane muna namune Allah natasa, rabon aurennasune yakai Maryam aikatau gidan yaya" ganin yanda suka cika da mamaki, umma takara musu bayani sosai yanda zasu fuskanta karsu dauki abun da wata manufa. sun dan jima a gidan suna tattaunawa akan al'amarin seda sukayi sallar azahar sannan aunty suka tafi da saleemat asibiti dubo gwaggo. Lokacin dasukaje gwaggo tana duniyar bacci. wadda ke zaune a gurinta Aunty tayiwa bayaninsu kansu takuma tabbatar mata zasu dawo nan bada jimawaba harda Maryam din, seda Aunty ta cikasu da Alkhairi sannan suka musu sallama suka tafi. seda ta biya ta dauko suhailat bayan ta sallami matar dake zaune da ita, se bayan la'asar dai ta komo gidan daddy........
*JOS*
Girke_girke mukayi, munsha aiki gaskiya. duk wannan hidimar akan yarinyar gidan dazata dawone wadda kullum senaji ammi da Aunty zuhura, da mama sunyi zancenta wai ita umaimah. daga jin yadda suke zancenta suna matukar ji da ita. Bayan mungama aikin nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga kalar dark pink, anmata adon baki da wasu fulawoyi a gaban rigar. faka gashin kaina dayasha gyara nayi ya sauka har gadon bayana, tattareshi nayi na cusa a cikin ribbom sannan na dakko wata bakar hula nasaka. dankunne fashion masu kyau nasaka tare da agogo da zobe. kwalli kawai nasaka a idona se white lipstick danasawa lips dina. humra me dadin kamshi na shafa a jikina, se wani turare na fesawa me sanyi da dadin kamshi. seya hadu yabada wani kamshi me dadin gaske. Kallon kaina nayi a mudubin dakin ammi, nikaina nasan nayi kyau, fatata tayi haske sosai jikina kuma ya murmure, tona samu kwanciyar hankalin zuciya tunda na mallaki *heartbeat* dina.
Maryam tana daki tana shiryawa umaimah ta dawo gidan, cike da farin ciki ahalin gidan suka tarbeta kowa na murna da farincikin dawowarta musamman ammi. Itama anata bangaren umaimah cike take da murnar dawowarta gida tayi missing dinsu sosai musammanma amminta, harsuka gama tarbe_tarbenta Maryam tana daki batamasan sunayiba. lokacin da Maryam ta gama shirinta ta shigo umaimah tana daki tana wanka. kusa da ammi naje na zauna bayan na musu sannu da gida. wayar Aunty na dauka nafarayin game, ita kuma suna hira da Aunty zuhura da mama. Bayan kamar 20 minutes umaimah ta fito daga dakinta karaf idonta yasauka akan Maryam, da dunbin mamaki take kallonta, danbatasan da zaman Maryam a gidanba. Aranta tace, "to wannan yarinyarfa, kodai daga Saudiyyan da Ammi taje tataho da ita?" a wani bangaren na zuciyarta kuwa kishi ne da kyashi ya turniketa na ganin kyawun Maryam, ita macece dabatasan taga anfita kyau, sekuma gashi yau taga wadda tafita komai da komai a cikin gidansu. hade rai tayi cike da hassada ta dauke kallonta daga kan maryam, kusa da mama taje ta zauna tana wani narke mata ajiki tana zuba mata shagwaba. se'alokacin Maryam tasan da zuwanta falon, dago kai tayi ta kalleta, mamakine yacikata ganinta katuwace amma take wannan sangartar, kallo daya Maryam ta mata ta dauke kanta tacigaba da game dinta. Ammi ce ta dubi Maryam tace, "ɗiyata ga autatah fa, danace miki tayi tafiya Abuja. kakaro fara'a Maryam tayi cikin sanyin muryarta tace, "sannu yakike" fuskarta babu fara'a tace. "Lafiya kalau" bankara cemata komaiba itama haka, a gani ɗaya dana mata naji ni sam batamunba, ita kam umaimah bakin ciki ne yakara turniketa dataji Muryar Maryam me sanyi da zaki, "yarinyar komai ta hada ga kyau ga zakin murya, salon yanda take maganama kawai abun burgewane" umaimah ta fadi haka a ranta cikin kyashi. Daidai lokacin Saddam da Mustapha suka shigo falon bayan sunyi sallama, kasancewar yau juma'a da wuri suke dawowa daga kasuwa. kamar ance ta kalli kofa idanunta ya sauka akan Mustapha. wani mayen kallo tabi mustapha'n dashi without control her self, kallonsa take tamkar zata lashesa............✍️
*By*
*zeey kumurya*
*5️⃣3️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
............. Umaimah har wani zunkuɗowa take daga kan kujera tana sakin baki da hanci tana binshi da mayen kallo, Saddam da zuhura tare da Maryam ne suka lura da kallon da take masan, ammi kuwa hankalinta yana kan ɗanta bata luraba. wani kishine yazo ya turnikemun zuciya irin me dacinnan, nibanmasan haka kishin yakeba dan bantaba jin na Aunty suhailat irin hakaba, yanda take kallonsa kamar idonta ze cire, tabe Bakina nayi nadauke kaina daga kallonta zuciyata namun kuna. Ita kuwa zuhura murmushi tayi dantasan za'ayi haka. Saddam ma murmushin yayi yakau da kansa daga kallon Umaimah. Mustapha seda yagaida amminsa da mama sannan ya zauna a kusa da Maryam, dan babu wani gurin zama da yay saura a falon senan, kuma shima ya lura da kallon da umaimah take masa. Lumshe idonsa yayi saboda kamshin Maryam daya shaka kamshin ya masa daɗi sosai. Ita kuwa Maryam bata rai tayi hartana turo dan karamin bakinta gaba batasaniba saboda zafin kishi. A hankali ya bude idanunnasa ya kalli Maryam ta gefen ido. Umaimah wadda takasa dauke idonta daga kansa sekara sakar baki da hanci take tana kallonsa, a ranta tace. "Wowww, wowww amma guy dinnan ya haɗu iya haɗuwa, yatafi da imanina, amma daga gani brother din yarinyarnanne" dan ita kama taga Maryam da Mustapha sun mata. danna wayar ammi kawai nake amma bansan menake dannawaba tunda yazauna a kusa dani nanemi nutsuwata na rasa, kawai daurewa nake ga kamshinsa gaba-daya ya cikani.
kara kallonta nayi naga har lokacin bata dauke idonta daga kansaba, sonake na kalleshi naga ko shima ita yake kallo amma nakasa. Mamace tatabo umaimah tana cemata. "Ke! Mekike kallo hakane?" Ajiyar zuciya umaimah ta saki ta juyo ta kalli mama a hankali tace, "mama suwaye wadannan wai? daga ina suke?" mama tace. "Bakin amminki ne" umaimah na far da ido tace, "amma suna da kyau sosai kamar ammin, musammanma namijin yafi kyau ga muryarsa me dadi" cikin tsokana mama tace, "yau wacce rana umaimah ta yabi wani ɗa namiji arayuwarta" tana satar kallon Mustapha tace, "mama ai yakai a yabeshinne, wlh bantaba ganin namijin daya mun kyau kamarshifa, guy ɗinfa yayi mama" murmushi kawai mama tayi batace komaiba. Maida kallonta tayi ga yayanta tace. "Yaya Saddam ina yini" "lafiya kalau sisina, aitunda nashigo nakeson na miki magana naga kunata sirri da mama senace bari najira ku gama." Dariya tayi tace, "kasan tsakanina da tsohuwarnan da amana" "hakane yar lelen mama, kindawo lafiya" "lafiya kalau yayana" maida kallonta tayi ga Mustapha tana wani fari a kokarinta nata dauki hankalinsa tace, "ina yini" sarai yasan dashi take amma ya mata banza tamkar bejiba. Ammice tace dashi, "NOOR ana gaisheka" batare daya kalletaba yace. "Lafiya" atakaice. hira suka shiga yi dukansu amma banda Maryam da Mustapha dasukayi dif tamkar basa falon, umaimah se wani iyayi take idan zatayi magana tana wani fari da ido, wanda takeyi danshi bemasan tana yiba. Bayan sunyi sallar la'asar ammi zata kaiwa Mustapha abinci, umaimah ta karba ta kai masa har daki tana wani yaya NOOR, gabadaya tabi ta susuce dataga mustapha. Shiko mustapha haka kawai yaji yarinyar bata masaba dan daga ganinta zatayi rawar kai, data kawo masa abincinma hade ransa yayi, a niyyar umaimah ta zauna suyi hira dashi amma ganin ba fuska seta fice badan tasoba. Yana gama cin abincin ya fice daga gidan.