← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 128

Sashe 3

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan minti goma sha biyar nayi ahanya,kafin nakarasa gidan lantana.amma nadaje lantana ta barni a tsakar gida ta shige daki,fiye da minti talatin sannan ta fito ta bani sakon.a lokacin raina yakai kololuwa wajen baci,domin nasan tana sane tamun haka,ga tsoro da fargabar abunda gwaggo zatamun yamun rufdugu akaina. Ashe sakon kudine shiyasa naga gwaggo tana rawar jiki.karba nayi na nufi gida.wajen ba mutane sosai,hasalima tunda na taho banhadu da kowaba,gudu na farayi zuciyata na bugawa,tsorone me tsanani ya kamani Wanda bansan kona meneba.......

Cikin takunsa na cikakken namiji,jarumi, yake tafiya,shida lukmanne daya rakoshi ze tafi gida,tafiya sukeyi zasu karasa gurin motarsa,dayay parking a gefen titi.kamar an cillota daga sama kawai jiyayi ta bugi kirjinsa,da sauri nayi baya jinnayi karo da mutum,banzataba banyi tsammaniba,saboda hankalina gaba daya baya jikina,yayi gida.wani daddadan kamshine yaziyarci hancina,wanda tunda uwata ta haifeni bantabajin irinsaba.wata irin bugawa kirjina yayi da karfi,jikina ya fara rawa,kaina naji ya mugun saramun, jinayi kawai nayi luuuu zanfadi,taroni yayi da tattausan hannunsa,ya hadeni da jikinsa.wani irin yammm yaji ajikinsa,tsigar jikinsa ta tashi ta mimmike,lokaci daya yanayinsa ya sauya,lumshe idonsa yayi cikin amsar bakon yanayin daya riskeshi,zuciyarsa na bugawa dasauri da sauri,kafarsace ta gagara daukarsa,kasa mukayi gabadayanmu dani dashi,shi yafarayin kasa ni kuma na fada kan faffadan kirjinsa,wani mahaukacin feeling ne yaji ya bujuro masa,jinta a kwance a kirjinsa, Wanda betaba jin irinsaba tunda yake arayuwarsa.✍️

*BY*
*zeey kumurya*
*AUNDA KA SHUKA*.........
_*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN*
👇
*ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

*Bismillahirrahmanirrahim*

0️⃣3️⃣

...........Bansan ya'akaiba kawai gani nayi na mike tsaye,jikina ya kama kyarma tamkar anjonamun schocking, wannan shine karon farko arayuwata dana taba hada jiki da wani da namijin,dayan da suke tarene ya rike hannuna,ganin bana cikin nutsuwata yace. "sannu 'yanmata,ba bakin magana se rawa kawai na jikina yakeyi,tamkar mazari.

Tattaro duk wata juriyarsa yayi,ya mike tsaye,har yanzu yanajin bakon yanayin ajikinsa.

Dakyar na tattara nutsuwata na sunkuya nadauki sakon gwaggo daya fadi kasa,Allah yasama kudin a cikin Leda ta sakamun.ban kara kallon Wanda muka fadi tareba,saboda kunya da tsananin tsoron daya rufeni. Kai na akasa,cikin rawar murya nace" ka..yi..ha..kuri...dan.. Alllah,shiru yayi kawai batare da yacemun komaiba. wani tsorone ya kara mamayeni karnaje kobe hakuraba. Dayan ne kawai yamun magana. "Karki damu 'yan mata,amma dai kidinga kula gashi dare yayi,muje mu rage miki hanya ko? A'a nagode,ina gama fadar hakan na kama hanya na fara tafiya,zuciyata cike da zullumin,kodai Wanda na buge kurmane,amma banda haka mezesa mutum yaki magana.gashi gaba daya kamshin turarensa ya gamemin jikina,Jinakeyi tamkar yana gurin har yanzu.saitin zuciyata na dafa,saboda har lokacin tana bugawa da sauri da sauri.numfashi na sauke,wani bakon yanayi dabansan na meneba yana ziyartata.

Dubansa lukman yayi ganin yanda gaba daya yanayinsa ya sauya,shi duk a tunaninsa ransane ya matukar baci akan abunda ya faru,hakuri ya hau bashi,amma seyaga ya daga masa hannu kawai,gurin motarsa ya nufa ya bata wuta.

Ikon Allah ne kawai yakaishi gida,saboda har lokacin jiyakeyi tamkar tana kwance a kirjinnnashi,wani irin yanayi yake ciki me wuyar fassarawa. Bedroom dinsa ya nufa tare da fadawa kan gadonsa,ina ze ganta,a ina zekara ganinta,ya kara rungumeta kozeji irin yanayin dayaji sanda tana kwance a kirjinsa,gashi ko fuskarta beganiba,saboda gurin ba wadataccen haske,kansa ya dafe,tare da runtse idonsa,zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri....

Kusan minti talatin nayi ahanya,saboda tunanin mutumin da na buge,se lumshe ido nakeyi saboda dadin kamshinsa,dayaki barin jikina,seda nazo kwanar gidanmu sannan na tuna da Abunda na bari,ga tuyar awara gashi gwaggo tace inyi sauri.addu'ar Neman tsari na fara karantowa a zuciyata.cike da tsananin tsoro na shiga gidan da sallama ta.gurin suyar awarar na kalla,kaskon na gani da guntun mai akasa, alamun an gama suyar awarar. Dakin gwaggo na nufa zuciyata na tsananta bugu,babu wutar nepa,amma dakin gwaggo da akwai sola. Tana zaune akan doguwar kujerar dake dakinnata,ta Dora kafa daya kan daya. Tsugunnawa nayi agabanta, "gwaggo ga sakonnaki" na furta cikin sanyin murya.

Wani mugun kallo ta jefeni dashi,tace."gidan ubanwa kika tsaya kusan awa biyu,kuma nakira lantana tacemun tun dazu ta baki sakon. Baya na farayi ina bawa gwaggo hakuri,domin bansan mezance mataba,nasan yau me kwatata a hannun gwaggo se Allah.wata wayar wuta ta janyo agefenta me matukar kauri ta zubamun agadon bayana,da gudu na tashi nayi tsakar gida ina kokarin fita waje,amma seda gwaggo ta cimmun.dukana ta hauyi kota ina,sekace jaka,ihu nakeyi da dukkan karfina ina Neman taimako,ina bata hakuri,amma tamkar kara zugata nakeyi.

Umman su saleemat wadda katangar gidansu take jikin namun gidan,itace ta shigo da saurinta.tsakiyarmu ta shiga ta rike wayar hannun gwaggo.da sauri na tashi na buya abayanta ina sakin ajiyar zuciya,akai akai.

"Ke suwaiba,ki matsamun ki bani guri kuma ki cikamun bulala,gwaggo ce take fadar haka cikin daga murya,se zaro ido takeyi ta fiffika tamkar wata sabuwar kamu.

"Bazan cikaba,gwaggo.yaza'ayi ki samu yarinya marainiyar Allah ki maidata sekace jaka,kullum sekin jibgeta haka akeyi. Tafa hannuwa gwaggo ta farayi tana salati,"ni zakiyiwa rashin kunya suwaiba,har cikin gidana.lallai wuyanki yayi kauri,kifita daga safgata suwaiba,banason shishshigin da kikemun akan maryam. "Ba shishshigi bane gaskiyace gwaggo kuma dole a fada miki,amma ni ba rashin kunya zan mikiba.Abunda kikeyi ba kya kyautawa... " yaza'ayi in kyauta in aiki yarinyar tun dazu taje ta zauna,amma se yanzu zata dawomun gida,dama nasan tun ba yauba,ai bin maza takeyi idan kuma sharri na mata kamshin turaren ubanwa takeyi,gatanan ai ki shanshanata kiji.saboda yadda gwaggo take magana cikin kakkausar murya tare da daga murya mutane 'yan gulma harsun fara shigowa gidannamu.

Juyowa umma tayi tana kallona,hawayene kawai yake kwaranya daga idona har lokacin. Tabbas taji wani kamshi a jikina,amma hakan bazesa ta gasgata maganar gwaggoba,domin tasan maryam tasan halinta ciki da waje tasan abunda zatayi da Wanda bazatayiba. "Maryam kifada mana gaskiyar abunda ya faru.labarin komai na kwashe na fadawa umma, amma kawai senaji nauyin dace mata na fadi ajikinsa,kawai sena cemata bugeshi nayi. Karyata maganata gwaggo tayi,tana cewa "wanne irin kamshine wannan daga ka buge mutum seya zauna ajikinka,inma zanfadi gaskiya infada,ai dama bayau na fara zuwa yawon karuwancinaba.hakuri umma ta kama bata,wasu matama da suka shigo hakuri suka hau bata. Dakyar gwaggo ta hakura amma da cewa tayi seta karyamun kafa taga da wadda zanna zuwa iskancinnawa. Dukan da gwaggo tamun bedameniba kamar yadda take ta faman aibatani,tana dangantani da Kalmar karuwa,durkusawa nayi agurin ina sakin kuka me tsuma zuciya.lallashina umma ta hauyi da banbaki amma Sam bana cinta bana fahimtar metake cewa, wani zafi zuciyata takemun, ahankali na mike na shige dakina bayan kowa ya watse daga gidannamu.....

9:00 pm,suke hallara akan dinning gaba dayan gidan domin yin break fast,kuku kamar yadda yasaba ya gama komai,ya jera akan dinning. Kowa ya hallara amma banda mustapha. Kiransa mommy tayi har 3 missed call amma bedagaba. Kallon suhaita tayi tace" daughter jeki duba ki gani ko lafiya yau son befitoba. Haidarne yace"haba mommy muci abincinmu kawai kinsanfa shi big bro,bawani damuwa yayi da cin abinci ba.harararsa mommy tayi,idan shi bedamuba nina damu,daughter kiyi sauri kikirawoshi.

Suhailat abunnema ya samu tashi tayi tana yiwa haidar gwalo,ta nufi part dinnasa.Baya falo hakan yasata nufar bedroom dinnasa,yana kwance idanunsa,a lumshe tamkar me bacci.tama manta da wani sakon kiranshi da'akace tayi,shaukinsa da wata muguwar sha'awarsace take fizgarta.fadawa tayi jikinsa,tana shigewa jikinsa,yayi nisa a tunanin yarinyar dabe saniba yaji mutum ajikinsa,abunda suhailat bata zato ba,kuma betaba mataba.jitayi yazagaye bayanta da hannayensa yana shafa bayan ta,yana kara matseta ajikinsa.cikin tsananin jin dadi Mara misaltuwa.suhaital ta fara kokarin kissing dinsa,soyake yaji irin yanayin dayaji dazu amma bejiba,ahankali ya bude dara_daran idansa,akan fuskar suhailat ya sauke su,da sauri ya tureta daga jikinsa, tare da mikewa zaune. ransa a matukar bace. Itama suhailat din tashi tayi ganin yanda lokaci daya ya sauya,zatayi magana yanuna mata hanyar kofa,tashi tayi tana turo baki gaba ta fice daga dakin.
Tunda mommy taganta tasha jinin jikinta,ganin yanda take babbata rai,dariya haidar da zannuraini suka kwashe da ita. Haidar yace"dama seda na fada miki karkije kokinjema baze zebo. Harararsa tayi tamkar zatayi kuka tace"mommy kinga su yaa haidar ko? Mikewa mommy tayi tace"kyaleni dasu daughter.Ku zauna,kuci abincinku bari naje na sameshi.

Yana zaune kamar yanda suhailat ta barshi,mommy tashigo bedroom dinnasa.zama tayi agefensa,tare da jawoshi jikinta.cikin rarrashi tafara magana "haba my son,meyasa bakason cin abinci,baka tsoron wani ciwon yakama munkai,please kazo muje muyi dinner.shagwabe fuska yayi sekace yaro yace." Mommy a koshe nakefa, ni tea kawai zansha. Shafa kansa mommy tayi cikin tsananin kaunarsa, "shikenan my son bari naje ha hado maka. Dakanta ta dafa masa a kitchen din part dinsa,seda yasha sosai tana lallabashi kamar karamin yaro,sannan ta kyaleshi.tana fita ya nufi toilet yasakarwa kansa ruwa koyaji sanyi aransa.domin gaba daya yarasa meke damunsa......

Tunda nashiga daki nake kukan tausayin rayuwata,kusan minti goma gwaggo ta shigo dakin. "Dan ubanki bazaki tashi kikarasa sauran ayyikankiba,maganarta cikin tsawa ta sani dagowa da sauri,mikewa nayi na nufi hanyar fita.jikina a sanyaye nake aikin yau,tunanin dan gayun dana gani yamun tsaye acikin zuciyata. Seda sha biyun dare ta wuce na samu kaina,domin har girki seda nayi. Bayan na karayin wanka nayi sallar isha'i na kwanta akan tabarmata.saboda tarin gajiya da ciwon kan dake damuna saboda kukan danayi tuni bacci ya kwasheni,cikin mintuna kalilan.

*************

Karfe 7:30am,ya gama shirinsa tsaf na zuwa office. Ko break beyiba saboda batashi yakeba,mommy ma awaya ya sanar mata ya tafi.ma'aikatan gidanne suketa gaishesa,hannu kawai yake daga musu. Drivernsa,yana hangosa ya fito da sauri tare da bude masa gaban motar yana gaisheshi. Shima hannu kawai yadaga masa. Ya shige motar.

7:45 sun isa ma'aikatar tasu,kullum haka yake zuwa baya latti,saboda shi bayason karya ka'ida.driver na rike da briefcase dinsa har office dinsa.ma'aikata se kwasar gaisuwa sukeyi a gurinsa. Zama yayi akan kujerarsa.sakatariyarsa ce ta shigo office dinnasa,gaishesa tayi tare da dakko masa wasu takardu ta 'ajiye masa a gabansa,cikin girmamawa.sannan ta juya ta koma wajen zamanta.
Chapter 3 · 0% Book details