Sashe 67
Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"kafin su kasheshin sunsha dambe dashi a kokarin shi na kwatar ransa, dan har wasu yajiwa ciwo da naushin daya dinga kai musu, to Sarkin yawa yafi Sarkin Karfi. susu biyarne shikuma shi ɗaya, kuma su da makamai a hannunsu. ni kuwa banda ihu babu abunda nakeyi ina neman taimako, ɗaya daga cikinsune yatoshemun baki, da gwabjejen hannunsa. maimaita kalmar shahada yayitayi harsuka yankashi sekace wani dabba. kansa nayi da gudu bayan sun fice ina jijjigashi ina kururuwa ina fadin yatashi karya tafi yabarni. gaba-daya nima nayi dama_dama a cikin jinin dake fita daga jikinsa, tun ina fahimtar menakeyi harna dena. farkawa kawai nayi naga gidan a cike da mutane, ga jami'an tsaro suna jiran na farfaɗo suji karin bayanin abunda yafaru. mahaifiyatace a kaina da kanina Muhammad, gaba-daya ido yadawo kaina, masumun sannu nayi masu kallon tsegumi namun. nidai dakyar na yunkura na tashi zaune saboda nauyin da kaina yamun, ashe nadade a sume dan har anyi masa sutura. Dakin dayake mahaifiyata ta kama hannuna ta kaini, muna shiga na hangoshi a makara da gudu na kwace hannuna daga nata nanufi gurin da makarar take na kwanta akan gawartasa na fashe da kuka, surutai naitayi irin na fitar hayyaci, dakyar aka banbareni daga jikinsa, ina kallo aka fitar dashi zuwa gidansa na gaskiya. Tundaga wannan lokacin nazama ba uhmm ba um'um, saidai naitabin mutane da kallo, banaci banasha kuma bana kukan fili sena zuci, a haka har akayi sadakar uku. Nidai bazance ina cikin hayyacinaba a wannan lokacin, suma kam nayita ba adadi, ga tsohon ciki. Seda na kwanta jinya a asibiti, dannamafi wata a kwance, mahaifiyata kullum cikin kuka take, dan duk sun fitar da rai dani. Kanina Muhammad koyaushe cikin kwantarmun da hankali yake, tare da alƙawarin seya daukarmun fansar mijina akan wadanda suka kasheshi ko su waye. Mahukunta nata aikinsu na binkice akan kisan. kwana biyu da sallamoni daga asibiti yan'uwan MODIBBO sukazo akan rabon gado, nace musu suje surike komai ni banaso. banason komai na dukiyar na bar musu. Muhammad ne, yace hakan bazeyiyuba ai rabon gado Allah ne yace ayi, kuma ko badonniba, abunda ke cikinafa ai dole a fitar masa da hakkinsa. Sukuwa yan'uwansa ba hankali harsun fara hada kan kadarorinnasa suna mallakesu. Muhammad ne yaje yasamu wani yayan abokinsa lauya yafada masa, shikuma yashigar da maganar kotu. segamu har gaban alkali. Alkali yace, ai babu zancen rabon gado yanzu harse na haihu anga menahaifa. dan haka a tattaro duka abunda ya mallaka a damka masa har zuwa lokacin dazan haihu, budar bakinsu secewa sukayi ai anyi scanning anga mace ce, a cikina dan haka ayi raba kawai. mamakinsu bakadanbane ya kamani, dan duk jinyar danasha ko duniya basuzoba, amma wai anmun scanning anga macece. Alkali kuwa fatattakarsu yayi yace dole sena haihu, kar wanda yakara zuwa masa da batun harse na haihu. Ba'afi wata dayin hakaba, na haihu a asibiti bayan uwar wahalar danaci. Nahaifi yaro kyakkyawa me kama da ubansa, lafiya kalau dashi. Nakai kwana 3 bansan waye akainaba, bayan na haihu. saboda damuwa tamun yawa,jinina yahau sosai. Nafi sati a asibiti sannan aka sallamoni. yaro yaci sunan *Muhammad* nayiwa kanina takwara, saboda soyayyar dake tsakanina dashi, dakuma yanda yake son Muhammad, kodayaushe yana hannunsa, har wanka yake masa sekace mace. kullum cikin fadamun yake, idan yayi aure nabar bishi Muhammad, yarikesa. Haihuwar yaron ita taragemun kaso 50 nadamuwar danake ciki akan mutuwar adalin mijina. soyayyar uwa da danta, daga Allah ne, bansan yazan fasalta muku yanda nakejin kaunar danakewa Muhammad karami ba. Munje kotu alkali yamana rabon gado, tunda namiji aka haifa yan'uwan modibbo basu da komai a cikin gadonsa, komai nasa na yaronsane seni da'aka bawa tumunin takaba. tundaga wannan rana damukaje kotu yan'uwan modibbo suka sakomu a gaba, nida mahaifiyata da kanina. suka takura mana suka tsangwamemu. watarana bayan munyi arba'in, sukazo mun da wata fitinar akan dole sena basu dukiyar Muhammad, tunda sune danginsa na uba, zasu rike masa su juya masa kafin ya girma. harna mike zan tattaro musu kanina Muhammad yashigo gidan, dayaji abunda ke faruwa abakin mahaifiyarmu yace basu isaba baza'abasu komai na dukiyar Muhammad. fada sosai abun yazamarmusu da Muhammad duk da befi ɗan cikinsu ba, daga karshe dai dole suka hakura suka tafi. Yan'uwan mahaifin modibbo danaje musu yawon arba'in sena fada musu abunda yake faruwa, shine sukace natattaro komai nakawo musu aisu basu isa sun kwata ahannunsuba. haka kuwa akayi natattara komai nakai musu. Gwalagwalan da modibbo yasiyo a ranar daya rasu sukadaine ban bayarba. dama a cikin wata jaka yake, sena boye jakar a dakina. Akwai wata a zurfa a hannun modibbo, tunda nasanshi da ita nasanshi da ita, seda ya mutu aka cireta. itama sena jefata a cikin jakarnan dakuma tambarin gidansu modibbo, duk na hada na ajiye. Watarana da daddare muna cikin bacci, wasu mutane suka hauro mana gidanmu. basu tunkari dakin kowaba senawa. Ina rungume da Muhammad a kirjina naji ana ƙoƙarin rabani dashi ta ƙarfi. da sauri na farka, shima Muhammad din farkawa yayi yana tsandara kuka. cikin matukar tsorata naja baya, ina kara kankameshi a kirji na. tare da fadin, "suwaye ku?" wata dariyar rashin imani wani acikin su yakece da ita, sannan yace. "Wadanda suka kashe megidanki ne, yanzu kuma munzo mukashe wannan dannakine, daya hana ruwa gudu." tsoro metsanani ne yakamani, zanin goyonsa dake kan gadon, na yayiba na mike tsaye na goyeshi, suna tsaye suna kallona basucemun kalaba. cikin kuka nace musu, "wai kudin suwaye, me mijina da yarona suka muku? Kunkashe mun mijinma bazaku barmuba, sekun biyo dannawa guda daya tilo shima kunkasheshi, kuwanne irin marasa imani ne? Wlh Allah bazai barkuba ku....." Wata uwar tsawa wani a cikin su yadakamun. wadda tasani hadiye maganata, batare dana shiryaba. maganganu yashiga yimun wanda bana fuskantar komai saboda dimuwa da razani, tunanin hanyar dazanbi inkubutar da dana kawai nakeyi. A kalamannasa dai na fahimci yace, turosu akeyi kuma saboda dukiyar modibbo ne. jin haka sena fara neman inda jakarnan take domin na basu, dansu kyalemun dana. seda nagama shan wahala nanemo jakar, nace musu ga dukiya nan, indai dukiyace. Nidai dan Allah subarmun yarona karsu rabani dashi, kokuma ni su kasheni akan sukasheshi. A lokacin senaji gwara ni namutu shiya rayu. wata irin kaunarsa nakeji, tana kara mamaye zuciyata. mutanennan sukace susam Muhammad akace sukashe kuma sesun kasheshi, sannan su tafi da dukiyar. daukar jakar nayi kamar mika musu zanyi, nafaki idonsu nafada toilet na kulle, bubbuga kofar suka hauyi da nufin su ballata. ganin danayi tsaf zasu iya balla kofar su shigo su riskeni sena fara tunanin mafita. shawara zuciyata tabani akan nayi nesa da garin kawai, inda halima nabar kasar gaba daya,ta hakane kawai zan tsira daga sharrin muggan mutanennan. batare da tunanin komaiba na amince da shawarar zuciyata, window din toilet dinmu na kalla naga zan iya fita ta cikinsa, harna bar jakarnan sekumadai nadawo nadauka dannasan zatamun amfani nan gaba, na ratayata, a kafadata, na gyara goyon Muhammad tamau, na fice ta window. da wani irin gudu dabansan ina dashiba nafice daga gidanmu naita falfalashi. Banmasan inda nake jefa kafataba kawai shiga duk layin dana gani yakeyi. nasan balla kofar toilet din sukayi sukaga bananan shine suka biyo bayana, ina cikin guduna kamar ance in juya na hango kyalli fitilarsu daga can nesa. Abunda yasa nagane sune, kuma ni sukebi, duk layin dana shiga nan hasken fitilar yakebi shima. hankalinafa ya kara tashi gashi harna fara gajiya da gudun, ina shan kwanar wani layi nayi kacibus da wani mutum...........(labarin abunda yafaru tsakanin ta da dady ta basu sanna ta cigaba) bayan na bashi yaron senaji hankalina ya kwanta, koda sun cimmun bani da damuwa tunda ɗana ya tsira da yardar Allah, kuma dukiyar da'ake fadan akanta bazasu sametaba. wata mota nagani tazo ta wuce ta gabana ina cikin gudu, can kuma naga motar ta dawo ta tsaya a gabana, kokarin canza hanya nayi cikin tsananin tsorata. mai motar ne yafito da sauri cikin harshen Hausa yacemun. "Baiwar Allah, zoki shiga mota narage miki hanya, naga wasu mutane sunata gudu da muggan makamai karsu suganki suyi miki wata illar, gashi yanzu dare ya tsala" jin kalamansa yasa da sauri na bude bayan motar na shige batare da tunanin komaiba, shima ya koma cikin motar. kafin yakai ga jan motar mutafi azzaluman mutanennan sun karaso layin.........✍️
_*kuyi hakuri da wannan, banjin dadine, dakyar nasamu na muku wannan ɗinma. ABUNDA KASHUKA FAN'S GROUP, nagode sosai da addu'oinku, Allah yabar zumunci mai ɗorewa Ameen🥰🙏*_
*By*
*zeey kumurya*
*4️⃣8️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
_*kuyi hakuri da wannan, banjin dadine, dakyar nasamu na muku wannan ɗinma. ABUNDA KASHUKA FAN'S GROUP, nagode sosai da addu'oinku, Allah yabar zumunci mai ɗorewa Ameen🥰🙏*_
*By*
*zeey kumurya*
*4️⃣8️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*