Sashe 58
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
naci indomie fiye da rabi, sannna na rufe plate din saboda aman dana faraji yana tasomun, ahankali na mike nanufi dakin aunty domin nace ta bani aron wayarta nakira yaya sadiq dina. Da sallama nashiga dakin, aunty dake hada kaya acikin wata yar karamar jaka ta amsamun sallamar batare data dago ta kalleniba. zama nayi akasan gado cikin sanyin murya nace, "aunty dan Allah kibani aron wayarki zankira yaya sadiq nasan yanzu yanata kirana besameniba" dagowa aunty tayi tazubawa maryam ido, cikin tausayinta domin ta dade da fuskantar soyayya sukeyi, gashi harta kasa hakuri tatambayeta Aron waya takirashi, batasan shine me kokarin bata mata rayuwaba, koda daddy befadaba dama aunty ta dukurcewa ranta bazata bar takara kwana acikin wannan gidan da'ake burin cutar da itaba. kasa nayi dakaina ganin aunty tana kallona, wata kunyartace ta lullubenu wata zuciyar tawace tacemun kodai aunty tasan muna soyayya da yaya sadiq dinne. "Maryam, nakirashi ai tundazu amma wayartasa bata shiga, akashe ake cewa" aunty tafadawa maryam haka, domin batason tasan komai tunyanzu tafison sekomai ya lafa tukunna. "Shikenan aunty" nabata amsa cikin sanyin jiki. domin bugun zuciyatane yakaro akannada...
Mustapha yadau tsahon mintuna 20 a toilet kafin yaja kafa yafito saboda matsanancin jirin dake kwasarsa amma bawai dan ruwan ya isheshiba. kan gadonsa yafada Cikin mawuyacin hali, jikinsa na wata irin kyarma, dakyar ya iya jan bargo ya lullube jikinsa saboda wani sanyi sayaji yana shigar jikinsa. tunanin abubunwa dasuka faru abayane suke dawo masa kwanyarsa, tabbas biri yayi kama da mutum, mommy tasha siyo masa kayan maye domin yadingasha, wai rayuwarce seda haka. Agaban mommy suhailat take hugged dinsa kota dane kan cinyarsa amma mommy bazata kwabetaba sema ta nuna jindadinta. Mommy bata bashi tarbiyyya tagariba kokadan tayi masa abubuwa dadama domin ya lalace amatsayin soyayyar datake masane haka, Allah ne kawai yakareshi dakuma tsaiwar dakan da daddy yayi wajen ganin rayuwarsa ta inganta. wasu hawayene masu matukar dumi suka digo masa, wanda dakyar yasamu suka zubo. har yanzu yana mamakin wai mominsa datafi kaunarsa fiye da komai da kowa a duniya ita ce take furta Kalmar tsana agaresa saboda abunda duniya. har yanzu yanajin guntun kaunar mommy acikin zuciyarsa, kobabu komai ta raineshi kuma ita yataso yake kallo amatsayin uwa. zurfaffen tunani yashiga sosai akan rayuwarsa wanda hakan yakara haddasamasa matsanancin ciwon kai dana zuciya, tun yana gane meyakeyi haryafice daga hayyacinsa,komai yadauke masa dif.......
Daddy akokarinsa nason tafiyarsu takance da wuri, yadauki mota yafita dakansa domin yimusu cuku_cukun tafiyar, ga wayarsa dake Cikin aljihunsa sekiransa akeyi ga tarin damuwar dake addabar ransa. tukin kawai yakeyi amma hankalinsa baya jikinsa yanacan duniyar tunane_tunane. be'ankaraba sekawai jiyayi ya gwabzi wata mota adaidai dangi. Cikin tsananin firgici daddy yafara ambaton "subhanallah" a fili, dasauri yayi parking motar tasa yafito ko rufewa kofar beyiba. mutane harsun fara taruwa saboda motar ta jirkicene anata kokarin dago da ita. shima daddy karasawa yayi akafara kiciniyar daga motor dashi. direban dake tuka motar yafito babu wani rauni ajikinsa sedai juya dake dibansa sakamakon jirkicewar da motar tayi, dan motar ta barin dama ta jirkita. Anyi nasarar juyar da motar har'aka fito da matar da direban yake tukawa, sedai matar babu alamar numfashi atattare da ita. tashin hankali wanda ba'asamasa rana. "Ana wata ga wata" daddy yafurta hakan azuciyarsa. "Ya Allah kasa ba kisan kai nayiba" yakara furta haka lokacin da'aka dakko matar a hannu rai ahannun Allah,babu inda yake motsi ajikinta. hankalin direban idan yayi dubu yatashi. Se kiran "innalillahi'wa'inna'ilahirraji'un" yakeyi kamar yadda daukacin mutanen wajen keyi. Cikin sauri daddy yayi gaba zuwa wajen motarsa aka Sanya matar abayan motar. Kasancewar daddy ba boyayyen mutum bane, mutane se fadin. "Yallabai Allah yakiyaye gaba sukeyi" driver seat daddy yashiga direban motar kuma yashiga front seat daddy yaja motar yanufi asibitin aminu kano. wayarsa yazaro yakira bakanikensa yasanarmasa yazo ya dauki motar dayabugedin yatafi da ita, tare da kiran asibitin yasanar musu da zuwansu. Cikin mintuna kalilan suka karasa asibitin abakin emergency yayi parking motar yafito dasauri yabude bayan, ma'akaitan asibin suka kama matad suka sanyata akan abun tura marasa lafiya suka nufi ciki da ita dasaurinsu, suma su daddy rufa musu baya sukayi.........
Doctor yazo yaduba hannun maryam yasa mata maganin,yakuma bata wasu dazata dinga sha. har Aunty tagama hada yan abubuwan datasan zasu bukata atafiyarsu sukayi sallar azhar amma daddy shiru_shiru bedawoba bekuma kirataba. part din mustapha takoma domin tagano halin dayake ciki, tana zuwa tatarar dashi cikin mummunan yanayi. cikin kidima mommy takira daddy danta sanar masa. "Hello, yaya ina katsayane?" numfashi daddy yasauke yace, "saudart ina hanyata tatafiya na bugi wata motane, yanzu haka muna asibiti" "innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, subhanallah Allah yasadai babu wanda yayi mummunan rauni" "to, su biyune dai acikin motar, da driver da wata mata, direban yar buguwa yayi, sunma samasa ruwa, matar cedai kwance haryanzu likitoci nakanta" "ya Allah, Allah katakaitamana" "ameen" "yanzu kuna wanne asibitinne" "Aminu kano" "OK, bari muzo nida su faruq, Allah yakiyaye gaba" bayan sunyi sallama mommy takira faruq tace yadakko mota yazo bakin part din mustapha. taboyewa daddy halin da mustapha yake cikine saboda kar abun yamasa yawa,wannan tashin hankali har ina, dama haka rayuwatake,watarana dole se Allah ya jarrabeka. koda faruq yazo yaga halin da mustapha yake ciki hankalinshi yatashi sosai shima, batare da bata lokaciba yakira su haidar suka kamashi sukasashi a mota suka nufi asibiti dashi. aunty ce, tafadawa asabe me aiki sunfita, idan maryam tatashi tasanar mata, dantunda tasha maganin da doctor yabata sekuma bacci yadauketa. Asibiti mafi kusa dasu suka kaishi wanda yakasance private ne, suna zuwa aka karbeshi likitoci suka rufa akansa,domin ceto rayuwarsa........
mommy cikin mintuna kalilan takarasa gidanta dake lamido, wanda babu kowa aciki se megadi. horn tahau dannawa ba kakkautawa megadi dake kwance adakinsa yana bacci yaji horn din tamkar a mafarki. ahankali yabude idonsa yajidai azahiri yakejin horn din, dasauri yatashi yasuri rigarsa yasaka yafito danyaga waye a wannan lokacin yakatse masa baccinsa. karamar kofar gidan yabude ya leka, ganin motar mommy ce yasashi komawa da sauri ya bude mata get din, zuciyarsa cike da mamakin ganinnata domin tunda yazo gadi gidan bata taba zuwa a irin wannan lokacin ba, tafi zuwa da yamma koda daddare. A fili ya furta "banda abuna,ita da gidanta mene nawa aciki." gudu_gudu, sauri_sauri, yakarasa inda mommy take bayan yarufe gida. "Hajiya sannu da zuwa dafatan kin iso lafiya" yafadi haka yana kokarin karbar jakar hannunta kamar yadda yasaba a kodayaushe idan tazo yakai mata har cikin falo. Amma yau ga mamakinsa seyaga tadaga masa hannu bata bashi jakarba, bakuma ta amsa masa sannun dayake mataba tayi wucewarta ciki. kallonta kawai yatsaya yanayi harta bacewa ganinsa, zuciyarsa cike da mamakin ta, dan duk da bata da sakin fuska amma yau yaga abun yafi na kullum, yana tunanindai akwai matsala tunda gashima ita kadai tazo, sabanin da datake zuwa da driver wani lokacin ma, harda danta. komawa dakinsa yayi domin cigaba da baccinsa.
Momy tana shiga falo ta ajiye jakarta gami da mayafinta akan kujera, zuciyarta sam babu dadi, zarya tafarayi afalon cike da tsananin damuwa, se'alokacin wani gumi yafara keto mata. tanunawa su daddy warkewar mustapha bedaga mata hankalibane dankarsuga gazawarta da wuri. Amma bakaramin dimuwa gami da tashin hankali tashigaba, musamman datasan boka yace, idan aiki ya lalace komai zekoma kan sadiq ne. Tarasa meyasa tun mustapha yana karami kome tamasa na sharri sedai taganshi akan yayanta, taso mustapha ya lalace yazama mebin mata kuma takadirin dan shaye_shaye amma kuma sebezamaba, seyayantane sukeyi. lokacin da mustapha suka fara soyayya da suhailat agabanta suhailat zata dane kan cinyarsa kotayi huging dinsa amma bata hanata, duk dan mustaphan yalalace amma kuma belalace dinba. "tabbas! yazama dole natafi Neman mafita ayau ba gobeba, yanzu_yanzu ma kuwa!" mommy ta fadi haka a fili,tana cizon yatsa. (Hmmm, momy kenan, aishi sharri dan aikene.) wayarta dake cikin jaka ta dakko ta lalubo number wata kawarta takirata. tayi sa'a wayar tashiga amma harta katse bata dagaba,kara kira tayi nanma bata dagaba. Tsaki mommy taja afili ta furta. "ko'ina binta tashiga tabar wayartata oho,Inata kiranta amma taki dagawa" kara kiranta tayi akaro na uku, harta kusa katsewa sekuma ta daga. "Hello kawata, uwargida agidan alh mai nas".......... "kinga dalla ni badogon zance nanemaba, ina kika shiga inata kiranki baki dagaba" mommy ta katseta da fadin haka. "ina falone ina hutawa wayar kuma na daki" "ohk, idan babu damuwa inason ganinki yanzu domin akwai wata matsala babba" "matsala kuma atika, tame?" binta tatambayeta cikin kidima. "Kedai kawai idan da hali kizo, maganar bazata yiyu a wayaba, amma bana gida zanturo miki address din inda nake sekizo kisameni." "Tom, shikenan ba matsala ganinan zuwa yanzunnan" "yawwa binta sekin karaso" mommy nagama fadar haka ta katse wayar, address din inda take ta turawa binta kawarta. jefar da wayar tayi akan kujera bayan text din yaje, zama tayi itama akan kujerar ta rafka uban tagumi da hannu biyu tana tunane_tunane.