Sashe 75
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Misalin ƙarfe biyar da yan'mintuna bayan nagama haɗa komai nawa kamar yadda ammi tace, ina zaune adakinta akan gado nikadai, ammi da Aunty zuhura suna part dinmu suna kara gyarawa. Ammi tace ta shigo dakin da sallama, amsa mata nayi cikin girmamawa. Ammi tana kallona tace, "yawwa Maryam kingama haɗa komai, har su turarukan da mayukan?" cikin sanyin murya kamar yadda jikinama yake a sanyaye nace, "ehh ammi nagama" wayarta ta mikomun tana fadin, "yanzu aka kirani da wata number wai ana nemanki" nace "ba Aunty bace kuma" ammi tace, "ehh ba ita bace wannan ma kamar yarinya" cikin mamaki na karbi wayar na duba number senaga kamar nasan number'n. danna kira nayi nakara a kunnena. Ammi ta dauki jakar da Maryam tahada kaya tafice. seda wayar takusa katsewa sannan aka daga da sallama. wayyo daɗi, wani farinciki naji ya lullubeni danaji Muryar sahibata kawar asali, kawar rufin asiri saleemat. cikin ɗoki nace, "saleemat!" itama tana dariyar jindadi tace, "na'am kawata nayi kewarki sosai wlh" "hmmm, kedai bari saleemat dazunnan nagama zancenki acikin raina, ya gida yasu umma da baba da kowa da kowa" "duk lafiya kalau Maryam" "Masha Allah, ina Habibi Adam?" "Habibi yananan kalau, ke ankawo lefenafa tun waccen satin" "kai haba, shine ba labari" "wlh Maryam nakai wata ina neman wayarki bata shiga" "wayar ta fadine, wai dagaske kike ankawo lefennaki saleemat" "dagaske mana, zan miki wasane dakina chat ma dana turo miki kingani" "kaii, amma naji dadi kawata Allah yasanya Alkhairi, Allah yasa damu za'ayi." "Ameen" hira muka shigayi irinta amininan juna, harna tambayeta inata samu numbar ammi tacemun aunty ce ta bata. muna cikin hirarne nace mata, "ina gwaggo kuwa saleemat? Aunty tacemun idan tazo zata hadani da ita inata jiranta naji shiru" saleemat tace, "gwaggo tananan lafiya kalau" (dayake Aunty tarokesu karsu sanar da Maryam ciwon gwaggon dantasan halinta tada hankalinta zatayi tayita koke_koke, tafison idan tazo kafin azumi seta taho da ita ta duba gwaggon.) nace, "kigaidamun da ita sosai, kikarbomun number'n tama kituromun nakirata" "toh" kawai saleemat tace, ta kawar da zancen da fadin. "Yanaji wai muryarki kasa_kasa, kodai angonnaki ya tumurmushekine a gado" ta karasa zancen tana dariya. Cikin jin haushi nace. "Bansaniba yar iska, ni kaiwa umma wayar mugaisa" dariya tacigaba dayi harta kaiwa umma wayar, mungaisa sosai da umma na mata Allah yasanya Alkhairin lefen saleemat. Umma tamun yar nasiha akan aure na mata godiya mukayi sallama. banbari saleemat ta karbi wayarba na kashe dannasan tsokanata zata cigaba dayi. Haka kawai naji ina hawaye, dama jikina duk a sanyaye yake yau. goge hawayena nayi da sauri jin tafiya a falo, dan kofar dakin abude take. Ammi ce kuwa ta shigo dakin, bata lura da halin da Maryam take cikiba dan tayi kokarin boye damuwarta. Ammi tace, "Maryam kungama wayar" nace "ehh, wata kawatacema ashe Aunty ce ta bata number'n ki" tace. "ayya, kema Yakamata ace kina da waya a hannunki, bari NOOR yashigo sena masa zancen yasiyo miki" ban iya cewa mata komaiba dan kuka ze iya kufcemun" zama ammi tayi akan gado tana fadin "washh" araina nace. "Ai dole kigaji" saboda ammi kwata_kwata bata zama, koyaushe cikin dawainiya take damu nida yaya Mustapha, har tausayi take bani. "Sannu ammi" na furta a hankali. "Yawwa Maryam" mikewa nayi nace "ko in miki tausane" muryar ammi na nuni da gajiya tace, "dakuwa kin kyauta ɗiyata" kwanciya tayi akan gado nikuma nashiga yimata tausar............
*KANO*
Suhailat tunda suka dawo gida taketa baza ido taga ta inda zata ga Mustapha, amma ko alamarsa bata ganiba. kasa hakura tayi taje har part dinsa, amma setaga a kulle. Da hanzarinta ta dawo bako kunya tatambayi aunty. Aunty kawai tace mata yayi tafiya ne. bataji dadiba kuma bataso hakaba, ta koma daki ta ɗauki wayarta taita kiransa amma wayar bata shiga, haka ta hakura zuciyarta babu daɗi kokaɗan. Aunty sunyi waya dasu daddy sun isa lafiya. wajen karfe biyar tasa suhailat ta hada kayanta danda ita zata wuce Kaduna, suhailat bata iya hada kayanba saboda batajin dadin jikinta. Se aliyace tana kunkuni ta hada mata, bisa tursasawar Aunty. Aunty kallon suhailat kawai take tunda ta dakkota yanda gabadaya ta zabge ta rame, se uban fari kamar zabiya. gashi sebin tiles take tana kwanciya, Aunty dai takasa hakuri tatambayeta meke damunta. setace mata wai malaria ce. Aunty baiwar Allah babu tunanin komai aranta seta yarda ta mata fatan samun sauƙi.......
*JOS*
Duk da part din dazamu zauna yana jikin na ammine,dan amminma tacemun anan ta zauna kafin mamansu Saddam ta rasu, seda ta rasu ta dawo inda take yanzu. Amma wlh jinake kamar wani garin za'akaini me nisa gashi zuciyata cike take da fargabar yadda zamannamu ze kasance, nasan dai ni ina matukar sonsa amma shi nasan baya sona. Idannatuna hakan se inji duk zuciyata ta karaya jikina yayi zanyi, musamman ma yanda yake nuna halin ko'in kula akaina. dauriya kawai nakeyi ina boye damuwata. Zuwa yanzu umaimah tasan waye mustapha a gurin ammi, kuma tasan Maryam matarsa ce, dan part din mama taje ta matsa mata da tambaya akan waye mustapha, seda mama tabata labari ta samu sa'ida. Tsana da haushin Maryam ne suka cika mata zuciya ganin ta rigata mallakar irin mijin datake mafarkin samu, amma dadinta daya dayakasance gida ɗaya zasu zauna, ita kuwa zatasan yanda zatayi tajanyo hankalinshi yadawo kanta, zatayi duk yanda zatayi ganin ta kwaceshi daga hannun wannan karamar yarinyar wato Maryam.
Bayan sallar magriba ammi tasani nayi wanka na shirya cikin wata hadaddiyar doguwar riga me kamar alkyabba yanayin jikinta. nayi kyau sosai acikinta, nafeshe jikina da daɗaɗan turaruka masu sanyi kamshi. Bayan nagama shiryawa ammi tamun faɗa akan zamantakewar aure, mama ma, tamun. nidai hawaye kawai nakeyi ina saurarensu.
Bayan sallar isha'i ammi ta kama hannuna ita da mama suka rakani har inda yake a matsayin dakina ta zaunar dani akan gado. nasha kuka sosai bayan sun tafi. Daga baya kuma na rarrashi kaina nadena kukan. A hankali na tashi nakarewa dakin kallo yayimun kyau sosai sai kamshin turaren wuta da sabon fenti yakeyi. kayana su ammi sun jeremun su a cikin cover, su turaruka da mayuka duk anjeremun akan mudubi, komaidai need abun gwanin ban sha'awa. Falo na fito shima yayi kyau sosai babu wani tarkace, yasha labulaye masu kyau. daga falo kitchen nanufa, shima yaji kaya komai na amfani akwaishi. dakina na koma bayan nagama kalle_kallennawa, dakinsane kawai banyi gigin shigaba. ina mamakin wai wannan gidanane da kayan cikinsa komai nawane, nida bantaba zaton zansami koda rabin wannan ba. Zama nayi a bakin gado nashiga sake_sake. Ƙarfe goma da yan mintuna ya shigo part dinnasu, hannunsa dauke da ledoji manya. Kitchen ya nufa ya ajiye kajin daya shigo dasu kamar yadda ammi tace yasiyo. Shima seda yagama karewa gidan kallo, shima gidan yamasa kyau sosai, kafin yashiga daki seda ya saita kayan kallo danshi mutum ne meson kallon news da kallon ball. Ina zaune tsuru naji shigowarshi ajiyar zuciya nasauke cikin jindadi,dandama a tsororace nake da zaman nikadai, nandaima da wutar NEPA ne. Dakinshi ya shiga ya ajiye sauran kayan dayashigo dasu, sabulayene da mayuka da turaruka. Nashi ya kwasa ya jera a gaban madubin dakin. sannan dauki sabulu da saban towel din daya shigo dasu ya nufi toilet. bayan kusan 30 minutes yafito yazira jallabiya yafashe jikinshi da turaruka ya kwanta. Lumshe idansa yayi yana tunanin wannan aure da daddy yamasa. shiyanzu besan yazeyi da yarinyar mutaneba, tunda bashi da lafiyar daze bata hakkinta na aure akansa, kodama yanada lafiyar baya tunanin waccan karamar yarinyar zata iya dashi, shifa yaraina Maryam a matsayin matarsa ganinta yake yar karamar yarinya, dandai baze iya bijirewa daddy bane da....... wayarsace ta katse masa tunaninsa ta hanyar yin vibrate. Ahankali ya bude idansa ya tashi ya dakkota daga kan madubi. MY UNCLE yagani yana yawo akan screen ɗin wayar. kanin ammi ne dayake saudiyya kullum sesunyi waya dashi, dagawa yayi sukasha hira har yaransa yabawa suka gaisa sannan sukayi sallama. Nasihar da daddy yamasa ranar da zasu koma kano itace ta dawo masa kwanyarsa tamkar yanzu yake masa ita. "Mustapha, karike yarinyarnan amana kaga marainiyace kuma bata da wani gata sena Allah, idan ka cutar da ita Allah baze barkaba. Kuma yazama dole kakula da cinta da shanta da kuma lafiyarta." Mikewa yayi yaɗauki ledar daya shigo da ita, bisa umarnin da zuciyarsa ta basa akan yakamata yaje yaga lafiyarta kafin ya kwanta, tunda yanzu amanace ita a hannunsa, da wannan tunanin ya nufi dakinta. Maryam dataga zaman ya isheta gashi ko digon bacci a idonta, seta tashi dama da alwalarta ta shimfida sabuwar daddumarta ta tada sallah.............✍️
*By*
*Zeey kumurya*
*5️⃣4️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
............ Ahankali ya tura kofar dakin yajita a bude, bakinsa dauke da sallama ya shiga dakin. wata irin faduwar gabace ta ziyarceni duk da Sallah nake jin shigowartasa. kamshinsane yatabbatarmun da shine, gaba-daya jinayi na diririce, narasama menake karantowa a cikin sallar saboda tsabar fargaba. shiko mustapha ganin sallah Maryam take, seya ajiye ledar hannunsa ya juya ya fice. Ajiyar zuciya nasauke jin yafita na sallame sallar amma banko motsaba daga inda nake, duk da yafitan amma bandawo cikin nutsuwa taba.gani nake kamar ina juyawa zanganshi yadawo cikin dakin, kusan 16 minutes sannan na daure na tashi daga kan dardumar har lokacin daddadan kamshinsa bebar dakinba. hijabin jikina na cire na ajiye, leda nagani dabansan da itaba a dakin. cikin mamaki na dakkota nafara fito da kayan dake ciki, sabulayen wanka ne dana wanki,se MacLean da sabbin burush guda biyu da mayukan shafawa harda sosan wanka me kyau acikin ledarsa araina nace, "gaskiya wannan ya iya siyayya, komai dayasan zan bukata seda yasiyo." mayar da kayan nayi cikin ledar bayan na dauki abunda zan bukata a yanzu na ajiye a gefen gado. Toilet na fada nayi wanka, ina fitowa na zira rigar bacci nafada kan gado dan wani irin bacci naji inaji lokaci daya......