Sashe 106
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da yamma bayan sallar la'asar mustapha da daddy ne suka fito cikin shirinsu zasu gidan gwaggo domin gaisheta, da mustapha yacewa daddy ze jene, shine daddy'n yace suje tare shima ya gaishenta ya kuma duba jikinta, seda suka kira Aunty tayiwa driver'n Daddy kwatance gidan sannan suka tafi. basusha wahalar gane kwatancen layinba tunda babu nisa da titi kuma wajen firamare ne, direban yasan gurin, gidannedai seda suka tambaya aka nuna musu. A Kofar gidan gwaggo direban ya faka motar kasancewar motar tana shiga har layin. fitowa sukayi daga motar mustapha ya shiga bin layin da kallo, dan wannan shine karo na farko daya zuwa irin wannan unguwar a rayuwarsa, abokinsa lukmanne ya fado masa rai, ya manta rabon da suyi waya dashi gashi yanzu yayi aure baya unguwar gandun sarki, daya biya ta gidansu sun gaisa. yaro Daddy ya samu ya turashi gidan gwaggo dan a sanarmata da zuwansu, gwaggo na zaune a tsakar gida akan tabarma ita da asabe wadda take zaune a gurinta yaron ya shigo yayi sallama, su gwaggo suka amsa masa. Yaron yace "wai ana sallama da gwaggo" gwaggo tace, "Ni kuma dannan suwaye?" Yace "wasu ne a mota me kyau su biyu suma masu kyau" gwaggo tace, "jeka tambayo kace suwaye" yaron ya fita bajimawa yadawo yace, "wai yace Alhaji mainasara ne da.." gwaggo ta kwalalo ido waje ta katse yaron da sauri tace, "wakace yaro?" Yaron ya kuma cewa "Alhaji mainasa" gwaggo ta dubi asabe da dunbin mamaki a fuskarta tace "asabe! Kinji wa akace yana sallama, wai Alhaji mainasara ko kunnenane beji daidaiba?" Asabe tace, "a'a gwaggo shi akace" gwaggo ta dubi yaro tace, "jeka maza kace ya shigo" ta juyo ga asabe tace, "dakko musu wannan ƙatuwar daddumarnan sabuwa ki shimfida musu" asabe ta mike da sauri ta dakko dardumar ta shinfida, daidai lokacin su Daddy sukayi sallama. gwaggo ta amsa musu tana washe gajiyayyun haƙoranta tana binsu da kallo cikin tsananin farin ciki tace "sannunku da zuwa Alhaji, dafatan kunzo lafiya?" Daddy ya zauna da fara'a yace "lafiya kalau baaba ina wuni" gwaggo kamar zata ɗauki Daddy ta ɗora a cinya yanda take acting tace "lafiya kalau Alhaji, ya iyali?" Mustapha dai kawai kallonta yake ta ƙasan ido, a ganin farko daya mata a rayuwarsa yaji sam matar bata masaba" bayan sun gama gaisawa da daddy kamar wanday akaiwa dole yace "ina yini" gwaggo ta kalleshi da Fara'a tace "lafiya kalau dannan" daga haka be ƙara cewa komaiba, asabe ta gaishe da daddy da mustapha suka amsa mata. gwaggo ta dubeta tana kunce hannun zaninta tace "ungo ɗari biyu nan kisiyo musu lemo da ruwa, bari in kawo muku abinci" Daddy ya dakatar da ita da faɗin, "A'a baaba ki barshi, a koshe muke mukam" gwaggo tace "to ai ko ruwa kwasha Alhaji" Daddy yace "ki barshi baaba mungode, ya jikinnaki kuwa" gwaggo tana maida 200 ɗinta cikin zani tace, "jiki ai yayi sauƙi Alhamdulillah" Daddy yace "Masha Allah, Allah yakara lafiya, ai naso zuwa tun wancan lokacin to sai kuma wani uzuri ya tsaidani" gwaggo tace "bakomai ai Alhaji, a hakanma Nagode ai naga saƙo gurin Hajiya(Aunty) nagode" Daddy yace "babu komai, sai kuma maganar yarinya Maryam dana aurar da ita batare da neman izni ko yardarku ba, da....." Gwaggo ta katseshi da sauri da faɗin "haba alhaji, babu komai ai, kaima uban Maryam ne kana da iko akanta, ka kai da zartar da duk wani hukunci dakaso, mune da godiya ai dabaka kyamacemuba ha haɗa zuri'a damu" Daddy yayi murmushi ya mata Godiya, shidai mustapha yayi tsit kamar babu shi a gurin. Gwaggo se sakarwa daddy zantuka takeyi, shi kuma kawai sedai ya bita da murmushi da eh'ko A'a, ganin ƙarfe shida ta gabato Daddy yacewa gwaggo su zasu wuce, nuna mata Mustapha yayi yace "ga sirikinnakifa, shine mijin Maryam ɗin" gwaggo ta gwalalo ido waje tana kallon Mustapha, aranta tace _"yanzu wannan mutumin me kama da Balarabe shine mijin maryam"_ jinjina kai tayi tace, "Masha Allah, ɗana ashema kaine sirikinnawa to Allah ya baku zaman lafiya, dafatan dai baka fuskantar wata matsala daga gurinta?" Mustapha ya gyada mata kai kawai. Tace "aidama nasan Maryama yarinyar kirki ce gata da biyayya da hankali, bata da wata matsala ko...." maganar gwaggo ta makale lokacin dataga uban kuɗin da Daddy ya fito dasu daga alhajinsa ya ajiye a gabanta.Gwaggo ta wangale bakinta tana duban Daddy dake cewa, "bamu samu mun taho da komai ba ga wannan a sai goro" gwaggo ta haɗiye wani yawu tace, "Alhaji angode Allah yasaka da Alkhairi, ya raya zuri'a yajikan mahaifa, Allah ya ƙara buɗi" Daddy ya amsa da "Amin" yana bin bayan mustapha wanda tuni yayi gaba, gwaggo har ƙofar gida ta bisu babu ko lullubin kai se ɗan kwali tana zuba musu Godiya, mustapha yana jingine jikin motar yana latsa wayarsa, saleemat ce ta fito daga gidansu hannunta riƙe da leda zata kaiwa wata kawarta a tamfar anko, kallon su Daddy take cike da mamaki ganinsu a ƙofar gidansu, gasu ƴan gayu dasu wanda kallo ɗaya zaka musu kasan Naira ta zauna a gurin su, bata lura da gwaggo sai daga baya anan ta gane ashe gurinta sukazo, gaishe da Daddy tayi cikin girmamawa duk da batasanshiba, amma tana ganin kamar tasan fuskarsa, amma ta kasa tuno inda tasan sa, Daddy ya amsa mata da fara'a, shima Mustapha gaisheshi tayi a ranta tana yaba kyawun da Allah yayi masa kamar ba ɗan ƙasar nan ba, ya amsa ba yabo ba fallasa, ta gaida gwaggo ma ta wuce, seda gwaggo taga barin motar su daddy layin, Sannan ta dogara sandarta ta koma cikin gida da ƙyar kamar wadda zata bisu. Zama tayi akan dardumar dasu daddy suka tashi ta ɗauki kuɗin tana jujjuyashi a hannunta kafin ta dubi asabe tace "Asabe kinga ikon Allah ko, nida na ɗauki Maryam na kaita aikatau danta wulakanta se gashi ita aikatau ɗin ma ya zamar mata Alkhairi, jibi fa wanda akace shine mijinnata kamar shi yayi kansa dan kyau, anya kuwa wannan ma bahaushe ne kuwa?" Asabe tace "ikon Allah kenan gwaggo yafi gaban komai, amma dai Maryam tayi sa'ar miji" gwaggo tace "Ni duk ba ma wannan ba, wai yau Ni Ladi nice Alhaji mainasara yazo har cikin gidana da sunan ya gaisheni, wayyo daɗi kasheni wlh jinake kamar mafarki nake asabe..." Haka gwaggo taita zubarta cikin tsananin farin cikin yau Alhaji Mainasara ya zo gidanta, asabe dai se dariya take mata, Maryam kam tasha addu'oi kala_kala, kamar ba ita ce da gwaggo take tsine mata ba gami da aiba tataba........✍️
*Na so page ɗin ya fi haka amma abubuwa sun shamun kai yau ɗinnan, mu haɗu bayan sallah idan Allah yakaimu inda za mu ƙare book ɗin gaba-daya cikin kwanaki ƙalilan da yardar Allah, AYI SALLAH LAFIYA MASOYA.*
*By*
*Zeey kumurya*
*ABIN DA KA SHUKA....!*
_*BY*_
_*ZEEY KUMURYA*_
*Bismillahirrahmanirrahim*
*7️⃣3️⃣*
*Na so page ɗin ya fi haka amma abubuwa sun shamun kai yau ɗinnan, mu haɗu bayan sallah idan Allah yakaimu inda za mu ƙare book ɗin gaba-daya cikin kwanaki ƙalilan da yardar Allah, AYI SALLAH LAFIYA MASOYA.*
*By*
*Zeey kumurya*
*ABIN DA KA SHUKA....!*
_*BY*_
_*ZEEY KUMURYA*_
*Bismillahirrahmanirrahim*
*7️⃣3️⃣*