← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 128

Sashe 113

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

tashe ni" nace "amma dai yau bazaka fita ba?" yace "why?" nace "ruwa mana" yace "idan ya tsaya zan fita ai" na ɗan ɓata fuska nace "ka bari gobe ka fita, kaga jiya ka dawo baka gama hutawa ba" yana gogamun sajen fuskarsa a kuncina yace "gobenma haka zaki ce karna fitan" nace "Allah bazanceba, ka huta yau kaji, kaga ruwa ma ake" yace "to dama nace miki zan fita ne" nace "ai nasan zaka ce zaka fitanne" murmushi yayi yace "bakyaso in fita" na gyada masa kai alamar eh, ɗayan hannunshi yasa ya kwantar da ita a jikinshi yace "nima banason na fita, na fiso in zauna inta kallonki ina jin daɗi" lumshe idona ina shaƙar kamshinsa bance komaiba, ragowar choculate ɗin hannuna ya karba yace "daga tashi se shan zaƙi? shan zaƙin ki yayi yawa Ummu, shiyasa kike ciwon ciki, zan kwashe sauran na ledan ce na bayar kin gama shan rabonki" ɗago kaina nayi daga jikinshi cikin shagwaba nace "to bakai ka siyomun ba?" yace "ai ba siyo miki nayi ki shanye a lokaci ɗaya ba, kaɗan_kaɗan zaki dinga sha, kuma shima ba kullum ba, amma ke jiya kinsha da yawa, yauma daga tashi tun dira akansu" cikin marairaicewa nace "to kayi hakuri karka kwashe sauran zan dinga sha kaɗan_kaɗan ɗin" yace "to na barmiki, amma idan kika shanye kafin 1 month bazan ƙara siyo miki ba" nace "to na yarda, yanzu bani wannan na ƙarasa shanyewa" yace "A'a kingama shan na yau" nace "Please daga wannan fa shikenan se gobe zan ƙara" yace "to anjima sai kisha" badon naso ba na haƙura, amma na ɓata fuska sosai, murmushi yayi yace "muje muyi wanka" nace "ni nayi ai" yace "sai kimun ni" waro manyan idanunta tayi waje sosai tana kallonshi, daga mata gira yayi yana jifanta da wani irin da kallo daya kashe mata jiki, barin jikinshi nayi na koma gefe na kwanta nace "bacci nakeji" bace mata komaiba ya miƙe ya sauka kan gadon ya shige toilet, ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe ido cikin jin daɗin ya shige wankansa shi kaɗai, dan batasan zatayiba daya takura se sun shiga tare, jiyama da sukayi taren kuka ta dinga masa, kuma har sukayi suka fito idanunta a rufe suke, batasan ya dawo ɗakin ba, sai ji kawai tayi an ɗauketa, be direta a ko inaba se a cikin ruwa tajita, yanzunma idanunta a rufe sukayi wankan tana ta aikin turo baki gaba, shikuma yanata tsokanarta.. Tsaye yake a gaban madubi yana shafa mai da towel daure a ƙugunsa, Maryam kuma tana kan kado ta ƙudundune jikinta tunda suka fito daga wankan ta kasa kwakkwaran motsi, kunyarsa take ji sosai kamar ƙasa ta zage ta shige cikinta haka take ji, juyowa yayi a hankali ya dubeta, da sauri ta juya masa baya, murmushi yayi ya ƙasara bakin gadon ya tsugunna a gabanta, ƙara yunkurin juya masa baya tayi towel din jikinta ya kunce ya ɗanyi ƙasa, rabin Brest ɗinta ya fito waje, "saurin riƙe towel din tayi tana hawaye tace "kadena kallo na" idanunsa akan kirjinta yace "dama Ni ba kallon ki nake ba, ko kinga mun haɗa ido?" tana ƙara volume ɗin kukanta tace "gashinan kana kallar mun...." se kuma tayi shiru ta fashe da kuka, dama kaɗan take jira akan tsokarta da yay tayi da suna wanka, tashi yayi ya zauna a gefenta ya janyota jikinsa ya rungume yana murmushi yace "nifa ban kallar miki komai ba" cikin kuka tace "amma ai kagani a toilet" yace "shima ban kalla ba fa" ya ƙarashe zancen yana share mata hawayen fuskarta, shiru tayi jinta ajikinsa tana sauke ajiyar zuciya, gashin kanta ya shafa yace "to tashi muje in shiryaki, kinga time yana tafiya ba muyi break ba" barin jikinshi nayi nace "zan shirya da kaina" yace "shikenan jeki ki shirya" nace "toh rufe idanka, karka kalleni" ya rufe idon yace "na rufe" kallon fuskarshi nayi naga idanunshi a rufe, ta bayanshi na sauka daga kan gadon ina faɗin "karka juyo sai nace nagama" ya gyadamun kai, na ƙarasa gaban mudubi na fara shafa mai, inayi ina kallonshi ta cikin mudubi, harna gama shafe_shafe na be jiyoba, sai dai kuma ba kayan da zansa a jikina, tunda nawan ya jiƙasu suna toilet a shanye.........✍️
Chapter 113 · 0% Book details